Sashe 26
Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baban su... Kullum cikin sawa kaina kato yake kake. Hakika Kai din end of discussion ne. As-sadeeq dina daya tamkar da dubu. Ina son ka Ina kaunar ka har karshen numfashi na ba zan dai na rokon Allah ya yaye maka dukkanin damuwar ka ba ya cika maka burikan ka. Ya biya maka dukkanin abunda kake muradin samu. As-sadeeq Kai ne kaahada komai. Duk inda namijin kwarai yake ka ka kai. Ka zarce Kai ka Kuma fin kaiwa As-sadeeq. Hakika Kai din adali ne, gwarzo maabocin addini da kamshi, kyakkyawa Mai kyawun zuciya. Dawisu sarkin ado. Ina gwanin wasu? ga nawa. As-sadeeq hakika na yi mugun sa'a da kansan cewar ni matata agare ka. Domin samun miji Kuma uba nagari ga yayan sa kamar Kai wallah sai an tona. Kai din ka wuce duk inda kake tunani. Kai din kayi gaba sai dai sauran su biyo baya. Mutinci, dattako, Kamala, Ibadah, hakuri, temako, walwala, gayu, kamshi, tsafta... The list goes on and on and on As-sadeeq na. Sakii linzamin ka mai nasara as-sadeeq. Allah ya iya maka ya dafa maka. Kayi musu nisa ya zasuyi da Kai? Wallahi dole su hakuraa. Shi zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzu ana shaho wabillah sai yayi. Shelele na. Habibi da'iman kenan. Na kalle ka nace Alhamdulillah. Na sake kallon ka nace mashaa Allah. Na sake duban ka nace Subhan'Allah Allahu yayi halitta. Duk dan Adam tara yake bai cika goma ba As-sadeeq dina. Kai Kam ka cika taran ka cif cif ba ragi. Allah ya saka maka da mafifin alkhairin sa. Me zaa fara wanka ko abinci ko shayi ko tausa. Me kake so?uhm?" Ta karasa fada tana narka masa manyan idanunta akansa.
Dr abubuakhar dollars yayi murmushi yana matseta a jikinsa hadi da kwantar da kanta akan kafadarsa. Hannunsa daya yana shafa gefen fuskar ta yace,
"Na ma rasa bakin magana . Mariri na rasa ma mezan ce miki. Kin gama karar mun da man Kai na da zan kwarara milk godia .hakika bakina yayi nauyi. Kalamai sunyi karancin magana. Idanuwa na miki kallon kauna da fatan alkhairi. Gabban jiki na maraba da kansancewa a tare da ke. Zuciya na zillon samuwarki acikin ta. Allah ya biyaki da gidan aljannah . .... Ai ina dawowa na wuce bangarena. Nayi wanka. Na kure gayu na shafa turare. Ina zuwa kamar ko da yaushe. Kin sake cinye wankan daren yau . Daga shigar ki zuwa kamshin dake tashi daga fatar jikin ki zuwa gashin ki da kayan ki. Da gidan bakj daya da ke kamshin turaruuka na wuta masu ratsa zuciya da sanyata nutsuwa. Allah ya biyaki Qibdiyya ta .."
Murmushi hajja Qibdiyya tayi tana girgiza kai hadi da dan daga kanta ta saka kan kafadarsa tana duban sa tace,
"Kafi kyawu kyau As-sadeeq. Sai walwali kake tamkar wata daren goma sha tara. Idanuwa na futar da hasken nutsuwa da comfort din kasance wa atare da kai.. Sannu nawan. To ya aikin?. Afuwan.. barka da dare muradin rai na. Fatan ka dawo lafiya. Ayi tausa?"
Ta karasa fada tana kokarin janyo kafarsa. Dr abubuakhar yayi hanzarin riko hannunta yana girgiza kai,
"A koshe nake mariyata. Allah tun abincin dazu bakiji ciki na ba. Ba abunda nake so yanzu sai dai mu kasance a haka muna masu cigaba da hirar mu har ya zuwa sanda zamu kwanta"
.
"As-sadeeq dina kenan. A dai yi hakuri ka asha tea din da dan sauran light food haka ba nauyi kaji?"
"Duk abunda kikace ai hakan za'ai mar'atussaliha"
Hajia Qibdiyya tayi murmushi. Ta mike ta na sumbatar tafin hannunsa. Ta shiga kitchen. Cikin kankanin lokaci ta jere dukkanin abunda zasu bukata akan wani kyakkyawan yadi da amfanin sa aci abinci akai Kawai..
Nan ta jere komai ba akan dinning ba. Ta riko hannuwan sa suka koma can suka zauna. Ta shiga zuba masa komai ta wanke hannunta tana bashi komai a baki. Ya bude baki yana karba suna ci suna murmushi .
Yadda suke zuba kaunar junansu suna bawa soyayya hakkin ta Kai kashe wasu sabbin ma'aurata ne da basu aurar baa.
Bayan sun gama cine. Ta tabbatar ya samu nutsuwa sosai ta fara bashu labarin komai da komai tun daga kan fara aikin Hindu da dukkanin abunda ya faru ya zuwa rasuwar su da komawar yaranta biyu zuwa gidan marayu.
Tiryan tiryan har ya zuwa sanda ta fara sanar masa kadarorinsa da sunayen wadanda sukayi muguntar da makircin.
Ta cigaba da sanar masa komai, Zusa sanda take sanar masa wadanda sukayi muguntar da zagon kasa aka raba shi da kadararorin sa.
Hakika yayi mamaki matuka har yake sanar mata da ma ya fara karkatar da hankalin sa akan Alhaji sambaso amininsa dubada yadda yake bibiyar lamarin da alamun ayar tambaya....
_KWANKWASON JIMINA_
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
_31_
Daga bakin kasuwa ya ke tafiya sambal daga titin zuwa layin gidan sa. Gaban wani shago kadan da ake sayar da kayan dinki ake Kuma dinki ya tsaya yana zaro yan chanjin kudin da ya samu na lodin mota.
Dari hudu da cassa'in ne. Ya kirga su yana zare dari biyu da cassa'in din kai ya mayar da dari biyu sauran cikin aljihun gaban rigar sa.
Sanye yake cikin riga yar shara gabanta anyi aljihu sai hula samfarin tashi ka fiya naci
Yaci saa kuwa wajen mai awarar ba layi. Ana bawa wani yaro ya mika mata kudin hannun sa . Ta sadda kanta kasa tana duban sa tace,
"Ina wuni babaa?"
"Lafiya kalau diyar albarka. "
"Ta nawa zaa bayar ko ta du?"
"Eh ta duka"
Ta zuba masa awarar ta Kara masa wata akai ta daure yaji tana barbada masa kabeji.
Shiru yayi kansa akan awarar dake soyiwa acikin mai. Kwakwalwar sa ta shiga tariyo masa alokacin malama Hindu mai dakin kaninsa malam junaidu.
Tunda ta fara awarar sayarwar har Allah ya karni ranta bata taba karbar kudin awarar su ba. Sannan bata taba fashi ba kullum ne sai ta aika musu da awarar fal da yaji da su timatir da albasa da kabeji.
Idanuwansa ne suka kawo ruwa yayi hanzarin janye su kar su zubo masa.
"Gashi baba" Mai awarar ta sake fada a karo na biyu tana mika masa bakar ledar awarar.
Karba yayi ya mata godia yayi gaba. Ya nufi kwar gidan nasu. Gidan farko kamar koda yaushe sai ya tsaya yatuno shekarun baya alokacin da ran dan uwan nasa.
Samun waje yayi daga can gefe yana duban gidan. Maaikata magina nata Kai da kawowa ana gyaran gidan fadadashi akeyi sosai. Wanda gidan ya koma hannunsa ne ya ke masa na zamani daman gashi gidan fuska biyu ne
Ya tuno sanda motar data kawosu ta saukesu a kofar gidan nasu alokacin da suka dawo garin naduka da zama.
Tariyo komai ya shiga yi yana gani a idanuwan sa. Sanda suka fito daga mota. Junaidu shi yayi masa komai na wayarin wuta da ruwa da sauran kayayyakin gidah alokacin da zasu dawo..
"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun" ya ambata yana goge hawayen da suka zuba masa. Ya girgiza Kai ya mike cikin nasa gidan yana sake maimaita,
"Allah ya jikan ku da rahama junaidu da Hindu da Ashir. Allah ya raya abunda kuka bari ya musu albarka ya daukaka su..Allah ya shiga lamuran su ya musu arziki. Nayi kewar ka junaidu nayi kewa ka nayi kewar dan uwa na gari , aminina, abokin shawarata, bango majinginata junaidu, Subhan'Allah. Gata ya kare Allah ka iya mana. Hindu Allah ya rahamshe ki kema..ubangiji ya dubi bayan ki. Hakika kedin gwarzuwa Kuma kanwata ta gari Kuma mata ga kanina ce.. Hindu Allah ya dubi alkhairan da kika yi ya jikan ki da rahama. Allahu Akbar" ya karasa fada yana dage hanunsa a bango
Ya sanya kasan rigar sa yar shara yana jan majinar data taho masa. Sakamakon mura da lokaci daya ta sarke shi saboda hawayen da yakeyi,
"Ashir... Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Allahu akbar.. Ya Allah kai kasan munufar hakan. Rabbi ka iya mana, rabbi wadannan bayi naka da ka amshi ransu rabbi yasa suna aljannar ka madaukakiya. Allah ka gafarta musu ka enta su. Allahu akbar. Ashir.. Allah ya jikanka da rahama. Yaron nan Mai zuciya da hakuri da ladabi da kawaici. Yaron nan Ashir ba abunda zance sai fatan Allah yasa kana aljanna, ka dakko halayyar mahaifin ka. Da zuciyar mutuntaka ta mahaifiyar ka. Yaro Mai nutsuwa da son zumunci da yan uwan sa innalillahi Wa inna ilaihi rajiun Allah kafimu sanin abunda yasa ka dauke gatan mu duka. Rabbi ka maye mana zukatan mu dake rauni ka yafe mana muma. Allah mun tuba" ya karasa fada yana kwankwasa kofar shiga gidan nasa daya gani a rufe.
Nusaiba na zaune a kujera tayi zuru ta mike kafa.jiran shigowar sa take don haka da sauri ta mike ta sanya hannu ta bude kofar.
Yana dubanta ya kauda kansa. Ya shjga ciki bakinsa dauke da sallama,
"Wa alaykm Salam" ta amsa shi tana zama akan kujera..
"Layla..Ahmadu"
"Naam.bappah" Layla ta amsa shi daga daki
Ta fito da sauri hannunta rike da maficii tana fiffita,
"Bappah sannu da zuwa"
"Yauwa sannu Layla. Ina Ahmad?"
"Ya fita tun dazu"
"Ungo rike nan awara ce. Ayi hakuri abunda aka samu baki daya dari hudu ne da cassa'in. Na saya awara gatanan ta dari biyu da cassa'in. Gaa dari biyun nan asayo wani abun ayi Kari da safe. Allah yabamu saa"
"Sannu da kokari bappah. Mama ya zamuyi da rabin? Bappah zakaci amma ko"
"A'ah a koshe nake Layla. Mun Sha fura wani bawan Allah ya saya mana "
"Banda tsabagaen gulmar dan ubanki a Ina awarar dari biyu da cassa'in zata ishemu? Mu da ku? Ku kanku ba isar ku zatai ba. Ko ke kadai kika dage tsaf zaki cinyeta. Har nawa take awarar? Tashi kiban waje" nusaiba ta fada tana dankarawa Layla harara.
Da Sauri laylan ta mike da awarar a hannu tana duban cikin ledar awarar tace,
"Ai kuwa da yawa Allah. Kamar tafi ta kudin"
"Eh tasa gyara kamar. Ai tanada kirki yarinyar"
"Ohh ummalo ce ko?"
"Wacece haka?"
"Bappah ba me awarar wajen shagon masu dinki kake nufi na?"
"Eh ita fa"
Layla tayi murmushi tana cusa awara daya a bakinta tace,
"Haka take tayita karawa yafi na kudin mutun."