← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 44

Sashe 16

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki daya ta manta sunada aikin da aka basu da zasuyi. Wanda library din ya cika , Wanda garin dube dube acikin wayarta nan taci karo da abubuwan da suka daga mata hankali.

Tunani ta shiga yi na yadda zatayi. Kafin ta sanya hannu ta kira laylan ganin Kiran ya katse bata daga ba

Nan take sheda mata gata nan zuwa . Tattara takardun tayi ta chusa acikin yar karamaar jakar dake hannunta

Futa tayi daga dakin ta bar cikin gidan marayun zuwa bakin kofar makarantar tasu ta hadu da Layla.

Tayi kokari ta saita kanta kafin laylan ta gano wani abun. Don sam batason kowa ya gane halin da take ciki gudun kar ta rusa shirin da take kokarin daura damarar sa.

Dakyar ta iya sauya kanta suka hadu suka duba aikin da zasuyi na makarantar. Suka karkare komai tare suka raba yadda zasu bada aikin idan malamin nasu yazo karbar aikin presentation din da zasu yi.

A gurguje ta iya tsayawa suka kammala sauran darussan ranar tana daukar Amnah daga makarantar ta samu kanta da zuwa inda ashfeef yayan su yake aikin kanikanci. Don tuni ya dena zuwa jami'ar sosai yake aiki tukuru a sansanin wajen kanikacin da biyar da goma yake samu ya saya musu wasu abubuwan har ma da katin waya wataran idan ya samu hali.

Yana karkaashin wata mota yana gyaran ta. Suka karasa wajen . Abokanan aikinsa suka shiga kiran sunan sa .

Ya fito daga karkaashin motar yayi butu butu da bakin mai. Neman halak da wuyan baki daya kayan jikinsa rigace mai yankakken hannu shimi da wando sun yayyage. Hannunsa dauke da karafunan kayan gyara.

Yana ganin su ya saki murmushi . Ya dauki ruwaa a buta yana dauraye hannunsa da fuskar sa

"Sannu da aiki" Nawraah ta fada masa tana murmushi

"Sannun mu dai. An tashi ne daga makarantar?"

"Eh an tashi..."

"Hamma"

"Naam Amnah ta.. yauwa ga cheese dinki dana saya dazu a shago rike kici" ya karasa fada yana mikawa karamar kanwar tasu ledar cheese balls guda biyu

Ta karba da hannu biyu tana murmushi. Nan da nan ta yage ledar ta fara ci tana turawa Nawraah wai ta dauka. Nawraah ta girgiza mata Kai tana daga kanta tace

"Na koshi Amnah. Ci kinji?"

"Wani abun kuke so ne?" Ashfeef ya tanbayi Nawraah yana kokarin zaro kudi a aljihunsa

"A'a hamma ashfeef ba wani abun muke so ba magana ce dai nazo na gaya maka ita. Don kada kaji daga baya"

Waiwayawa bayansa yayi ganin abokanan aikinsa daga dan nesa dasu. Yasa ya nuna mata can wajen wata mota suka matsa. Ya dubeta yace,

"Meya faru?"

Nawraah ta nuna masa wayarta tana murmushi hawaye nason futo mata tace,

"Kasan meyasa hamma Ashir yace kar nayi amfani da wayar nan sai na bar aji daya dana biyu da sauran su?"

Ashfeef ya girgiza mata Kai alamar a'ah..

Hawayen da take kokarin mayar da su ne suka bujere mata suka fara zuba a fuskar ta masu dumi sosai

Ashfeef shima lokaci daya yaji hawayen na kwaranyo masa ya dubeta cikin tsantsar damuwa yace

"Menene Nawraah? Wani abun ne ya faru? Dan Allah ki sanar mun ? Menene ki gayamun kinji?"

Nawraah ta girgiza Kai tana sharce hawayen tache,

"Su suka kashe ummy.... Suka kashe abbiey... Kuma suka kashe Hamma Ashir" ta karasa fada tana daga wayarta

Ya dubeta yana duban wayar jikinsa na kyarma yace,

"Su waye eh?"

"Ina kyauatata zato na akan mutanen dana dade Ina tabbatar da sune suka kashe mana gatan mu. "

"Su waye Nawraah?"

"Alhaji sambaso... Alhaji ateeks... Dr bintu. Wadannan mutane uku acikin su akwai Wanda ya kashe mana su ummy. Duba kaga"

Ta karasa fada tana nana masa wayar a kunne yana sauraron maganganun da sukayi sanda ummy ta jefar da plate. Ta Kuma nuna masa fefen bidiyon da aka jefar da mahaifinsu ta baranda

Ashfeef ya sake hannu ya kulle bakisan saboda wata Kara da take son futowa. Idanuwansa suka furfito waje cike da dimuwa yace,

"Yanzu meye abunyi? Kinsan sunfi karfin mu. Bamuda kowa bamu san kowa ba Nawraah"

"Muna da Allah. Shi kadai ya isar mana. Domin shi din mamallakin kowa ne Kuma da komai"

"Hakane Kam kin gama magana. To yanzu da me zamu fara? Ko bappah Auwalu zamu gayawa?"

"Idan muka gayawa bappah Auwalu ai anyi baayi ba kenan. Domin aunty nusaiba sai ta bata mana shirinmu. Don itama Ina tabbatarwa tanada nata kason kwamashon akan kisan da akayiwa iyayen mu"

"Hakane. Amman Nawraah kina ganin ba zamu janyowa kanmu babban abu ba kuwa? Dubafa ba wani babba da ke tare da mu da sauran su"

"Hamma ashfeef nice fa ko ka manta ne?"

Ashfeef yayi murmushi yana girgiza Kai yace,

"Ya za'ai na manta. Nawraah ke din ai KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA..."

"yanzu kayi magana. ... To da yardar Allah karshen su ne yazo. Zan samu hajia Qibdiyya muyi maganar. Na tabbatar ita kadai ce yanzu zan iya aminta da ita acikin kowa... Duba da tushen matsalar daga wajen su aka samu"

"Gaskia ne . Toh Allah yasamu dace. Ni yanzu akwai abunda zanyi na daban?"

"A'a hamma. Kawai dai dama nazo na gaya maka ne. Kar na fara koma menene ya zama ba sanin ka aciki, tunda kaga kaine babban mu. Sai da yarjewar ka"

Ashfeef ya kada Kai. Tausayin kannen nasa ya sake lullube shi, rayuwa kenan wai yau shine Nawraah suke kira babban su. Ba iyayen su ba ran hamman su. Baa wani dake tare da su sai Allah.

Hawayen da yake kokarin mayarwa ne suka zubo, Lalle girma ya hau kansa. Ya dube su cike da so da kauna yace,

"Shikenan Nawraah na amince. Allah yasa mu fara a saa. Allah Kuma yayi riko da hannayen mu. Allah yasa karashen kowane mai hannu aciki ne yazo, Allah yasa hakanne yafu alkhairi, Allah ya jikan iyayen mu. Ya bude mana kofofin alkkhairinsa aamin"

"Aameen hamma. aameen"

Kudi ya zaro nera tamanin ya mikawa Nawraah yace su saya wani abun. Suka masa sallama suka tafi yayinda ya koma karkaashin motar ya cigaba da gyaran da yakeyi

Nawraah na rike da hannun Amnah suka tinkari gidan Alhaji Abubakhar dollars.

Ta dora hannu akan gate din gidan zata bude kenan wayarta ta fara Kara. Ganin me Kiran yasa tayi murmushi, ta juya ta dau wayar a kunnenta suka koma bakin gate din gidan marayun .

Marwaan ne ya kirawota suka fara waya. Yake sheda mata gashinan zai zo su gaysa.

Don haka ta fasa shiga gidan Alhaji Abubakhar dollars din suka shiga gidan su na marayun tana tafe da wayar a kunnenta suna waya. Hannunta na dama rike da hannun Amnah suka karasa shiga ciki....

*NADUKA ZONE*

Da kanta ta ke tukin motar, Bayan motar shake yake da kayayyakin abinci da manya manyan ledoji....

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[5/7, 6:54 PM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_21_

:::::::::

A haka ta karasa unguwar Naduka zone. Tana juya kan sitiyarin motar ta faka a daidai kofar gidan da zata shiga.

Fitowa tayi daga ciki motar ta ta bayan ta karasa parking din a inda ya dace. Sanye taa ke cikin doguwar riga ta atamfa. Tayi daurin channel o.

Sai mayafi da ke dabaibaye da manyan stones da aka bi da shi da design din flowers.

Hango Ahmad tayi yana tahowa daga cikin gidan su.

"Ka ga" ta daga hannu tana kiran sa...

Karasawa yayi wajenta ya gayshe ta ta amsa tana nuna masa bayan motar ta ta,

"Dan dakko kaya anan. Idan zaka iya hadawa akwai wasu a booth ma."

"Tohm" ta fada tana bude murfin baya... Ya dakko wasu manyan ledoji ya rike.

Ya zagaya wajen booth din nanma bayan ta bude ya dakko wasu ledoji ya dora akan sa. Sauran kuma ay rike su da hannuwan sa.

"Ina za'a Kai?"
Ya tambaye ta yana rike da kayan

"Muje gidan ku" ta amsa shi tana yin gaba.

Ahmad na biye da ita, suka karasa har kofar parlorn su..

Nusaiba ce a zaune akan kujera . Tanata girgiza kafa. Ta jiyo motsi, idanunta a rufe saboda masifa ta shiga cewa,

"Wallahi wallahi zan surfa maka rashin mutinci Ahmad. Dan iskanci nace maka kaje kayi sauri ka gaya masa ko ya bada wani abun ko ya kwan a waje ni ba baiwar gidan su bace. Aikin kawai"

Ahmad da ke rike da kaya ,Nike Niki kunya duk ta mamaye shi hi na maganganun da mahaifiyar tasu nusaiba ke fada,

Aiken sa tayi wajen bappah Auwalu mahaifin su, kan yaje ya nemo shi duk inda yake ya sanar masa inde ba zai bada kudin abincin da zaa dafa ba ko ya bada abincin da zaa ci, lalle kar ya dawo mata gidah zai kwana, ya nemi waje kwana daban..

"Assalamu alaikum Wa rahamatullah" Dr bintu ta yi sallama tana kutsa Kai ciki

Nusaiba na zaune sai ta mike tana dashare hakora hadi da saka hannu ta gyara dankwalin kanta.

"Waalykm Salam hajia. "

Ahmad ya karasa shiga da kayayyakin ya ajiye yana komawa gefe

"Yauwa yaron kikri nagode. Ungo wannan kasha ruwa" ta zaro yan dubu daya guda biyar ta mikawa Ahmad

Ahmad ya girgiza Kai yana murmushi,

"A'a nagode"

"Rike mana baka nayi ai ba roka kayi ba" cewar Dr bintu
Chapter 16 · 0% Book details