← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 44

Sashe 31

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya cigaba da cewa da ita,

"Da farko ni marwaan sambaso lokacin dana fara ganin ku dinnan daya ke cewa kin tare masa wajen parking lot. Har ga Allah Anees ya bude baki zaice wnai abu nayi hanzarin cewa dashi ni nayi mata Ina nufin ke kenan. Sai yayi murmushi kawai, tun daga lokacin aboki na ya nuna yabar mun ke nasan halinsa komai da komai. Tun daga lokacin yake kokarin nesanta kansa daga gareki. Ni Kuma by Allah alokacin kawai irin nayi niyyar date and dump dinnan Kawai zanyi .saboda haka nakeyi by Allah player ne ni lokacin, Idan na samu kin karba soyayya ta sai na yaudareki nace bazan cigaba da alakan dake ba. Nayita cusa Kai na agare ki. Har kika amince, Shekarun baya Muna fteshers abokina ca sukeyi dani play boy.... Ko M-Con. Saboda dai iya tsara mata da yaudarar su. Tohm Amman bansan haka destiny na zai canzu akan ki ba. From playing/toying with your feelings sai na koma praying to have you as a wife. Allah ya kamani na kamu da madaukakiyar kaunar ki. Inason na mallakeki a matsayin matar aure, Amma kafin sannan ko zaki iya tunowa da abaya idan kunje wajen cin abinci ko in kinje aji ana kyamatarku suna bullying naku? By Allah Anees ne ya hanasu Nawraah. Ko kinsan cewa kyamatar ku da ake ana muku dariya da farko da kuka shigo da aka dena daga baya waye? Ba kowa bane fyace Anees shi ya hana adena muku. Da kudinsa da guminsa sanda kanwarki batada lafiya dinnan kunje asibitin cikin school ..Nawraah wallahi ba karya nake miki ko ince zan miki ba. Anees shine Wanda ya turomin sako yace gashi Kun kawo wata yana tunanin sister dinki ce karama, sannan shine Wanda ya biya likitoci da nurses din da suke a tsaye suka mata aiki da sauran abunda ya dace. Wallahi ba kwandalata aciki.... Nawraah Anees bai bar asibitin ba. Tun lokacin sai dai yaje gidah ya dawo ya zauna a waiting area da facemask yana ganin shige da ficewar ku. Dukkanin abincin da ake ta kawo muku na abinci da sauran needs tun sanda kuka kwanta zuwa sallamar ku dik shine..hospital bills Kai komai da komai Anees ne...."

Ya karasa magana yana tura mata wasu hotunan.. hotunan receipts na shedar biyar an saya abu da pos. Da wani littafi dake dauke da biro agegensa.

"Kingane wannan book din?"

Nawraah da gaba daya so take ya dena gaya mata maganganun haka ta samu ta kwanta. Tace dashi cike da kufulewa,

"Na abokin ka "

"Na Anees ne..tabbas. duk Wanda yake Alharamein university final year dinnan zai ce books din Anees ne. Sannan ba Wanda yasan ya cikinsa yake duk amincewar mu da shi kuwa .. Bai masan na sato masa ba acikin mota rannan. Amman akwai wani abu dayake Ko kina waje duk inda kika Saka yana biye dake. Zai faramiki zanen. Zanen fuskar ki da jikin ki. .... Duba ki gani hotunan dana dauka duka zanen ki yayi. Ki duba sauran hotunan Dana yi screenshot..tarin hotunan ki ne Nawraah tun ranar da kika fara sanya kafa a makarantar Alharamein. Anees bai tsayar da alkalaminsa ba..bansan yanada wannan talent din bama sai akan ki. Duk inda kike zai fara zana hotunan ki. Ya na lura dake sosai. Ko sanda kika kirani ban dauka ba last. Anees yakirani na dauka ranar ma na san yana bibiyar ki ne dan tsaro.. temaka dai Nawraah. Anees wallahi yana mutiar kaunar ki fiye da yadda bakina zai furta miki. Fiye da yadda hannu zai rubuta Miki . .dik yadda zan sarrafa ba zaki gane ba. Amman ki sani Anees abubukhar dollars yana kaunar ki sosai. Kaunar da zai fatan samun ki amatsayin matar sa. Amma guess what? Saboda loyalty da Kuma girmamaawa irin nasa. Ya kauda kansa yayi tamkar ba sonki yake ba. Kamar bashi ya fara ganin ki yaji yana sonki ba..ni nayi masa shigar sauri. Gashi bayason alakar zumuntakar tsakanin mu ta rage. Shi yasa ya hakura yabar mun ke. Tundaga ranar don ba zai iya tsayawa muna musaya akan mace ba. Nasan halinsa zan shede shi..abubuwa da yawa dai Nawraah. Anees is your truest lover, He loves you beyond your wildest expectation.. Amma saboda son kai irin nawa, da selfish interest na kasa nuna masa nasan shine yake sonki tun fari, naki bashi kofa, Ina babba gaba da shi naki cin girman na bar masa, saboda gaskia sonki ya mun rikon karfi I can't do without you, ke ce bazan iya barwa Anees ba. Amman duk abunda na mallaka zan iya bashi... karki ga kaman na hakura da kene no, not a bit. duk da haka ban hakura dake ba fa..shi ya zabi ya bar sonki a ransa bazai gaya miki ba tunda mai hakuri ne.. So saboda hali na rayuwa. Dakuma dubada yadda muke cikin matsatsin abubuwan da suka gabato mu. Komai sai da albarkar iyaye..inshaa Allah ban cire ran auren ki ha Nawraah... Sai dai ko idan rai yayi halinsa. Shima ran idan yayi halin nasa a sannan ne to zan rokeki da Allah ko bayan rai na ban yadda ki aura kowa ba fyace Anees. Ke ko Allah yayi auren mu sai mutuwa ta riskeni. Dan Allah ki auri Anees shi kadai ne zai iya rikemun iyali na....... Ina nan Ina cigaba da shawo kan mahaifinw. Domin su maka kansu a kotu idan sun tabbatar da shedar su din basu aikata ba to sai su fuskanci wani abun ...

"Zain iya cigaba ko na barshi haka?" Marwaan ya rubutawa Nawraah bayan yayi vn..

"No " ta amsa masa da reply

Marwaan yaga sakon ta ya shigo ya sake danna speaker ya fara mata wani vn din .

"Ni dai Dan Allah ki yafemun, nasan ni mai laifi ne awajen ki. Amman ki sani wallahi Allah banda masaniyar abunda iyayena suka aikata akan iyayen ki. Ko faifon bidyon nan ni ne Sanda Muna ta video call da baban mu shine naga shi mutumin mahaifin ki kenan ya shigo haka suna yar tsama sai na danna recording na bidyon bayan naga abunda ya faru bancewa mahaifi na nagani ba nace nabar wajen yanzu na dawo wajen system din. Anan na fara bincike akan iyalin naga duk sun rasu sai babban dan su na samu aka samomin number sa na sayi sabon layi anan kasar wajen nayi registering number na tura masa bidiyon Ina tura masa na tabbatar ya karba kawai na yi de-actibating layin gaba daya. Bayan mun dawo Nigeria ne just recently bayan mun samu sabanin nan dake har kike fada shine nasan mahaifin ki ne, sannan yayan ki ne wannan dana turawa shima ya rasu. Dan Allah kiyi hakuri banda bakin da zan iya wanke Kai na awajen ki. Amman ki sani tabbas iyaye na ne su amma wallahi banda masaniyar abubuwa da suka aikata Nawraah.. duk wani lefi dana miki Dan Allah ki yafemun ki kuma dubi maganguna... Allah ya baki hakuri ya shiga cikin lamuran ki da yan uwan ki. Kuma inshaa Allah zan cigaba da fafutar nema muku hakkin ku da yardar Allah. Ina fatan Kuma nasara ce zata biyo ba. Love you die💜"

Ta gyara kwanciyar ta hawaye na zuba daga idanunta. Maganganun sun matukar sata razana, tu'ajjabi da kuma ban mamaki... Kawai ta Saka hannu ta katse vn bayan tayi forwarding dukkanin chats din nasu zuwa number ta. Ta yi blocking number tasa tayi deleting gaba daya..

A ranar dai bacci ya kauracewa idanun su har aka kirayi sallar asubah... Kowanne bangare na cikin wani hali marar misaltuwa musanman Nawraah jagora kasancewar ita din KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA....
_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_38_

:::::::::

  *Tana* zaune a bakin gado tayi wanka ta sauya kaya zuwa na bacci. Ta daga kanta ta sauke akan katon agogon bangon dake wata kusurwa a dakin.

Lokaci yaja ainun mai gidan nata bai dawo ba bai Kuma dauki wayar da take ta kiransa ba. Bai Kuma kirata ba. Ta tuttura masa sako a text message data Whatsapp ba reply. Har ta mail ta tura masa ko zai duba nanma ba respond.

Jikinta ya shiga rawa. Ganin hakan bata taba faruwa ba. Bai taba Kai dare haka ba. Bai Kuma taba kin daukar wayarta ba ko yaga sakon ta yaki magana ba.

Duk ta samu sosai tanata kawo abubuwa da dama..Allah yasa ba wani abun ne ya faru dashi ba. Don tabbas duk yadda akai yana cikin wani hadarin ne kilan..tanata kamo addu'oi abakinta tana rokon Allah yasa lafiya yake..Allah ya Kuma kareshi a duk inda yake

Karar horn dinsa taji ya gama parking . Tana tsaye agaban window dinta na dakinta a sama tana lekawa gabanta na dukan uku uku..ganinsa tayi ya fito daga cikin motar ya jingina ajikin ta yana waya yana murmushi..

Tashiga sake sake a ranta. Ko wani abun ya sakeyi ne yake farin ciki? Ta tuno ai nusaiba ta turo mata sako zasu bar burnin naduka din sun amince. Da yayi wani abun da nusaiban zata fada.
Chapter 31 · 0% Book details