← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka yaran nata ma lamarin ya dame su sosai musanman marwaan da dama yana dauke da tarin damuwa kala kala....

*******

Ganin shiru shiru har dare yaja ainun ba wata tsayayyiyar magana yasa bappah Auwalu dake zaune akan kujera ya dubi nusaiba tana kusa dashi duk tayi tsuru tsuru,

"Nusaiba.. tun dazu ta bakin ki muke jira fa fisabillahi"

"Tace mu saurara."

"Tun dazu kika cewa tace mu saurara tun safe. Haba Dan Allah. Menene matsayar gwara mu saki "

Nusaiba ta latsa wayar hannunta ganin yadda lokaci yaja ainun ta nunfasa tace,

"Auwalu tafiyar nan Ina tunanin ba yanzu bane sai nan gaba"

Bangane ba"

"Eh yadda na fada dai hakan take. "

'meye manufar hakan. Meyasa sai gaba wani abun ne?"

"Haka dai tacemun...don haka sai mu mayar da kayayyakin mu ma'ajiya. Su Kuma baqi su koma inda suka fito"

Nawraah tayi murmushi Jin karashen zancen nusaiba. Sarai tana sane da su take. Don haka tace,

"Aunty muma dama ba zama zamuyi ba. Yanzu tunda dare bai ja ba zamu koma namu gidan"

Nusaiba ta kece da dariya tana tafa hannuwa,

"Naku gidan? Sannu masu gidah kice dai gidan marayun da kike a tsakure. Amman gidah ai gashinan ya tashi daga naku mallakin na wasu ne"

"Nusaiba meye haka. Zan mugun saba maki. Ai dama tun baa je ko'ina ba halayen naki basu sauya ba? Yaran nan yaushe rabon da ki gansu? Yaushe kika taba takawa kika je inda suke. Nan gidan mahaifin suke? Uba nake awajen su. Amma saboda kwakwazo da kiyayyar da kike musu da tsangwama da kyara shysa ko suzo su wuni basayi.kiji tsoron Allah nusaiba. Wallahi"

Nawraah tayi murmushi. Hannunta rike dana Amnah tana lankwasa yan yatsun . Yayinda ashfeef na daga gefe a zaune shima.

Tache,

"Bappah kayi hakuri . Tabbas munyi kuskure da bama zuwa mu ziyarci ka da yan uwa kasancewar ka mahaifinmu. Domin Kai ma uba ne. Ko da abbiey yana nan. Da Kai da yaran ka ba abunda kuka mana na nuna rashin son zaman mu a tare ko hana abinci da sauran su. Duk kunyi bakin kokarin ku. Musanman bappa da kake yawan zuwa kana ganin mu a gidan marayun . Mungode sosai bappah, Yaya Ahmadu Ma idan yaso wajen hamma ashfeef Muna zuwa mu gaysa. ..."

"Idan Kun fita, ku turo kofar sauro wallahi"

Nawraah da nusaiba ta kaita makura duk hakurin da takeda shi . Yau dai tace bara ta mayar mata,

"Aunty kenan..wallahil Azim koroko kike kina kuka jina jina mu dawo nan gidan wallahi ba zamu dawo ba. Ai nan ba gidah bane. Gidah shine inda ake samun nutsuwa da kwanciyar hankali , ahada karfi da karfe atare.. Gidah shine Wanda ba zaa hanaka abinci ba, ba zaa maka wulakanci ba... Gidah shine inda zaka huta. Cikin yanayin da kake a lullube na bakin ciki da damuwa sai an yaye maka shi,gidah rufin asiri ne . Gidah marayu gidan mu ne, lamba daya kuwa, domin sunfi wadanda muka hadu dasu ta zumunta, Sannan alummar da ke cikinsa da yardar Allah Allah zai amince mana da su baki daya. ..wannan har gidah ne da kike tunkaho da shi?"

Sai ga nusaiba ta daka tsallen albarka,

"Okay Auwalu kana jinta ko?.to gashinan tana rena maka gidan..ah lalle wuyan ki yayi karfi.wato yan kujerun nan namu da katifu da sauran kayan kitchen a takaice wannan kango ne, ah lalle. Wuyan ki ya isa yanka. "

"Tabbas nan ba gidah bane anty. Ai kaje gidan da ake maraba da Kai shine gidah Koda kuwa ba shida komai na more rayuwa, ko da kuwa kullum dusa ake ciki, Amman zaa tarbe ka da so da kauna, nanne gidah . Ba karamin abubuwa ne ke sanyawa hakan ba. Gidan da zaka je a karbe ka hannu biyu..na ciki da suka rigaka shiga su karbe ka kamar dan uwan su. A tare an zama daya. Ga wajen kwana ishasshe. Ga hadi da kayan kallo ga abuncii har sai mun ture kullu yaumin. Abubuwa dayawa dai wannan gidan ya zamar mana Kuma mun samu hanyar arziki sosai acikin sa. Bamu kadai ba harda wasu.. Alhamdulillahi. Nan Kam anty ba gidah bane. Gidan ba aso kazo. Gidan da aka baka daki daya da tumaki da akurkiin kaji. Gidan da inde baka nemo ba ka kawo ba zakaci abinci ba, gidan da ruwan sha ma saii ka roka. Wanka kuwa sai dai kayi a awaje. Kai wasu abubuwan ma ba zasu fadu ba. Amman tabbas fita zamuyi mu mu tafi gidan mu. Inda ake son mu da kaunar mu ana farin ciki kasancewa damu. Har gaban abadan bazan dai na fariin ciki ba akan kasancewar mu ni da yan uwana acikin gidan marayun. Saboda gidan marayun ya zamar mana riga da zani harda danwali, Gidan marayu ba yunwa. Ciwon Kai kake sai an baka magani kasha. A Kuma kula da Kai. Duk abunda muke so bamu rasa ba banda na iyaye. Ku. Bayaga haka Alhamdulillah mun samu sauyin rayuwa bayan rasuwar mahaifan mu kala kala. Wanda ya zamar mana tarihi Mai dauke da mamaki. Bakomai bane fyacr cikinsa shine mutanen da basa yi dakai sai da ran mahaifan ka. Hahahaha duk anyi walkiya mun gansu Kuma da saura. Suma Allah bazai bar su ba. Akwai Wanda ma daman kaman jiran yake iyayen mu su rasu saboda mu shiga ha'ula'in rayuwa.... Sai yanzu na tabbatar Dan uwa ba wai shine jinin ka da kuka hada jinin zumunta ba, Dan uwa shine Wanda zai daukeka ya rikeka tamkar Kai din jinin sa ne, Baku hada komai dashi ha. Amman har yafi Dan uwan ka na jini zumunta.

To ki cigaba da shararawa a gidan ki. Mu ba zama zamuyi miki agidah ba. Mun daina zama inuwa daya da makiyan mu. Gidah dai naki ne sai yadda kikai da shi. Ko akukurkin kaji da kika bamu a baya muka zauna, kada ki manta mu ma mahaifin mu ne ya baki. Sannan abubuwa nawa suka miki na rufin asiri aunty...?"

"Auwalu kana ji kayi shiru ko?"

Bappah Auwalu ya tafa hannuwan sa yana kauda Kai yace,

"Me zance mata?. Yo ai duk abubuwan da ta fada babu na karya aciki nusaiba. Sannan da fari ke kika dakko zancen ma. Na meye naki kina babba zaki fada musu haka? Wani lokacin mantawa kike ne yayan yan uwan na ne?.sannan ko mantawa kike gidan nan dai nawa ne ba naki ba. Amman idanun ki sun rufe sai magana kike, Wallahi summa tallahi kece kika bangaro nusaiba.... Tun suna kankana kike zubar fada agaban su, taci ta cikata yau ta amayar, A wannan daren zasu fita su koma ?.kamar wadda batada Yaya ba kisan ciwon kan Yaya ba. Ko da yake naki gasunan a kusa suyi fitsari su kwanta yan gidah ne. "

"Yo Allah na tuba daman ai haka nasan zaka fada Auwalu. Ai yayan da basalefi ne shafaffu damai. Baka goyan bayan kowa inde akan sune. "

Nawraah har ta Kai bakin kofa sai ta juya idanuwanta na hawaye tache,

"Anty kenan. Wallahi badan bappah ba da tuni jin dadin duniya ma kin dena yin sa. Ya Ahmad, Layla ku mun hakuri .Amma mahaifiyar ku lamarin tsanar da take mana yayi tsamari.... Aunty ni da yan waiana kallon ki kawai muke.."

"Dalla can ..wannan wannan wannan yarinyar dama ana cewa sanda kina karama waye waye ba zaki magana nmba da surutu, idanun ki Ina kallon sutun a zamin baya na gano bakida da'aa.."

"Aunty kenan. Me bibiyar mu dik inda muka sanya kafa. Duk wani farin ciki nida yan uwana bakkya so mu samesu. Kokari kike ki dakile komai"

"Ke dallacan.. kinata zuba baki ya bude ana bin maza ko? To ki tsaya kiji dakyau nafi karfin na bi sahun kafafun ku baku Kai matsayi na ba, yan Wahala.. ku Kuma Kun tsaya sakeke yarinya karama tana gasawa mahaifiyar ku magana" ta fada tana dankarawa su Layla harara.

"Me zasu ce?. Ai fadan kine wannan sai yadda zaki karashe kedaya" cewar bappah Auwalu

"Auwalu kenan. Ka gaya mata idan tana cin kasa ta kiyayi ta shuri. Wallahi wallahi yarinyar nan Nawraah naga alama. Tana nan akan wannan tankwararran halin na ta na KWANKWASON JIMINA CE MAI WUYAR SHAFAWA. toh wallahi zan dagargaza kwankwason nata naga bakin da zata dinga magana dashi .. ko hukuma ta shiga tsakanina da ke. Tunda ke din banza ce. Marar da'a. Saboda maza na baki kudi kin kode kin zama fara kina wani fiffika kina iyayi"

"Aunty kenan Ina kyautattan zaton ko ya yanki ba zasu kaini kyakkyawan hali ba, Na biyu anty zaki iya zuwa hukumar ki ce su shiga tsakani na dake. Da ni dake zaa ga Wanda hukuma zata rike. Domin komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskia"

Tana karasa fadaar abunda za ta fada tana rike da hannun Amnah suka tafi. Ashfeef dama tuni ya fita. Suka jere suka nufi gidan marayun nasu..

Babba Auwalu duk da dare ne ba wajen zuwa. Takaicin Kalaman nusaiba ya sashin sanya slifas dinsa ya futa

Yayinda ahmad da Layla ma kowanne yayi dakinsa suka bar nusiba tanata maganganu..

Yadda Nawraah ke fadan maganganu tabbas tasan wasu abubuwan sun fito ne?

Hannunta na rawa ta dau waya ta na Kiran Dr bintu..Amman Kiran duniya wayar taki shiga batasan ta sanya ta a blocked number ba.

:::

Su Nawraah na futa daga gidan bappah Auwalu ta sauke babban numfashi tana goge hawayen fuskar ta

Ta sanya kanta ta dubi gidan, mallakar su ne a baya. Wanda a yanzu wani mutumi ne gidan ya dawo hannunsa gashinan yana modernizing dinsa ma

Suka karasa gidan na su suka shiga. Su Raudah suka tashi suna rungumeta jin dadin sun dawo

Nawraah ta janyo wayarta dake jaka missed calls rutudu na hajia Qibdiyya dake a silent tasaka baaji. Nan da nan ta kirata back .bayan sun gaysa nawraan ke gaya mata yaddaa akai basu samu tafiyar ba

Hajia Qibdiyya ke sheda mata da zuu Alhaji sambaso yayiwa Mai dakinsa Dr bintu auren bazata. Babban abunda zai sake tsoratata ma shine aminiyarta ya auro Kuma batada masaniyar yana naman auren..to tana dai nanne tasan zuciyarta da gangar jikinta dai ba lafiya dan ance har kwanciyata tayi asibiti bayan ta Suma..
Chapter 34 · 0% Book details