← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 44

Sashe 27

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ita Kuma haka take?. Allah Saka mata da alkhairi. Allah ya raya su idan da rabo sai ayi aure ma"

"Amin. Amman fa yaya Ahmad take so" Layla ta fada tana daria ta cigaba dacewa,

"Tayita kunyaa idan ta ganshi. Shine yayanta Gali abokin su ya Ahmad ne shine yake ce masa sokuwar kanwar nan tasu nan duniya shi take so "

Nusaiba ta juya a chake tana janyo tsaki hadi da dankarawa Layla harara a kufule tache,

"Narantse da Allah. Zan Kai miki bugun mahangurba. Sai zuba kike kaman bakin naki ba linzami wacece ummalo? Me awarar? Kike maganar ta da Ahmad. To bude kunnunki kiji...

Dai dai lokacin Ahmad yayi sallama ya shiga parlorn na su Nusaiba na na sallamar sa ta juyar da saitin yatsan da take karkadawa Layla ta mayar dashi kan fuskar Ahmad tace

"Soyayya kake da me awara? Ai Kai har nan har ka Kai minzalin tsayawa da mace Kuna hira ko?idanma zakai budurawar to kaje gidan maiko maiko inda zaka samu ka dandali arziki. Wallahi inde Ina raye. Ku bude kunnuwan ku kuji ba zaku auro yara Tsantson talaka ba. Mai za ai da auren jeka na yi ka. Auren zaman yaran da ka haifa kawai auren kaddara. Auren Allah wadai. Kullum kaine fararo fararo kana yar murya a sanmaka abinci. Ba zeyiwuu ba. Kuce zakuyi irin auren da nayi auren da har yanzu ina dana sanin kasancewar yinsa. To ba zakuyi irin sa ba. Ga damuwa ga yunwa. Da karancin shekarun ka ka koma babba saboda wahala. Ina bazaiyiwu ba. ..kuna ganin matsatsin da muke ciki suturar kirki banda ita. Lahai lahai iska zata dauke mu saboda yunwa. Daga yau karka sake kar na sake naji Kai ko musayar kallo kaayi da me awarar nan sai ranka ya baci. Haka zalika kema shashasha. Kinje makarantar yara masu da hali amman kin ki samo Wanda zaki aura kema auren gatan nan da aketayi kiyi mumaa mu huta. Kwata kwata ba kida saurayi. Amman tunda haka kika tsara shikenan. "

Ta dinga kwafa tana jefa musu harara. Ta dankarwa Ahmad ta juya ta narkawa Layla. Ahmad da baki daya ya kasa gane kan inda zancen ya dosa. Kawai ya sake gaisheda bappan su yana basu hakuri kafin ya mike ya fita daga cikin gidan nasu

Layla ma daki ta shige. Hawaye daya na bin daya. Tarasa wane irin hali ne da mahaifiyar su. Sam kullum ne sai ta saukewa bappam su bubun tijara ba bataa jin dadi. Gashi wani lokacin ma har makota sukan shiga rabiyar fadan su.

Tana danna awarar a baka tana hawaye ahakaa ta karasa cinyewa ta korada ruwa ta goge fuskar ta kwanta.

Nusaiba bayan yaran sun mike sun tafi. tache,

"Bakina ba zai gaji ba dai da maimaita maganar nan ba. Yanzu Kafi son mu zauna a wannan rayuwar Muna yunwa da wahalar rayuwar juna..bansan wace iriyar zuciya bace da Kai wallahi. Ace ga sauki yazo mana baki daya amman ka kasa fuskanta"

"Idan maganar nan zaki sake maimaitawa zan tashi na bar miki wajen baki daya.... Bana hango abunda yayi mun nisa na gaba dani, Abunda Allah ya horemun ya isheni rayuwar duniya.."

"Naji, ajiye shi gefe. Yanzu saboda Allah a wannan kangin zamu cigaba da zama. Kana zuwa dakyar ba kawo dari ko dari biyu kana tafiya dakyar haka kake so muci gaba da rayuwa eh?"

"Sai Kuma kiyi. Na gaya miki, kwadayi mabudin wahala.. wannan zuriyar da kike bi kibi a hankali. Kwarai zasu Kai ki su baro ki. Ato"

"Gaskia Kam. Kai naga saboda zuciya da rashin son abu wasu ,da kake dashi ka zama wani abu yau rayuwa, ah sannu Wanda ya tara yayan kudi a banki....Mashahuri.."

Bappah Auwalu ya dauki carbinsa yafuce daga gidan,. Yabar nusaiba nata kunduma mita

"Wahalle uban yan fadin rai" ta fada tana hararar sa bayan ya futa.

Haka ta zauna a parlorn tanata sakin tsaki ta mike ta shige dakinsu tanata kunduma ashariya tana durewa a zuriyar hamidniyya lebanon...

*Nagode da addu'oi Allah ya jikan musulmai ya bamu lafiya Mai dorewa amin*

HANSATUWA🧕

VIP PAGES NA
: AREWABOOK:MSSXOXO

_KKJ_

_32_

***

Kwance take akan gadon ta. Baki daya bacci ya kauracewa idanun ta. Ta sanya kasan rigar ta tana goge hawayen dake zurara daga idanun ta..

Baki daya ji take duniyar ta mata nauyi. Rayuwa ta mata zafi. Shin Ina madafa? Su Wa zata duba ta gayawa tarin dakon dimbin damuwar dake addabar zuciya, ruhi da Kuma gangar jikin ta?

Ta tuno yadda suke zaune a baya taree da iyayan su da babban wan su kula dasu kamar Wanda ya haifee su?

Ta sauke ajiyar zuciya ahankali tana girgiza Kai ita daya. Tunani dankare cikin ranta. Tayi wannan ya kauce ta dakko wannan shima ta gama haka da haka dai.

Baki daya yan dakin nasu tuni sunyi bacci. Don wasunsu har da sakin minshari. Alamun baccin yayi nauyi tuni sun dade da lulawa duniyar bacci.

Mikewa tayi a hankali. Hannunta rike da wayarta ta shiga bndaki bakinta dauke da addua

Fitsari tyi hadi da tsarki ta Kuma dauro alwala. Kan sallaya ta nufa ta tsaya ta janyo hijabin ta ta tada iqama. Sallolin nafilfili tayi hadi dayin adduar istikhara don neman zabin Allah acikin lamuran data Saka agaba.

Ta jima tana kwarara addua tana rokon Allah ya dube su ya dubi halin da suke ciki ya musu tallafi ya dorasu akan makiyan su..

Tayi istigfari da sauran adduoi ta shafa. Ta dade a zaune abakin gado bayan ta idar bacci sam yaki daukar ta

Dakyar dai bacci barawo ya dauketa zuciyar ta fal da sake sake abubuwan kan yadda zata bullowa lamarin da suke ciki da Wanda zai doso su..

Haka ta cigaba da addu'oin neman zabin Allah..tana istikhara har ya zuwa kwanaki hudu. Tuni tafara jin ranta na mata sauki daga matsayin da take ciki.

Tana zaune lamarin nata jujjuya mata. Ta saki wayarta tana duban number marwaan yau kwanaki kusan nawa basa waya. Ba message ba chat. Zuciyarta na mata zugi da rada'di..

Ta samu kwarin gwiwar danna masa kira a waya. Marwaan na zaune akan kujera a dakinsa. Baki daya har ramewa yayi ya zabge saboda tashin hankalin da yake ciki

Wayartsacetafara kara. Dajin ringtune din yagano Nawraah ce. Don ita kadai ya sakawa ringtune daban saboda ita din special one ce, a duk inda yake idan ta kira zai gane itada ce.

Gabansa ya tsanants bugawa. Hannunsa na rawa, ji yake anya zai iya daukar kiranta kuwa? Baki daya kwanakin daya sauke mata wuta baya nemanta baya amsa Kiran da sakon da take yi masa duk saboda matsayin da yake cikine. Sam bayason ya sanyata a damuwa acewar sa ga abunda iyayensa sukace akanta. Sannan ba babbar matsalar da take gabansa

Ya samu kansa da daga wayar yana duban screen din. Har wayar ta tsinke bai dauka ba. Ta sake kira. Ya danne kirjinsa da hannunsa daya yana cije lebe ya dauka.

'hello..."

"Assalamu alaikum " ta fada cikin sanyayyar muryarta.

Kana jin muryoyin nasu kasan dukkanin su na cikin matsalar rayuwa, Dubada yadda kowanne muyarrsa ke a cunkushe dake lullube cikin radadi da zugi na tashin hankalin da take ciki.

"Wa alaykm Salam" ya amsa yana sauke numfashi.

Duban screen din wayar tayi bayan ta zare daga kunnenta. Ta mayar cikin kunnen nata tana mai sake cewa da shi,

"Ina wuni?"

"Alhamdulillah" ya amsa yana sake jan kasan lebensa, shi yana rasa me zai ce mata

"Marwaan" ta kira sunansa cikin wata iriyar muryar dake nuna tana cikin damuwa

"Uhm"

"Kana jina?"

"Uhm"

"Kazo inason magana da Kai"

Samun kansa yayi da zunkudawa daga zaunen da yake a kujera yana sosa kasan keyarsa yace,

"Ba.."

"A'a ... Yau nakeso nanda anjima kadan kazo muyi magana da Kai"

"Nawraah please"

"Yau please marwaN... Kazo inason muyi magana"

"Nawraah ki sake hakuri, har yanzu Ina kokarin tausasar zukatan su ne. Kinji?"

"Ba damuwa kazo dai muyi magana"
Kit ta katse kiran tana ajiye wayar a gefe

"Nawraah kina ji? Please give me some time, like I'm battling with .....hello?"

Jin tayi shiru kamar shi daya yake magana yasa ya daga wayar yana kallon screen, Ashe ta katse kira.

Ya sauke gwauron numfashi. Hadi da saka hannu yashafi fuskar sa yana tallabe ta.

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun " ya fada yana sake suake numfashi

Mikewa yayi ya shiga bandaki ya watsa ruwa. Closet dinsa ya nufa ya dakko jallabiya da singlet ya Saka. Ya faffesa turare ya dauki mukullin motar sa ya fita.

Yana shiga ya tasheta ya nufi unguwar su Kai tsaye. A bakin kofar gate din gidan su Anees ya tsaya da motar sa. Ya kutsa daga ciki ya shiga gidan

Kai tsaye ya nufi sashen Anees din. Ya shige har zuwa kofar dakin Anees din ya murda kofar ya jita a rufe.

Yadda saitin karatun qurani da kiraar maheer mueqly ke tashi ya tabbatar masa da Anees din na ciki.

Anees na cikin dakin nasa a kwance akan gadi. Ya daga wayar sa saitin fuskar sa yana duban hotan Nawraah. Kallontaa yake kamar ita din yake gani a gaske. A tsaye take a cafeteria sanye cikin wasu kaya riga da skirt da mayafi da sukayi matukar amsar surar jikinta.

Gashi yanayin yadda ya dau hoton komai da komai nata ya fito tayi kyau sosai tana daria.

Tun daga kan kafarta yake zooming ya zuwa kan kirjin ta data rike handout awajen ya zuwa fuskar ta.

Ya samu kansa da dan kasa da yin hannunsa yana zoomo wajen mayafin ta data rufe saman kirjin da handout

Bai San meya same shi ba, ya sake zooming yana duban ko'ina na jikinta kamar ita yake gani ba hoto ba

Sosai surar jikin Nawraah ta sake sanya Anees acikin wani yanayi da bai zata ba. Daman yadda takeda kyan hali da kyawun fuska hakama jikinta yake dama ?

Lalle tsarki ya tabbata ga Allah daya halicci wannan halittar Mai halittin abubuwa masu ingiza zuciyar dukkanin wani namijin da zai dora idanunsa akanta sai ya ji wani abu game da ita..
Chapter 27 · 0% Book details