← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 44

Sashe 4

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Masu awara da sauran su an hanasu shigowa cike so kuje ta gate zaku mika kudin ku su baku. Harda me wainar fulawa ma duk akwai. Amman nan cafeteria din bata yayan talakawa bace Irina . Don haka kudin abincin plate daya kadai ya isa ka saya kaya a dinka ma. Haka makarantar take. Sai a hankali. Kudai kawai abunda nake son ku dinga yi shine. Komai rintsi kada ku bari musu ko fada ko cacar baki ta hada ku da sauran dalibai nan. Don harda malaman basu da karfin iKon hukunta daliban don yayan manya ne. Sannan duk wani shirgi da zai hadaku dasu ku tabbatar kunyi nesa da juna. Banda soyayya ko kawance da dalibai yayan masu kudi. Akwai tarin bullies da yawa a makarantar nan lefi kadan zakai akan su sai a koreka, bayan sune da rashin gaskia. Shikenan ruwa ta sha, don haka ku tsaya ku dai ku Saka idanun ku. Ku zama bebaye Kuma makafi masu raunin gani da jin su akan abunda bai shafe su ba Kai har ma da abinda ya shafeku din, ni da kuke gani badan sunkuyar da kan da nake Ina binsu da ladabi ba da tuni nima na dai na zuwa makarantar , Amman dana karance su sai lamarin suke zuwa mun cikin sauki . Sauran abubuwa zan sanar da ku agaba, yanzu kuje bakin gate ku saya abunda zaku saya kuci sai ku tafi inda zakuyi lakca. Allah yasanya albarka a karatun da zakuyi ya kauda duk wani sharri tuggu ko makirci aameen. Bari naje wajen su .. wani abun ya hadaku da sune?"

"A'a komai ya wuce imraan. Mungode maka Allah yasa ka maka da alkhairi ya biyaka Amin "

"Aameen Yaa Rabbi. "

Shigewa yayi cikin cafeteria din yana daga musu hannu. Suka nufi gate din jikin su a sanyaye. Suka siyi awara da gurasa da ruwa pure water kowa daya daya suka koma gefe suka tsakure suka ci suka kora da ruwa sannan suka wuce ajin da zasu dauki darasi na ranar.

To haka rayuwar daukar darasin nasu ya kasance a jami'ar Alharamein university dake yankin naduka crescent.. Suna ganin tarin abubuwa da yawa na kyara da izgilanci amman sai dai su shanye kawai idan an tashi suyi tafiyar su ..

Layla ta tafi gidah Nawraah kuma ta nufi gidan marayun su..

To dama haka rayuwar ta gada. Kowane dan Adam da irin nasa kaddarar.m

Bawa baya tsallake kaddarar sa fyace Allah mahalicci ya Kadarta haka.

::;

Tun asubah data tashi....

_HGL CHARITY FOUNDATION_

_ASSALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH!_
JAMA'A BARKANKU DA _WARHAKA... ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA BADA LADA HADI DA BIYA MUKU DUKKANIN BUKATIN KU DA KUKE FATAN SAMU AAMIN_

GODIA DUBU GA TALLAFIN DA KUKA SAKA NA CIYARWAR AZUMI
INSHAA ALLAHU WANNAN GIDAUNIYAR MAI SUNA A SAMA NA KIRAN MUTANE AL'UMMA MASU SON SAMUN LADAN WANNAN MANYAN AIKI DA MUKE SAKA RAN FARA SHI KAMAR
НАКА

1• DAFA ABINCI A RABA GA MABUKATA RANAR JUMU'AH KO A KAI RUWAN SHA GA MASALLATAI RANAR JUMU'AH

2• HAQA RIJIYOYI ACIKIN KAUYUKA DA UNGUWANNIN DA BASUDA RUWA

3• RABA KAYAN ABINCI KO KUDI GA MABUKATA
MARASA HALI

4•KAI ZIYARA GIDAN MARAYU DA KAI MUSU
ABUBUWAN AMFANI DA SUTURA IDAN DA ME BAYARWA

5• KAI TALLAFI KO ABINCI GA ASIBITOCI WAJEN
MASU JINYA MARASA KARFI..

6•KOKARIN KARASA MASALLACI KO YIN MASALLACI
AWAJEN DA BASUDA SHI...

MAI NERA BIYAR MAI GOMA DiK
YADDA HALI YA KAMA ALLAH YA HADA MU A LADAN DUKA..
JAZAKUM ALLAH BiL JANNAH..
DOMIN SAKA TALLAFI GA ASUSU

9044191709
OPAY
JAZAKUM ALLAH BİL JANNAH💜
[4/28, 1:00 AM] Hafsaat🧕💞: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_7_

:::::::::

*Tunda* ta tashi da asubah bata sake komawa ba. Zuciyar ta baki daya ta mata rauni. Ji take anya ba zata dai na zuwa makarantar nan ba kuwa?

Ta juya ta dubi Amnah da take bacci tana sauke numfashi ahankali. Yayin da take rawar dari na sanyi. Duk kuwa da garin damina ne. An basu sanyi bishiyu nata kadawa. Garin yayi dalam cikin ni'imar Allah..

Nawraah ta kai hannunta akan goshin Amnah ya dau zafi sosai. Hakama jikin nata baki daya ya gauraye da dumi kamar garwashi..

Jikin ta na rawa ta mike ta shiga bandaki ta taro ruwa a roba ta hado da dankwalinta aciki ta nufi wajen gadon Amnah ta saka hannu tana tashin ta ahankali.

"Amnah .. Amnah..." Ta Kira sunanta ahankali tana taba goshin ta.

Faty da Kiran sunan Amnah da Nawraah take tasa ta tashi tana yamutsa fuska. Ta daga hannuwan tana mika hadi da sakin katoton tsaki,

"Meye haka ne saboda Allah ke kullun dan bakin zalinci sai ki dinga tashin mutane suna cikin baccin su kawai don ke bakyaji haba wannan shiga hakki ne" ta karasa fada tana juyawa gefe.

"Kai Faty tsakani da Allah renin hankalin naki yayi yawa. Banda yau yaushe Nawraah ke tashin ki a bacci? Yanzun ma kina ganin Amnah take tashi kekuma kika tashi. Gaskia maganganun da kike suna yin tsauri." Cewar Raudah wadda gadonta ke gaban na su Nawraah.

"Gaskia dai banga wani abun tada jijiyoyin wiya anan ba Faty. Zancen gaskia fa kenan. Amma kiyi hakuri" wasila ta fada tana zaune akan gado hannunta rike da littafin hisnul Muslim tana karantawa.

Nawraah da jikinta sai rawa yake sahoda batason tashin hankali wani sabanin yazo ya gitta tsakanin su daman fatyn taki jinin su tun sanda aka kawo su gidan marayun akace su zauna a dakin su. Batada aiki sai kyara da tsangwarar su. Tai ta so ta takalo abunda zai sasu fada da Nawraah

Amman tunda Nawraah ta fuskanci irin halayen nata sai ta ke binta sannu ahankali sam bata biye mata. Takanyi shiru aduk sanda fatyn zata yita banbamin fadanta. Sai dai su wasila su shigar wa Nawraah. Sannan fatyn take shiru.

"Kiyi hakuri Faty... Wallahi ba da biyu nayi ba. Amnah ce naji jikinta ya dau zafi zazzabi sosai take. Amma kiyi hakuri. Kinji ko?"

Faty taja digon tsaki ta dauki pillow dinta guda daya daga kan gadon ta mike ta fita tana bugo kofar dakin da karfi tamkar zata ballo..

"Allah ya kyauta. Shareta dan Allah... Karki sake bi takanta. Da kanta zata sakko. Uban me aka mata yarinya kullum cikin nunkufurci. " Raudah ta fada tana sakin tsaki itama

"Ai faty ni nakan kasa gane kanta Allah" Wasila ta fada tana girgiza kai

"Ku bata hakuri dan Allah..." Nawraah ta fada idanuwanta na tsiyayar da ruwan hawaye...

"Dalla shareta kiyi abunda kika Saka agaba. Zamu mata magana kakki damu"

Nawraah ta katse hawayen da yake zuba. Ta matsa kusa da Amnah da temakon su wasila suka daga jikin Amnah suka kaita bandaki

"Ina ke maki ciwo Amnah?"

Amnah ta kasa magana ta daga hannu dakyar ta nuna cikinta da kanta.

"Sannu kinji zo muje awanke baki kici abinci kinji"

"Na koshi Adda" Amnah ta fadawa Nawraah hadi da zumewaa ta kwanta saboda yadda jikin ta baki daya yake nukurkusar ta.

"A'a ai bazeyiwu ki ki cin abinci ba Amnah. Bazeyiwu ba"

Su wasila ne suka temaka ta daga Amnah suka sake dauraye mata baki da jikinta sannan suka komai farfajiyar daki. Dan flask din da ake duro musu ruwan shayi ta tsitaya da ragowar madarar su ta hada mata shayi ta karyo biredi ta bawa Amnah..Amnahta girgiza Kai bata so.

Nawraah ta shiga tsoma mata buredin a shayin tana bata. Dakyar ta karbi guda uku na tsoman hudun ta amayo komai gaba daya.

Su wasila suka kintsa wurin. Nawraah ta dauki Amnah dakyar suka nufi asibitin dake cikin gidan marayun.

Likita yayi gwaje gwajen sa yace malaria ce. Aka bata maganguna. Ranar Nawraah bata je.. makarantar ba.

Wasa wasa sai datayi kwana uku bataje makarantar ba. Kullun idan Layla ta biyo mata taga jikin Amnan ne dai har yanzu. Itama sahoda tsoron rashin Nawraah a kusa yasa take komawa gidah taki zuwa makarantar.

Ciwon Amnaah meyakwan yayi sauki sai gaba ya sake yi ma. Tayita ramewa a tsaye kamar zaa hureta ta fadi. Asibitkn cikin gidan marayun sunyi iyakar abunda zasu iya since yafu karfin su don haka su dangana da specialist hospital wato asibitin babban na kwararrun likitoci.

Duk inda Nawraah da Ashfeef suka zaga babu way out. Basuda wata madafa da zasu kama suce zasu samu sauki ta bangaren. Ko zaa yaye musu matsalar lalurar da Amnah ke cikin ta rashi lafiya domin kusan cuwonta na baya da aka mata aiki ne yake dawowa

Dakyar take iya cin abinci ruwa ma sai anyi dagaske take iya sha.

Zaune suke a zauren gidan marayun. Amnah na jikin Nawraah dake jingine da bango. Yayinda ashfeef yake daga can gefe ya saka hannu ya tallabe habarsa yana tagumi.

"Nawraah me kikaci karshe cikin naki ya fara miki ciwo. Likita nata tanbayer ki kinki fada ko?"

Amnah tayi rau rau da idanun tana lankwasa yatsun hannuwanta tace,

"Kiyi hakuri Adda.... Hamma ashfeef kayi hakuri Kai ma"

"Hakurin me? Muna sauraron ki..."

Ta Saka hannunta dakyar tana katse hawayen dake zuba mata tache,

"Irin wannan abunda Ammi take kawomun kafin ta mutu dinnan"

Nawraah ta dubi ashfeef shima yana duban ta muryar Nawraah na rawa tace,

"Wane abu eh Amnah? Me kikaci"

"Wannan abun da ake cin su chakulet acikinsa ko Madara me kwakwa"

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Filled doughnut Amnah..ain kika ci?"

"A cikin sharar can suka Saka suna gama ci fa basu cinye ba suka wullar dashi to shine... Shine na dauka na karkade na ci"

Salati Nawraah da Ashfeef suka kamayi. Amnah ta fashe da kuka tana basu hakuri. Da sauri ashfeef ya sungumi Amnah suka nufi asibitkn cikin gidan marayun.

Sunata haki suka sanar da likitan yadda ake ciki. Likitan yayi dube duben sa sai sunje anyi mata scanning awani asibiyin nan baayi acikin saanan zaa gane inda lamarin ya dosa...

Suka dai durkawa amnah allurar bacci akan gadon marasa lafiya daker acikin asibiyin..

Ashfeef da Nawraah suka futa daga ciki suna tunanin yadda zasu samu kudin da zaa yiwa Amnah scanning.

"Kache su bapoah sani kowanne bai ce komai ba ko?"

"Wallahi Nawraah ba abunda kowanne ya ce. Bappah salisu fa cayayi yana meeting ya katse kawai"

"Subhan Allah ya Allah ka kawo kana dauki"

"Aameen Yaa Rabbi"

"Nawraah..."
Chapter 4 · 0% Book details