← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 44

Sashe 39

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

_K'K'J_
_(M/W/S)_

_BOOK TWO_

_✍️:MX_

_47_

:::::::::

****Suna idar da sallar asubahi suka yi wanka itada hajia Qibdiyya. Daga nan Kuma maaikatan otel din sika kawo musu na karin kumallo.Bayan sunci sun koshi ne suka nufi asibiti Kai tsaye.

Nawraah ta shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar laffaya Mai matukar kyau da tsada.

Abayar na daga daga cikin wadda hajia Qibdiyya ta sassayo mata alokacin da zasuyi tafiyar.

Ba kadan ba Nawraah tayi kyau. Ba kwalliyar da tayi sai kwalli data shafa da Kuma man lebe fari data goga a labbanta.

Hajiya Qibdiyya tayi knocking dakin da Anees yake jinya. Sannan daga bisani sika shiga ciki bakunan su dauke da sallama.

Dr abubukhar da Anees suka hada baki wajen amsa sallamar tasu...

Hajia Qibdiyya ta fara gayshe da mijin nata sannan ta nufi wajen Anees dake kwance idanunsa na bin Nawraah da kallo tun daga kan kafafunta da suka sha lalle ja ta Saka takalmi baki Wanda yayi matukar Mata kyau. Kafafun nata sun karawa takalmin kyau.

Hajia Qibdiyya ta daga kanta tana dubashi.. Anees ya gaysheta yana rike hannunta.

Nawraah ta karasa Dan gefe ta tsugunna ta gaysheta da Dr abubuakhar dollars sirikin ta, ya amsa fuska dauke da murmushi a sake..

Kanta na kasa tache,

"Ina kwana? Ya jiki ? Allah yakara sauki"

Anees yayi kicin kicin da fuskarsa bai amsa ba. Hajia Qibdiyya ta dube shi tana duban Nawraah hadi da nuni da ita,

"Nawraah na gayshe ka tana duban jikin ka bakaji bane?"

Yamutsa fuska yayi yana satar duban Nawraah yace,

"Mami bata ambaci suna na ba fa"

"Toh dole ne sai ta kira sunan ka ta gaysheka ? Haka akeyi ne? Tunda dai kasan a dakin nan Kai kadai ne majinyaci Kuma ta gayshe da abban ku da fari. Ai kasan da Kai take. "

"Hakane, afuwan"
Ya fada yana kokarin mayar da kansa gefe Mami ta sake yin masa magana

"Baka amsa gaysuwa da tambayar jikin naka da tayi ba. "

"Alhamdulillah..."

Ya fada yana karkatar da kan nasa gaba daya... Nawraah ta mike ta koma kujerun dake gefe ta zauna..

"Kina bukatar wani abun ne Nawraah?"

"A'a mami"

"Idan akwai abunda kikeso dai ki magana kinji ko meye"

"Tohm Mami inshaa Allah"

Anees ya sanya hannunsa daya yana girgiza kansa ya ce,

"Abba, Mami"

Suka amsa da

"Naam" a tare... Dr abubuakhar dollars ya Kara da,

"Wani abun kake bukata Anees?"

Anees ya girgiza kansa yace,

"Ina marwaan? Suma suna asibitin nan ko wata kasar?"

Dr abubuakhar dollars ya juya ya dubi Mami dake kusada Anees.yayinda itama kallon nasa tayi sai Kuma ta juya ta kallo Nawraah da kanta ke a kasa"

Anees ya sake numfasawa yace,

"Na tuno sanda muka hango tahowar su shida jamian tsaro. Ciwon dayaji da yawa ne? "

Nanma hajia Qibdiyya da Dr abubuakhar sukayi shiru. Kowannen Su tunanin da yadda zai gaya masa komai s. Gashi bashida lafiya basaso a tayar masa da hankali..

Shirun da sukayi ne gaba daya basu ce komai ba ya sashi sake tanbayar su da,

"Taya akai marwaan ya bari aka aura mun Abar kaunar sa Nawraah ? Bayan kowa yasan irin kauna da burin dayaci akanta na aurenta, Meya faru? What's happening ?"

Dr dollars ya mike ya nufi gaban gadon yana duban Anees dake kwance ya riko hannunsa yana yace,

"Meya faru ne kaketa wadannan maganganun haka?"

Anee ya dube su zaiyi magana hajia Qibdiyya tache,

"Haka gaisuwar matarsa ma bai amsa ba. Wani sabon atitude ne ga yana bayarwa . Ko magani ne ko allurori ne sike sashi"

"Definitely. Baari a kira doctor din yazo ya sake duban shi"

Anees yayi murmushi jin maganganun da suke fada. Ya daga Kai ya sauke akan Mami yace,

"Mami"

"Naam Anees"

"Abba" ya fada yana duban Dr abubukhar

"Naam Anees. Wani abun ne? Ko kan kane yake ciwo"

Anees ya sake sakin tattausan murmushi kafin yace,

"Ba sai Kun kira likita ba Mami kalau nake... So nake nasan dalilin dayasa aka hada aure na da Nawraah. Da babban dalilin dayasa marwaan ya amince aka aura mun, sannan Taya akai Nawraah ta amince aka daura auremu. Bayan tarin kiyayyar da take mun. Inason nasan meysaa. Kar ku boyemun komai. Domin rashin maganar shike sakawa zuciyata radadi. Na rokeki da girman Allah kada ku boyemun.."

Hajia Qibdiyya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya mai dauke da tarin amsar tambayoyin da Anees yayi musu. Amman bakinta Sam ya gazaa furta bayyana komai. Ya mata nauyi matuka.

Don haka ta Dan kallo Mai gidanta Dr dollars da suka hada idanu

"Anees ka rufe ido kayi bacci Dan Allah. Da alama wani side effect din maganin ne yake damunka ko allura. Bari dai akera su. Ina wayar ne kira likitan"

Ya daga wayar da ake kiran doctors din idan emergency issues ya taso. Anees ya daga hannu ya riko na Dr dollars yana girgiza Kai. Hawaye masu matukar dumi na zuba daga idanunta.

Jikinsa har wani rawa ya farayi yana zillo yace,

"Kada ka kida kowa Abba. Dukkan ku boyemun kawai kukeyi... Amma marwaan ya rasu ko? Marwaan ya rasu ne shysa aka aurawa Nawraah ni. Marwaan ya rasu ne shysa naga banganshi Tare da ku ha. Marwaan ya rasu tabbas shi yasaa kuka kasa cewa komai duk tanbayar da nake. Yanzu sun kashe min marwaan? Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun "

"Dena kuka Anees. Wayace maka marwaan ya rasu uhm? "

Anees ya kadaa kansa hawayen nata zuba daga idanun sa yace,

"Bakwaso ku gayamun ne don kada na tada hankali na. Saboda halin da nake ciki .. Amma tabbass marwaan ya rasu. Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Subhan'Allah. "

"Kayi hakuri Anees ... Ba Dan wani abun aka boye maka ba. Sai Dan halin da kake ciki. Tunda Kai ma coma ka shiga baka farfado ba sai bayan munzo nan kasar ta turkiye...sun sassare ka yayinda shi Kuma sika harbe shi. Tun Muna yankin bunza ma da aka kaiku aisibti shi ya cika... Batun aurenka da Nawraah Kuma zamu iya kiran sa daga Allah ne. Dubada bamu taba sanin kana kaunar taba sai da muka dauki wani littafin ka da wayarka da hirar chatting dinku da marwaan din. Sannan itama a tata wayar ta bamu voice notes mun saurara ne daga maganar auren ku da kaunar ta da marwaan din yayi yace ko bayan ransa da sauran su. Sannan kana dauke da cuwon damuwa ya fara maka illa ma Wanda daga bisani likitoci ma suka sake fadar damuwar taka,sai muka nefi Nawraah. Muka roki alfama awajenta . Ta Kuma amince zata aureka.. sai Kuma abun farinn ciki shine an kama Alhaji sambaso don yanzu hakama ancemun surutai kawai yake na daga abubuwan daya aikata, donya samu tabin hankali ma yana gidan yari. Sannan matar sa itama tana gidan yarrin Amma da Tara zaa saketa, yayinda mata ga bappan Nawraah da ta fada hada Kai dasu .itama tana Tara da zaman kurkurku na Dan wani lokaci. Kai na karkare maka zance dai duk wani Mai hannu da ruwa da tsaki acikin lamarin hukuma ta cafke su. "

Anees ya kasa ceaa komai. Bayan wani lokaci kankani Kuma ya fashe da wani irin Kuka Mai dauke tarin damuwa. Yanayi yana jijjiga Kai yace muryarsa na rawa yace,

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun. Marwaan fa. . Marwaan fa Mami. Na shiga uku. Marwaan fa amini na, abokin shawarata, dan uwana Subhan'Allah "

Su hajia Qibdiyya da Dr abubuakhar na bashi baki suna ce masa addua zai yi masa ba kuka ba...

Anees ya dade yana kuka yana maganganu , har lokacin shigar likotociin sa yayi, suka shiga suka duba abunda zasu masa. Kuma suka sarqafa masa allurar bacci nan da nan kuwa yayi baccin

Hajia Qibdiyya da dr dollars na maimaitaa zantukan. Nawraah na jinsu a gefe . Hawaye ne ke zurara mata na tunowa da tayi da marwaan....

::;;;

Hakika lamarin ya daki Anees sosai, don sai da ya yi doguwar suma bayan ya tashi daga allurar da suka masa ta bacci...

Yayita surutai gwanin ban tausayi. Ya dau tsawon lokaci na sati biyu kafin komai ya lafa masa. Don har yana iya tashi ma da sandunan karfe ya tsaya...

Hajia Qibdiyya da Dr dollars su biyu suka zauna awajen sa suna jinyar sa . Nawraah ce Mai sayo abinci yanzu tasan kan gari tana Kuma rage wasu abubuwan. Da daddare take tafiya can hotel dinsu ta kwana.

Yayin da bayan asubah daga gama kintsa komai sai ta koma hotel din nasu...

Anees dai daren ranar ya badewa idanunsa kasa. Yana muza yatsu ya dubi Mami yace,

"Mami..."

"Naam auta"

"Bacci kikeji Kalli idanuwan ki. Hakama Abba"

"Ba wani bacci ai Muna samun bacci Anees.."

"Amma ai da wahala"

"Wadannan maganganun da kakeyi na meye?"

Ya dan sauke zuciya yana satar kallon Nawraah da tayi kicin kicin da idanu yace,

"Yarinyar nan yau ta zauna itama ta kwana. Ku kuje ku huta"

Hajia Qibdiyya ta bude baki zatai magana Dr abubuakhar dollars yace,

"Hakane ya kamata Kam. Daughter yau sai kiyi hakuri ki kwana kinji?"

"Tohm Abba inshaa Allah" Nawraah ta fada kanta a kasa.

Hajia Qibdiyya ta dankarawa Anees harara tana duban Nawraah tace,

"Zaki kwana din habibty?"

"Eh Mami ba komai"

"Allah ya miki albarka... Kinji"

"Nagode Mami"

Anees ya daga hannu ya sosa keyarsa yana gyara kwanciyar sa sosai akan gado .

"Mariyah muje ko?"

"Tohm Abban su"

Hajia Qibdiyya ta mike ta sakala jakarta. Ta matsa wajen Nawraah tana sake sanar mata komai idan emergency ya tashi.

Nawraah ta musu sallama har bakin kofa suka tafi. Yayinda ta koma ta zauna akan kujera tana danna wayarta...

Anees ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana gyara saitin kwnaciyarsa. Idanunsa na kanta yace,

"Naw.....Rahhh..........

KUZO MU HADA KARFI DA KARFE MU DANDALI KUDI A TELEGRAM... WANDA NOTCOIN TA FASHE DASU ZASU BAMU LABARI. YANZU KUMA GA HAMSTER KOMBAT YAR UWA KINA ZAUNE IDAN BAKYA AIKI KI RIKA TAPPING NAN DA NAN KIGA KIN TARA COINS DIN KI. IDAN TA FASHE KEMA KI DANDALA...
Chapter 39 · 0% Book details