← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 44

Sashe 10

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hirar duniya suke , labarai kashi kashi wani na ban tausayi, wani bandariya wani Kuma ban haushi.

Faty na daga can nesa dasu kanta na kan ceiling tana kallo. Baki dayan tunaninta Kuma baya nan yayi wani wajen. Gangar jikinta ce kawai.

Nawraah ta daga kai ta dube ta ta sunkuyar da shi kasa da sauri. Yadda faty bata aminta da su ba kawai take jin ba dadi

Kowa na cikin gidan marayun tana mutinci da shi suna magana. Amman itada Amnah ne kawai ta tsana. Ta rasa wani dalilin ne oho.

"Menene Nawraah?"
Raudah ta tanbayeta cike da damuwa.

Wasila dake kitse kan Amnah ma ta daga kai ta dubi Nawraah tana tanbayar ta itama,

"Yanayinta ya canza kam wani abun ne Nawraah?"

Nawraah ta girgiza Kai da sauri tana mayar da hawayen dake son bijere mata ya zuba tace,

"Ko daya.... Kawai dai Ina mamakin abunda yasa faty bata son shiga harkata ni da Amnah abun yana damuna bansan ko mun mata wani lefin bane amma gaskia banajin dadi"

Wasila da Raudah suka Kalli juna suna girgiza Kai

"Ki ma dai na bari wannan abun yana damun ki. Normally Faty ta saba haka. Mu kara bata wani lokacin zatai adjusting don kanta" cewar Raudah

"Toh Allah ya amince ", Nawraah ta amsa mata

"Amin inshaa Allah.. kinsan yanayinne sai a hankali. Kuma kunzo Kun sameta alokacin da take kunci na zuciya. "

"Subhan Allah meya faru wasila? "

Wasila ta daga kai ta sauke cike da tu'ajjabi tache

"Tun tana karama take gidan marayunnan, Don ta rigamu zuwa ma kusan ance sune fist set na wadanda aka bude gidan marayun da su. Duk Wanda suke tare yara alokacin haka aka dinga dauki 'dai 'dai dasu kowanne mutane sikace sunaso suka dauka Amman banda ita.... Labari yazo mana cewa koda yake ta gaya mana Muma alokacin da aka kawo mu. Take cewa batada saa . Ba Wanda ke kaunar ta da zai dubi maraicinta ya dauketa itama akai ta gidah tashiga ciki itama yau gashi ace tanada yan uwa. "

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun..." Nawraah ta fada tana girgiza Kai.

"Ai abun akwai damuwa sosai. To haka shekarun sikai ta shudewa... Zuwanmu ba dadewa wasu zuriah suka zo haka kaman yare kaman yan kudu kudu dinnan dai. Amman musulmai ne Kuma suna jin hausa sosai suka ce suna so suyi adopting dinta suna son su mayar da ita yar su tunda basu taba haihuwa ba. Faty nata murna suka dauketa. To abu dai kamar almara washe gari Kiran sallar asubah na fari sai gashi sun dawo ita wai basa sonta gaskia, anan take suka dauki wasu yaran har biyu har yanzu Kuma suna wajen su. Babban abunda yafu damun ta ma shine cewar wai ita din yar tsintuwa ce baa san daga Ina zuriyar ta suke ba baasan daga inda ta fito ba. Kawai an ce an ganta acikin shawul tana jaririya..."

"Hasbun Allahu Wa ni'imal wakil...Allah sarki Faty. Gaskia gaskia lamarinta akwai tausayi sosai..."

Tamkar ance ta bude idanunta ta bude da sauri tana duban su. Ta mike daga kwancen da suke tayi kan Nawraah tana nunata da yatsa,

"Ya akai? Gulmar me kike? Magana ta kuke ko? Wato ke har kin isa kin Kai kina zance na ko? Har tausayi na kike. Wacece ke? "

Nawraah ta yi kokarin riko hannun faty , Faty ta fuzge da karfi ta fita.. suka bi bayanta da sauri dukan su banda Amnah dake wasa da kayan wasanta na mota da yartsana..

Can barandar sama faty tayi tana hawaye sosai,

"Gwara ma na mutu kowa ya huta. Gwara ka na mutu na bar muku duniyar kune yayan da ake so. Kuna da iyayen kunada masu son ku"

Magana take sosai da karfi har ta karasa wajen benen barandar karshe daga ita sai Katanga ana hango gidan mutane na unguwar

"Faty dan Allah kiyi hakuri" Nawraah ta shiga nanatawa ganin fatyn na niyar jefaa kanta kasa.

"Kun tsane ni. Badai nice kuke tausayi ba? Nice marar gata acikin ku, ni ce marar asali ko? Banza a wofi, To albishirn ku zan bar muku duniyar sai ku kwadanta ku ci"

"Innalillahi Wa inna ilaihi rajiun faty meye haka? Ina mike da gata? Duk rashin gatar ne ya sa muke anan gidan gaba daya. Yadda baki da iyaye haka dukkanin mu muke.Na sha sanar da ku, musanman ke ba sau daya ba ba sau biyu ba, Ni tsabar rashin usuli ma daga titin da mota ta kade iyaye na nice nayi rai, mutanen wajen sune suka kawo ni nan gidan marayun kasancewar baa san yan ina bane mu , kawai mun taho a titi a motar haya aka samu hatsari kowa ya rasu na motar sai ni da ke da sauran kwana agaba... Toh dukkanin mu Faty, Jirgi daya ne ya debe mu..."Raudah ta fada da karfi tana runtse idanunta

"Faty na dan Allah kiyi hakuri kinji? Wallahi Muna kaunar ki sosai...kamar yadda Raudah ta fada, Dukkanin mu nan baki daya bamu da wani gata sai Allah mahaliccin mu. Zan iya cewa ma kinfini gata, don kuwa ni gidan marayun ne dakansu suka dakkoni suka kawo ni cikin ku, kasancewar mahaifiyata ance ina karama ta rasu batada ishasshen hankali acikin kasuwa muke rayuwa. To faty tsakani da Allah wannene yafi wani gata acikin mu? Na sha gaya miki. Munyi zantukan nan ba sau daya ba tun ma kafin zuwan su Nawraah. Kowa da yadda Allah ya Kadarta masa rayuwar sa. Idan mukayi hakuri sai mu cinma burin da muke fata agaba...

"Abu na biyu, Nawraah ce take cewa yadda bakya kula su abun na mata video tana so ku dinga mutinci kamar yadda kik1e da kowa"

Faty ta juya ta dube su tana girgiza Kai tache,

"Komai ta hada, makarantar yan gayu, kawaye irin ku, kawaye acikin makarantar gayun da suke, ga yan uwa tana dasu na ciki daya dana jinin zumunta. Dole ai taji tausayina saboda ni yar tsintuwa ce banda kowa da komai"

Nawraah na goge hawayen ta tana karasa matsawa wajen Faty tace,

"Wallahi kilama kin fi ni gata, ni da kike gani rayuwata gaba daya data yan uwana acikin hatsari da kunci take, hakika Muna da iyayen a baya. Amman Allah ya karbi abunsa. Ya zama na sai mu da yayan kadai, Shi yake mana komai shine bango majinginar mu. Shine komai namu na rayuwa. Wallahi bashida lokacin kansa sai namu. Mutuwa tazo ta sake mana yankan kauna ta dauke shi. Ya zamana sai ni da Amnah da yayan mu ashfeef. Yan uwa baki daya sun juya mana baya duk wata kadara ta mahaifin mu an kwaceta saboda bamuda arziki. Na takaice miki zance ni da Kai na na kawo mu nan gidan marayun nace zamu zauna saboda bamuda inda zamu zauna. Faty har zaman daki daya tare da tumaki da kiwo mun yi. Ba window a dakin haka muke kwana ba wajen wanka a waje mukeyi, muna karewa da zani, Ba wajen bandaki sai dai muyi a leda mu jefar, Abinci baka samu. Baki daya ba kwanciyar hankali.Yan uwan iyayen mu baki daya ba sayi damu. Dukkan su kowanne yaki amincewa ya dauke mu, mu zauna awajenn sa. Baki daya suka ciremu daga cikin ahalin su. Mutum daya ne zakka acikin su, yana zuwa shi wannan bayada halin rike mune da tuni ya rikemu sai dai Kash, baiyi sa'ar matar aure ba, Faty, Cikin kankanin lokacin da baifi shekara ba da kwanaki. A kub'i a kub'i Allah ya amshi ran iyayen mu da yayan mu baki daya ni da kike gani dawowa nan muksi daga baya lokacin iyayen mu na darai. Asalin mu yan yankin bunza ne...... Zuriyar hamidniyya lebanon. Idan kina raayi Kuma kina bukata. Ni Nawraah zan zamar miki kanwa agare ki da yardar Allahzakuma ki same ni me cikar alkawari. Wallahi summa tallahi bantaba ji na tsaneki ba a raina faty, Alkhairi ne kawai ya hada jini na da naki. Don naki jinin a tsaneni ko a tsameni ace baaso. Nafuson na zauna da kowa lafiya domin baki daya duniyar kankanin lokaci ne mai wucewa cikin yan kalilan dakikai "

Faty ta sharce hawayen ta da bayan hannunta tana duban Nawraah. Ta girgiza Kai tana hawaye sosai tace,

"Ban tsane ki ba nima haka zalika... Kawai banason na sake sabawa da wani ne azo a rabamu daga karshe... Kinganni nan banda saa. Dani aka dawo wannan gidan marayun da sauran yaran dika aka dinga dauki dauki daya daya aka Barni ba Wanda yake so na. Ba Wanda yake son hada zuriyar da son daukata, gaba daya kan baa so na, an dauke ni ma an dawo da ni haka kawai. Wannan abun yasa na tsani komai. Baki daya dukkanin lamurana suka fita da Kai na. Babban abunda yafu damuna ma irin nidin yar tsintuwa ce da batada usuli gaba daya kowanne acikin ku maraya ne. Amman ni fa? Bansan kowa ba. Kilama cikin she....

"Shhh karki karasa Faty. Kedin cikakkiyar mace ce me cikar albarka da alkhairi Wanda Allah ya halitta da so da kauna... Yadda kowa yake haka kike. Kilama kin fimu kusanci wajen Allah. Wallahi faty. Da ace kana iya tsara rayuwar ka daban kayo rayuwar ka smoothly ba wani matsala lokaci daya masifu suka dinga faruwa kinji Allah! Da irin rayuwata a baya. Wallahi zon fison ace irin rayuwar ki ce dani. Banda kowa bansan komai ba. Wallahi sai yafu mun Amman astagfirullah ni da kike gani Ina cikin wata irin rayuwata da yan uwana biyu da suka raye, Amman nasan da yardar Allah. Allah bazai bar mu dukan mu da ku haka ba, inshaa Allah nan da kankanin lokaci komai namu zai zama tarihi Kuma zaku zama yan gata kamar kowane 'da dake gaban iyayen sa."

Faty ta yi murmushi tana girgiza Kai. Nawraah ta dubeta itama tana murmushin taci gaba da cewa,
Chapter 10 · 0% Book details