← Book details Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 44

Sashe 1

Kwankwason Jimina Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[4/18, 1:24 AM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*

_*BOOK TWO*_

_paid page :001_
_

____

*welcome to Al-Haramein university Naduka* shine kalmomin da wani babban majigi kusurwa kusurwa yake rubutawa yana kuma haska kowanne sashe na cikin makarantar.

Daga can gefen inda suke gangarawa suna tafiya.... Wani babban majigi ne na daban dake rubuce da manyan bakin *faculty of social sciences* ... Daga can gaban sa Kuma wani tankamemen waje ne a killace an rubuta da,

*DEPARTMENT OF CRIMINOLOGY/SOCIOLOGY*

Abunda ke rubuce kenan da manyan baki masu sheki da nuna haske, a jikin wani katafaren signboard na karfe mai tsada. Wanda shi kansa signboard din kasan yaci kudi ...

    Wani hadadden gini ne tamkar irin gidajen nan na Cappadocia dake Istanbul . Tsaf zaka dauka hotel ne ma saboda tsananin yadda yake da kyawu. Can suka nufa inda sunan course din da zasu karanta yake.

Ga manyan motoci nan a faffake an faka su a harabar adana motocin bangaren. Tundaga kan furofesoshi kowanne da sunan sa a wajen da motar da zasu faka. Daga rank din furososhi zuwa daktoci da manyan students na postgraduate students zuwa undergraduates students...

Sai da suka tsaya suka bawa idanunsa abincinnsa. Dakyar Nawraah ganin lamarin ba na karewa bane yasa ta janye hannun layla suka shiga cikin department din.

Mai karatu idan nace zan zayyano muku adadin kayyakin kudi masu tarin yawa da aka kashe wajen zuba ado a department dinna Kai dama makarantar bakk daya sai ace sharri ne.

Amman duk inda makaranta ta manyan kasashen duniya da suka hada kai suka tunbatsa da kudi wannan makaranta ta kai, Kai harta zarce sauran wasu makarantun.

Sauran daliban dake ciki suka tsaya suna duban su Nawraah cike da kyama. Kayan su ba designers ba sannan kallo daya zakai musu ka tabbatar yayan malam ne mai dattin hula na soro.. (talakawa)

Dube duben supervisor office suka shiga yi sun rasa . Layla ta ceda Nawraah,

"Mu tambayi wadannan daliban mana su nuna mana ko?"

"Laylus da dai mun kyalle su kawai dubu yadda suke kallon mu tamkar sunga Kashi. Haba mana"

"To ai dole suyi tunda ba taba ganin mu sukayi ba. Uwa uba ba Wanda zai Rena mu. Kinsan dai wannan kayan na jikin mu mun kashe wajen dubu uku uku na kowa "

Nawraah tayi murmushi kawai. Suna rike da hannun juna suka nufi wajen wasu yammata su hudu. Yan gayu ne na bugawa a jarida . Kowacce sanye cikin tsadaddun kayan sawa. Dauke da manyan wayoyyin zamani a hannun su.

"Assalamu alaikum" suka hada baki wajen musu sallama

Yammatan suka tsaya suna binsu da wani irin kallo na renin hankali. Guda daya ce ta amsa musu sallamar itama ba wai fuska a sake ba

"Tambaya muke" Cewar Layla.

Daya daga cikin yammatan ta daga Kai tana duban tundaga tafukan kafafun su ya zuwa fuskar su tace,

"Ba ku akayi wa warning bane wai?"

"Warning Kuma?" Layla ta tambaye ta tana duban Nawraah..

"Eh . Yan talla ne mana. Na gane fuskokin ku ai. Ke kaman awara kike sayarwa, ke Kuma bandashe. " Ta fada tana Mai nuni da kowaccen su

Layla ta bude baki zatayi magana. Nawraah ta riko hannunta da sauri ta kakaro murmushi tace.

"Mu ma dalibai ne kamar kowa.. kaman yadda kowannen ku yake cikin jami'ar. Sai dai Alhamdu Lil Laahi. Mu yan tallafi(scholarship) ne ba iyaye ne suka biya mana kamar ku ba..."

Tana karasa fada ta ja Layla suka bar wajen.

"Ki kyale ni naje naci haka kaza ta uban su"

"Calm down Laylus. Maganar ta wuce. Bamuda wani option dai illa mu basu hakuri Koda wani abun zaj taso na daban su iyayen su sunada shi suna cikin halin samu. Mu kuma namu iyayen na cikin halin rashi. Allah yasa mu dace,

"Aamin Nawraah. Shikenan tunda kin gama magana . Amma gaskia ba zanyi tolerating ba gaskia. "

"Inshaa Allah. They won't be next time "

"Tohm Allah ya amince din. "

Suna tafe suna karanta dukkanin abunda aka saka a bakin ofishin malamam. Da haka har suka karasa kan sunan ....

"Layla Auwal... Da Kuma Nawraah Junaid...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[4/18, 5:26 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*

_*BOOK TWO*_

_paid page :002_

____

"Layla Auwal Hamidniyya... Nawraah Junaid hamidniyya?"

Suka jiyo wata siririyar muryar a bayan su tana kiran sunayen su. Da sauri suka juya.

Wata matashiyar budurwa ce haka ba zata dara shekarun su ba. Sanye cikin riga da skirt ta nannade jikinta da wadataccen mayafin . Fuskar ta dauke da gilashin na karas agajin gani...

"Ga mu" Layla ta amsa ta .

Nawraah ta ja ta tsaya itama suna jiran cewa ta bakin ta.

Yarinyar ta daga hannu tayi nuni da wani ofishi a bayan su tace,

"Ana kiran ku a dean's office."

"Toh Allah yasa kalau" Layla ta fada tana sauke zuciya.

Nawraah ta juya tana duban yarinyar data shige su tayi tafiyar ta.

Ofishin suka nufa suka shiga ciki

Hadadden office ne mai matukar kyau da ya sha kaya masu matukar tsada da kyau.

Bakunan su dauke da sallama suka shiga. Na'urar sanyaya waje ta doka musu sanyi mai matukar dadi da ratsa jiki.

Zaune take akan kujerar dean. Kai ka dauka itace dean din.sanye cikin doguwar riga baka ta abaya design din Dubai ta nade kanta da mayafin abayar. Yayinda gaban ta dan zame shi ana hango gashin ta,

Nawraah ta sake jin matar ta sake futa a ranta. Musanman da tayi wannan shigar tamkar ba matar aure ba. Sam ba sanin darajar igiyar aure a rayuwar masu kudi?

"Kece Layla ko. ? Ke Kuma Nawraah?" Ta tambaye su tana mai nuni da nawraah a matsayin itace layla . Ta Kuma nuna Layla ta ta nuna ta itace Nawraah?

Nawraah tayi murmushi tana sake jinginar da kanta ajikin bango tace,

"Mune. Itace Layla ni Kuma Nawraah"

"Ahh Mashaa Allah Ashe ban manta ba.. da farko dai yadda kuke kallon nan nawa magana ta gaskia ba nice dean ba. Amman zan iya cewa mukamina a jami'ar nan ma yafi ta dean. Kun gane?"

"Eh" suka hada baki wajen amsa ta.

Dr bintu ta mike tsaye daga zaunen da take tana duban su tace,

"Maraba da shigowar ku jami'ar Al-Haramein dake nan babban birnin Naduka... Muna farin ciki da kasancewar ku atare da mu. Don kaunace tasa muka baku gurbin karatu anan din daga yau yazuwa ranar daza ku kammala karatun ku idan Allah ya amince"

"Aamin"suka amsa ta

Landline wata waya dake kusa da ita ta janyo tasaka wasu numbers ta kara a kunnenta ba jimawa ta katse kiran bayan tace da na wayar,

"Zo yanzun nan Ina office"

Gyara zamanta tayi tana duba agogon wutsiyar hannunta sai ga shigar wani yaro nan ya dan saka kayan sa masu kyauu .yanada Kuma da kyawun sa tubarkallah

"Ma! Ga ni"

"Sannu da kokari"

Matashin ya sosa keyar sa, Yana duban su ta gefen idanu.

"Bakomai Ma.."

"Yauwa kasan meya sana kira ka?"

"Aa"

"Well just the usual ne dai ... volunteer work ne kawai.. zakai da wannan students din"

"okay ko'ina da koina za'a nuna musu?"

"Inda ya dace ..wajajen zaka kai su "

Har ya Kai bakin kofa sai ya juya wajen su Nawraah,

"Kune ko?"

Nawraah da Layla suka dubi Dr bintu dake gyara zaman mayafin ta. Murmushi tayi tace musu,

"Zai nuna muku bangare bangare na cikin jami'ar ne."

"Okay mungode. "

"Ina sauran mazan?' dr bintu ta tambaye su ganin bata ga su Ashfeef ba"

"Zasu zo suma anjima kila"

"Toh Allah ya amince amin"

Fita sukayi... Saurayin na gaba suna biye da shi abaya. Yanata kalle kallen lungu da sako kamar matsoraci ganin ba kowa awajen ya juya ya ce da su,

"Sunana Imraan....

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[4/18, 5:44 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*

_*BOOK TWO*_

_paid page :003_

____

"Sunana Imran Abbas... Kuma ni ma dalibi ne kamar ku acikin jami'ar nan."
Chapter 1 · 0% Book details