← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 45

Sashe 9

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan m samir ya fito daka toilet karema dakin kallo yayi lokaci daya kuma yayi tsaki domin bashi da kayan sawa a nan, jikinshi daure da towel ya fita falo yaga sonia tana kallon news sunanta ya kira tare da fadin bani da kayan sawa a nan, murmushi tayi tare da tashi ta nufeshi tayi hugging dinshi tana fadin karka damu ai babu inda zaka nafi son ka zauna a haka inyi ta kallonka.... Dai2 lokacin dad dinshi ya shigo da yake sun bar kofar falon a bude jin sallaman dad dinshi yasa ya dan jata baya amma saita kara manneshi tana fadin come on, dad dinshi ranshi bace ya juya ya fita daka gidan, ganin haka yasa ya ture sonia yana fadin mai kikeyi haka? Bakiji dad dina bane? Tace naji toh mai kakeso inyi mishi? Magananta ta dan bashi haushi amma saiya dake yace daya shigo saiki sakeni sannan ki dawo ki zauna kalla fah yanda nake daka ni sai towel so kike yayi tunanin ko wani abu mukayi? Tace sai me dan yayi tunanin hakan ni ba damuwa ta bane, cikin bacin rai yace look sonia inaso ki sani idan ke ba damuwanki bane toni damuwa nane, domin addini na bai ce inyi haka ba nd..... Ta dakatar dashi tare da fadin ya isa haka ni nace ka shiga cikin addininka mai takura ma mutum addinin da baya ba mutum yancin kansa so ya kamata ka gane gskya ka dawo christen dan shine hanya mai bullewa, shuru yayi yana kallonta cikin mamaki harta gama, sannan yace u r wrong sonia addinina shine addini mai bama mutum yanci addini mai haske dat islam addinina ya haramta zina sai yasa Allah yaba namiji daman auren mata har hudu domin gujema baraka...... What u mean ur religion allow u to marry more dan 1 women? Kai ya daga mata alaman eh, cikin zafin rai tace what kind of religion iz dis how can man marry 4 wife dan murmushi tayi mai zafi sannan tace kana nufin idan mukayi aure zaka kara auran wata?? Kai ya daga mata tare da fadin bani da burin auren mace fiye da daya amma ban san abunda Allah zaiyi ba, cikin rashin fahimta tace bata ganeba, yace idan Allah yasa zan kara zan kara in kuma bai sa.... Ta dakatar dashi cikin kuka tare da fadin ita ba zata iya aurenshi ba dan me zaice zai kara wata mace bayan ita, sannan yasan ita a nata addinin mace daya ake aure kallonshi tayi cikin fushi tace bazan zauna dakai ba yau zan tafi sannan bazan dawo kasar nan ba ko inzo gareka ba har sai ka canza addini domin bazan iya auren muslim ba tunda haka addininku yake tana fadin haka ta fita yana ta kiranta amma bata tsaya ba gashi babu kaya a jikinshi, koda ta fita daukan jakarta tayi a motar daya kawo su ta wuce, zama yayi ya daura hannu a kai alaman damuwa lokaci daya kuma yayi tsaki tare da ware hannu alaman ban damu ba daki ya koma ya dauko waya ya kira waya dan a kawo mai kaya yana gama fadin abunda yake bukata ya kashe waya

Jawaheer kullum bata fita sai dai tazo wajan dakin nan taita kallon mutane masu wucewa yauma tana zaune har yamma taji gaba daya zaman ya isheta dan haka ta fito waje ta tsaya ta gaban gidan tana kallon gidan dake kallon nasu domin gidan ya birgeta yana yin yanda aka tsara gidan a hankali ta furta duk yanda akayi suma nan kasar nan area din yana daya daka cikin wajan da masu kudin kasar suke dan gaba daya tsarin gidajen dake wajan gwanin sha'awa, ganin giftawan mutum tayi daka gidan dan murmushi tayi tare da fadin bari inyi karan bani in leka gidan ko zan saba dasu, dan zama mutum daya babu dadi, dan shuru tayi tana nazari nan fah kasar waje ne ba nigeria ba toh in taje mai zata ce musu? Wata zuciyar tace kije may be ma sun san m samir dinki dariya tayi lokaci daya kuma ta nufi gidan, koda ta karasa kofar gidan mutumin da taga ya gifta ta gani yana tsaye da ledoji a hannunsa alaman yana jira a bude mai kofa cikin harshen turanci take cemai sannu ni..... Bata kai ga karasa magana ba aka bude kofar tsayawa tayi cak tare da zare ido tana nuna wanda ta gani da hannu alaman kai ne ko gizau ne, lokaci daya kuma tayi murmushi tare da fadin no no ido nane ba m samir bane mai yasa idona kamin Karya mutumin da ganinshi ance min bamai yuhuwa bane sai gashi da towel a gaba na, duk cikin harshen turanci take maganan shiko mamaki abun ya bashi ganin yanda take mamaki kaman bashi ta gani ba, lokaci daya kuma yayi dariya tunawa da yayi itace shima yake nema matsawa yayi kusa da ita tare da riketa ya hura mata iska a fuskanta yace nine M samir nine a gabanki fadowa tayi jikinshi ganin kaman bata motsi yasa ya fara jijjigata......

*maryam obam*
[16/01, 17:56] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 12

Daukanta yayi cak ya shiga da ita cikin gidan bai ajiyeta ko ina ba sai cikin dakinshi akan gadon dakin ya kwantar da ita, mutumin daya kawo mai kaya ya ajiye ya wuce, toilet ya shiga ya dibo ruwa a hannunsa ya yayyafa mata wani irin ajiyan zuciya ta sauke mai karfi, tare da bude idonta dishi2 ta fara gani fuskan M samir ta gani wanda yasa ta bude idan nata da sauri tana fadin bashi bane bashi bane mafarki nakeyi taya zan ganshi lokaci daya ba tare da nasha wahalan da ake fadamin ba, ganin kaman tana kwankwanto yasa yakai bakinshi cikin nata ya fara kissing dinta, gaba daya komai nata ya tsaya cak, saida yayi kissing dinta na wajan 1minute sannan ya saketa dan ya tabbatar yanzu zata cire komai da take tunani tasan shi dinne dagaske, amma ga mamakinshi sai yaga ta tsaya cak, kai ya dan buga wanda hakan ya nuna mishi shine first time da aka taba kissing dinta dan murmushi yayi tare da jan hancinta da hakorinshi ihu ta saki, tana kallonshi yace yes nine a gabanki, nunashi ta farayi tana murmushi lokaci daya kuma ta fara kuka, kallonta ya tsayayi yana mamaki, rungumeshi tayi tana ci gaba da kuka ta fara fadin ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa na, duk da nazo nan kasar dan in ganka amma ance min ganinka ba abu mai sauki bane kullum nayi sallah sai na roqi Allah domin ya nuna min kai koda sau daya ne a rayuwa na, na ganka a asibiti lokacin ban san dalilin da yasa na kasa yi maka magana ba, saj gashi yau Allah ya nuna min kai gaka a gabana jikina a cikin naka duk da bada son raina nayi hakan ba, tsabar farin ciki ne.... Cire jikinta tayi daka nashi taci gaba da fadin bana kallon ball amma ranan dana fara kallo na ganka lokacin kaci ball naji anata kiran M samir tunda na ganka naji Allah yasa min sonka, idan ina magana iyayena suna min kallon kaman bani da hankali amma ni daya nasan abunda nakeji bani da wani buri daya wuce in zama matarka, amma ance min hakan bamai yihuwa bane saboda celebrity bazai taba auren yar nigeria ba, koda burina bai cika ba zanyi farin ciki na ganka kuma kaine namiji daya daka dara kissing dina na farko a rayuwa na, dan shuru tayi tana kallonshi shima kallonta yakeyi lokaci daya ya fara magana cikin turanci shima yace lokacin dana ganki a hspt irin kallon da kike min nasan kina da magana a bakinki domin na saba ganin mutane kala2 amma ke irin naki kallon na daban kike min nd kuma lokacin da zamu tafi naga sanda kika fadi kina kuka..... Dan shuru yayi sannan yayi ajiyan zuciya yace ya sunanki? Tace jawaheer kai ya daga tare da kara nanata sunan yace nice name, amma baki kama da yar nigeria ba kinfi kama da yar dubai, murmushi tayi cikin jin dadi, yaci gaba da fadin ngd da kauna da kuma so da kika nunamin amma am sorry to say ina da wacce nakeso na gode da kauna, idonta ne ya kada yayi ja kirjinta ya farayi mata zafi lokaci daya taji wani abu yana son taso mata, ganin halin data shiga yasa ya tashi ya dauko mata ruwa ya bata amma bata ma san yanayi ba ganin haka ya bude ruwan yasa mata a baki babu shiri ta bude bakin ta fara sha, lokaci daya kuma ta kawar da goran ta fara kuka mai karfi tare da ruko hannunshi ta fara fadin bana tunanin akwai wacce zata soka kaman yanda nake sonka wlh son gskya nake maka bana wasa ba ka kalli idona babu komai sai sonka, tashi yayi yabar wajan jim kadan sai gashi yasa kaya, tashi tayi tazo inda yake tana kuka ta rungumeshi tana fadin i luv u, dan janta yayi ya mata peck a goshi sannan yace ta daina kuka, sakinta yayi tare da fara tafiya yace zai fita zuwa wajan dad dinshi, yana fadin haka ya fita kasa tayi tana ta kuka sosai kaman ranta zai fita, tayi wajan awa daya tana zaune a wajan tana kuka sannan ta tashi dakyar ta nufi gidanta har wani jiri2 take ji, koda ta shiga gida a falo ta kwanta tana kuka gwanin ban tausayi tare da surutai kala2 dama mum ta fadamin babu abunda zaiyi dani mai yasa na kasa yarda da mum mai yasa yaki yarda dani kuka ta kuma saki tana fadin mai yasa mai yasa, tana kuka.
Chapter 9 · 0% Book details