← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 45

Sashe 11

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jawaheer tana kwance akan kujeran falo tana ta rusgan kuka, lokaci daya zazzabi ya kamata mai zafi, wanda yasa duk wani gaba dake jikinta ya mutu, ga kanta dake faman sara mata wanda kukan da tasha ya haddasa mata ciwan kai din da zazzabi, dakyar ta tashi tayi alwala tayi sallah a zaune dan bata ji zata iyayi a tsaye, kuka take tana roqan Allah akan ya zaba mata mafi alkhairi a rayuwanta, harta gama ta kwanta wajan da tayi sallah din, gaba daya taji zaman garin ya isheta burinta ta ganta a nigeria domin kuwa tasan M samir bazai taba sonta ba har abada, dakyar taja jikinta ta dauko wayanta dake ta faman ruri tun dazu, sunan mum ta gani dan haka ta dauka da sauri tare da fadin mum..... Sai kuma ta saki kuka hankali tashe mum take tambayanta maiya faru jawaheer lafiya kuwa? Cikin kuka tace mum magananki gskya ne, tabbas gskyan hausawa ne da suke fadin duk abunda babba ya hango yaro bazai taba hangosa ba, mum cikin damuwa tace jawaheer dan Allah ki fadamin maike faruwa, wani abu aka miki? Tace mum inaso a fara maganan biki na kaman yanda kike so da duk mijin da kuka ga ya muku, mum tace jawaheer dagaske kike? M samir fa? Kina nufin kin hakura dashi? Duk lokaci daya mum ta jero mata tambayoyi wanda yasa jawaheer din wani sabon kuka, cikin kuka taba mum labarin duk abunda ya faru tare da fadin mum jibi zan dawo gida, ki fadama dad yama PA din ambassador magana, mum tace shikenan jawaheer zan fada mishi kiyi hakuri ki cire komai a ranki insha Allah komai zai wuce, tace mum bana tunanin zan cire komai domin son M samir a jini na yake na amince da zanyi aure ne saboda alkawarin da nayi mum inaso ki sani wlh duk wanda na aura gangar jikina ne kawai a tare dashi amma zuciyata tana tare da m samir mum ki tayani da addu'a kawai Allah ya bani hakuri da dangana amma ina cikin wani hali mum tana fadin haka ta kashe wayan tare da sakin kuka mai karfi, a yanzu jawaheer bata bukatan komai face ta ganta a kasarta nigeria domin ta cire tsammanin m samir zai sota, sai dai koba komai zatai alfahari da ganinshi da tayi tare da kissing dinta da yayi duk da tasan ba abu bane mai kyau tunda ba mijinta bane, sai dai a yanda take jinshi koda jikinta ya nuna yana bukata bata tunanin zata hanashi dan tana mai mahaukacin so, wanda bata ganin kowa sai shi, sai dai kash shi ta gefenshi ba haka bane irin yanda ya nuna baya sonta yasa take ganin kaman zata iya rayuwa da wani wanda ita da kanta tasan karya ne, m samir kadai shine burinta shine namiji daya da zata samu tayi farin ciki a rayuwa koda kuwa zai dinga dukanta ne kullum, lokaci daya ta tashi da sauri duk da bata jin karfi a jikinta tafiya take tana tangal tangal kaman zata fadi kofar gidanta ta nufa ta bude ido ta kurama gidan m samir din wanda hakan ya nuna mata alaman ya dawo yana gida, tunda taga security dinshi, kirjinta taji yana buga mata da karfi, lokaci daya ta fara tafiya domin zuwa gidan har ta kusa shiga ta tsaya, lokaci daya kuma ta juya zuwa gidanta da sauri dan bata jin zata iya zuwa gareshi yanzu, amma koda ta shiga gida kasa sukuni tayi wanda yasa dole ta kara nufa gidan duk da kirjinta na buga mata dan bata san mai zata tarar ba yanzu, amma haka ta daure ta shiga cikin falon gidan a kwance ta ganshi akan kujeran falon kallo daya zakai mishi ka gane yana cikin wani hali dake bukatar taimako, da sauri ta nufeshi tare da fadin m samir, nufanshi tayi tare da fadin baka da lfya ne? Idonshi ya bude daya kada yayi ja ya sauka a kan fuskanta, murmushi ya sakar mata tare da kokarin tashi amma ya kasa, dan haka ta fara kokarin dagashi amma ta kasa, murmushi ya kuma saki tare da fadin na miki nauyi koh? Dan shuru tayi sannan tace baka da lafiya jikinka da zafi u need to see a doctor, ido ya kura mata yace jawaheer kema jikinki zafi kina bukatan ganin dr tashi yayi dakyar tare da janyota jikinshi yace maike damunki? Kirjinta ya fara bugawa da karfi wanda hakan yasa ta kasa magana domin gaba daya tunda ya janyota jikinshi wani irin shock ya kamata tare da shiga cikin wani irin yanayi bakinta sai rawa yake alaman tana son cewa wani abu amma ta kasa, ido ya kura mata yana kallonta lokaci daya ya furta she iz pretty.

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 16

Lokaci daya kuma ya furta nasara akan me? Bata bashi amsa ba dan kuka takeyi sosai ganin bata da niyan bashi amsa yasa ya tashi ya dawo kusa da ita zama yayi kusa da ita tare dasa hannunshi yana share mata hawayen dake zuba a fuskanta, yace jawaheer kibar wannan kukan koma miye insha Allah zaki samu ki dage da addu'a kinji kai ta daga alaman toh, sannan ta tashi tare da fadin sai anjima, bai tankata ba har takai bakin kofa ya kira sunanta tare da fadin inane gidanki? Tace can, dariya yayi tare da fadin can ina? Tace kazo muje saika gani, tashi yayi yana jan kafa dan har yanzu bawai ya warke bane tana gaba yana biye da ita a baya komai nata yana burgeshi kyanta nutsuwanta, maganan ta, tafiyanta kai komai nata ya mishi sai dai baya jin sonta a ranshi amma ya dauketa a matsayin kanwarshi domin so daya ne ya kuma bama sonia wacce bai san inda take ba a halin yanzu dan tunda ta tafi basuyi waya ba duk da yama dad dinshi alkawarin rabuwa da sonia amma baya jin zai rabu da ita dan itace rayuwanshi,.... Maganan jawaheer ne ya katseshi da take fadin shigo mana, sai a sannan ya gane sun zo gidan, shiga yayi da sallama, tace ya zauna a falo, bayan ya zauna ne ta nufi kitchen dan ta hada mishi coffee bata dauki wani lokaci ba ta kawo mai amsa yayi ya fara sha, sannan ya dago kai suka hada ido murmushi ya sakar mata yayin da ita kuma tayi saurin kawar da fuska dan taji kunyar kamata da yayi tana kallonshi, jinshi tayi yana fadin ina son idonki yana min kyau, bata iya cewa komai ba sai murmushi kawai da tayi, shima bai kara magana ba harya gama shan coffee din wayanta ne yayi kara dan haka ta tashi ta dauko taga ozil ne , dauka tayi da fadin kabir nayi fushi wlh sai yau? Yace kiyi hakuri m samir nasan nayi laifi tace uhm ni bazan hakura ba gaskiya, ban san mai yace mata ba naga ta saki dariya tare da fadin zan baku mamaki ku dukanku, nan dai sukai ta fira cikin harshen hausa har sukai sallama,
Chapter 11 · 0% Book details