← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 45

Sashe 29

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari jawaheer nada lecture karfe 8, dan haka da wuri ta shirya duk da ranta a jagule yake, dan tasan m samir yana fushi da ita, gashi yau zai tafi, ji tayi ba zata iya tafiya ba har sai ta ganshi, dakinshi ta nufa taga baya nan, fita tayi ta nufi falo taga mum na gyara kayan abinci akan dinning, tace morning mum, mum tace har kin fito? Tace eh mum gashi har na kusa makara, na tafi sai na dawo, mum tace ok samir yace in fada miki ya tafi, sannan ga sako ya bayar a baki, dam taji kirjinta ya buga wato tafiya yayi shine bai mata sallama ba......

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 41-42

Mum ta dauko wani karamin bag ta bata, amsa tayi ta koma dakinta ta ajiye tare da fashewa da kuka, wato haka za'a fara kenan, kallon jakan tayi ta bude taga kudi masu uban yawa kuma duk dallar, sai wata takarda data gani a ciki, budewa tayi taga anyi rubutu kaman haka...... *ga kudi nan kisai duk abunda kike bukata kin san ban san ya al'adunku suke ba, ki fara siyayyan abunda kike bukata inna dawo sai mu karasa wasu abubuwan, sannan inaso ki sani ni bana daya daka cikin maza marasa kishi dan haka kisan wa zaki aura ina da kishin kaina dan haka dole inyi kishin iyalina, idan kika kara kula wani ban yafe ba sannan idan na sami labari zaki hadu da fishina bye* baki ta sake tana mamaki lokaci daya kuma tayi dan murmushin takaici, tare da tunanin yanda rayuwan aurensu zai kasance ita dashi, bata taba tunanin zata aura mijin da zai bude baki yace baya sonta ba har kuma ta yarda da auran, wani siririn hawaye ne ya silalo mata a fuska jin karan wayanta yasa tayi saurin goge hawayen zarah ta gani, dan haka ta dauka da sauri ban san mai zarah tace mata ba naji tace gani nan zuwa, har takai kofa ta tsaya tare da waigowa komawa tayi ta dauki jakar ta fita, a falo ta kara ganin mum tace yauwa mum gashi kudi ne a ciki yace in fara siyayya kafin ya dawo, murmushi mum tayi tare da fadin ok in kin dawo mayi magana tace ok tare da fita.

Makaranta ta nufa direct bayan tayi parking ta kalli agogon dake manne a hannunta tare da fadin 8:03 Allah yasa bai shiga ba, jakarta ta dauka ta fita ta nufi department dinsu a tare da lecturer din suka shiga, kallonta yayi yace u r lucky 2day, murmushi kawai tayi ta nemi waje ta zauna, inda ya fara koyar dasu harya gama ya musu text, sannan ya kalli jawaheer yace sameni office dina yanzu, yana fadin haka ya fita, kallonshi tayi ta banga mai harara ta baya tare da fadin ko uban me zan mishi oho, zarah tazo kusa da ita tare da fadin sai ki tashi kije, hararan zarah tayi tare da fadin muje ki rakani, zarah tace wa? Ni din? Tab ai in kin ganni a lahira kaini akayi, ke yace kije dan haka babu inda zani, tashi tayi ta fita zarah tayi dariya tare da bin bayanta har kofar office dinshi zarah ta rakata amma taki yarda ta shiga, nocking jawaheer tayi taji shuru karayi tayi sannan akace come in, budewa tayi ta shiga, akan kujera ta sameshi yana duba wasu takardu, ganin ta shigo yasa ya saki murmushi, tare da fadin jawaheer right? Kai ta daga alaman eh, ya nuna mata kujera tare da fadin zauna mana, zama tayi fuskanta tamke, yace jawaheer mai yasa baki kira niba? Tace na manta ne, yace ok so yanzu ni sai ki bani number dinki, ko kuma ki kirani, tace zan kira inna koma gida, yace ok muga wayanki, kaman karta bashi amma babu yanda ta iya ta miqa mai, kiran layinshi yayi sannan ya mika mata wayan tare da fadin baki saving din number dina bama, dan murmushi tayi yace bari in gabatar miki da kaina sunana yusuf, ni dan garin kaduna ne wato dan zaria, ina da mata daya da yara biyu, jawaheer tunda na ganki naji Allah yasa min sonki sannan ni bada wasa nake ba da aure nake sonki, shuru tayi tana kallonshi, tare da takaicin kalaman da yake fada mata, amma ya dan burgeta dan da farko tayi zaton kalan lecturer din nanne masu bata yan mata, amma sai taji sabanin haka, sannan yusuf ba laifi yana da kyau sannan mijin nu nawa ne a ko ina, amma ita bata ganin kowa sai samir dinta kawai.... Katseta yayi da fadin jawaheer ya naji kinyi shuru, magana za tayi ta kasa ganin haka yasa yace kije zan kiraki zan baki lokaci kiyi tunani akai, da sauri ta tashi ta fita, wajan zarah ta nufa, zarah na ganinta ta tashi tare da fadin ya akayi? Tace hmmm muje kiji, suna tafiya tana bama zarah labarin abunda ya faru, zarah tace kai amma ni kam jawaheer mai zai hana ki yarda dan naga....... Tace dakata taya zan yarda bayan nanda wata biyu biki na, ido zarah ta bude tare da fadin ke dawa? Jawaheer tace m samir, shuru zarah tayi tana nanata sunan tare da fadin ni kam ina jin sunan, yauwa na tuna wani dan kwallon kafa ne mai irin sunan, jawaheer tace to ni dan kwallon zan aura, zarah kwashewa tayi da dariya tare da nuna jawaheer da hannu tace wannan wasan naki daban dariya yake, jawaheer tace kece kike da ban dariya amma banda lokacin miki bayani in lokaci yayi zaki gani, zarah dai dariya take tayi alama jawaheer wasa take mata, ganin tana kokarin mai data mahaukaciya ko kuma makaryaciya yasa jawaheer tace ni kinga tafiya ta, tayi gaba abunda zarah saboda dariya ma kasa binta tayi, ita kam jawaheer tayi gaba abunta.

Jawaheer koda taje gida a wajan bukka taga mum dinta da dad suna fira ga kayan abinci nan a wajan kala kala, nufansu tayi cikin fara'a tare da fadin dad mum sannunku da hutawa, amsawa sukayi su duka da fadin yauwa, zama tayi tare da fadin mum ina khalil ne wai? Tace ya fita shida ozil, tace lah ya dawo ne? Mum tace eh ya dawo dazu, dad yace jawaheer kinci abinci kuwa? Tace a'a yace haba bakinki ya nuna hakan, mum ta fara zuba mata tare da fadin babu yanda banyi da itaba amma taki ci da safe, mutum yaita zama da yunwa in kika jajibo ma kanki ulcer aike kika sani, ita dai jawaheer shuru tayi tare da amsan abincin ta fara ci, taci sosai sannan ta ajiye, bayan ta kammala mum tace jawaheer nasa an canzo kudin da samir ya baki duka kudin million 200 ne, zamu tafi dubai muyi siyayya a can na kayan akwati kafin ya dawo muji yanda yake son a tsara dan kin san mutum celebrity bazai rasa yanda yake son bikinshi ya kasance ba, cikin jin kunya tace toh mum, dad yace amma kudi ai yayi yawa, mum tace baiyi wani yawa ba,yar tawa ai mai tsada ce, dariya dad yayi yace nima haka dan nawa, ita dai jawaheer tashi tayi dan wani irin kunyan mum taji tanayi yanzu, suna ganin ta tashi suka sa dariya.
Chapter 29 · 0% Book details