← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 45

Sashe 3

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda jawaheer ta shiga cikin falon gidan taga mum dinta da dad da gudu ta fada jikin dad din nata tana kuka cikin damuwa iyayen nata suke tambayanta ko lfya mai aka mata? Cikin kuka tace dad anjima M samir ciwo mum tsaki tayi tare da kawar dakai daka kallonsu da takeyi dan tasha ko wani abu aka mata da farko ashe shirmenta ne data saba dan haka mum take daukan duk wani abu nata indai akan M samir ne, dad ya kalli mum yace haba bilkisu mai yasa kike irin haka kina ganin yarinya ta shigo cikin wannan halin sai ki dinga sakar mata tsaki ,tace toh mai zance? Indai akan wannan shirmen ne na jawaheer bani da abun cewa sai dai tsakin yarinya kullum bata da aiki sai fadin M samir M samir haba dan Allah ,jawaheer jin haka yasa ta kara fashewa da kuka dad yace yakuri J ki kyale mum dinki sannan M samir zai tashi insha Allah cikin shagwaba tace dad dagaske? Kai ya daga ya kuma cewa insha Allah, hawayen fuskanta ta goge tare da fadin dad dan Allah yaushe zaka hadani dashi? Murmushi yayi tare da fadin Ambassador dinmu na kasar Spain bashi da lafiya yana asibiti munyi magana idan ya warke zai fadamin sai ya hadaku dariya ta saki tare da fadin kai dad ina sonka sosai dad idan ya ganni zaiji yana sona kuwa? Mum tsaki tayi ta tashi tabar wajan dan takaici shiko dad ci gaba yayi da sauraran yar tashi yace sosai kuwa ai nasan idan ya ganki saiya rude sosai dan babu wanda zaiga my daughter yace bata mai kyau ba ,jawaheer cikin jin dadi tace dad kaga idan muka hadu ina gama skul sai ayi bikin mu koh?dariya dad yayi yace duk yanda kika tsara hakan za'ayi tashi dad yayi tare da fadin bari in fita ina da meeting karfe 6 kice ma mum dinki na fita tace ok dad take care yace i will my dear fita yayi ita kuma ta nufi dakin mum din nata ,a zaune taga mum tayi tagumi jawaheer tace mum lfya kuwa? Mum ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yauwa zo nan ki zauna bayan jawaheer ta zauna kusa da mum take cewa dad yace in fada miki ya fita,kai mum ta daga alaman toh, sannan ta kalli yar tata tace jawaheer wai yaushe zaki gane kin girma ne? Yaushe zaki farka daka wannan mahaukacin mafarkin da kikeyi ne? Shifa wannan mutumin da kike hauka a kanshi bai sanki ba yau ki duba shekarunki ishirin a duniya amma baki da saurayi tsayayye duk masu sonki in sunzo sai ki koresu yaushe zaki fahimci cewa shi wanda kike hauka a kansa bazai iya auranki ba..... Kukan jawaheer din ne yasa mum yin shiru tana kallonta cikin kuka tace mum ba mafarki nakeyi ba Mum kema kin san M samir gaskiya ne yana cikin duniyar mu kinga mum shiba mafarki bane mum bana jin zan iya auran ko wani namiji inba M samir ba wlh mum shi nake so inama zan iya nunama duniya zuciya ta taga irin son da nake mishi mum ko kin san idan ban sami M samir ba zaku iya rasani mum wlh ina cikin hayyacina tsantsar sonshi ne yasa nake duk wannan abun mum ki fahimce ni..... Salati mum ta saki tare da fadin nashiga uku wlh jawaheer kin samu tabin kwakwalwa..... Tace mum lafiya na qalau babu abunda ya sami kwakwalwa na ,mum cikin tausayi tace inko babu abunda ya sami kwakwalwanki toh wlh kinyi gamo ne cikin biyun nan dole akwai daya ban taba ganin irin wannan masifan ba dan Allah jawaheer ki cire wannan abun indai kina so in tabbatar da kina cikin hankalinki, kuka jawaheer ta kuma saki tare da fadin mum nayi kokarin inyi hakan amma na kasa mum idan ban auri M samir ba mum bana tunanin iya ci gaba da rayuwa na mari mum ta sakar mata ji kake tas.......

*comment dinku yana min kadan sannan plz sharhi nake bukata ba thx ba dan yana da matukar amfani*

*maryam obam*
[02/01, 14:23] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

Page 4

Rike wajan tayi tana hawaye mum tace jawaheer ki farka daka wannan mafarkin da bazai taba zama gskya ba, keba yarinya bace ki daina yaudaran kanki kuka mum ta saki itama ta fara magana cikin sanyin murya tare da sigar rarrashi tace jawaheer ke daya ce y'ata mace ina sonki fiye da yanda kike tunani bana son duk wani abu da zai saki cikin damuwa koya taba lafiyanki nafi kowa son inga yau kin sami abunda kike so amma wannan abunda kike so bamai yihuwa bane dan Allah jawaheer ki cire wannan kwallon a ranki da shi dan kwallon da kike so ki nutsu ki fitar da miji cikin manemanki kiyi aure idan kikayi aure hankalinki zai kwanta zaki manta da wani M samir, kai jawaheer ta fara girgizawa tare da fadin kiyi hakuri mum inama zan iya hakan da nayi farin ciki Allah ya sakamin son M samir bana iya ganin zan iya rayuwa da wani namiji inba shiba mum ki fahimce ni ban taba kin duk wani abu da kika fadamin ba wannan yafi karfina ne son M samir a jini na yake wlh mum Allah shine daya koh toh idan ban sami M samir ba zan iya mutuwa tana fadin haka ta tashi tabar dakin mum din nata da gudu tana kuka itama mum din kuka ta saki tare da fadin wlh jawaheer tayi gamo dole insa ayi mata addu'a na shiga uku wannan wani irin bala'i ne ita kuma irin tata jarabawan kenan son bature wanda suke kyamar yan africa suke kiran yan africa animals mum daukan wayanta tayi ta kira maman kabir hjy hauwa, bayan ta dauka suka gaisa hjy hauwa tace bilkisu lfya kuwa naji muryanki kaman kina cikin damuwa? Tace hmmm hauwa kedai bari kawai wlh jawaheer tana son sani cikin damuwa maganan nan bata waya bace kina gida yanzu in shigo? Hjy hauwa tace ina nan ki bari bari ni inzo mum tace toh sai kin shigo ina dakina in kinzo hjy hauwa ta amsa da toh sannan suka kashe wayan.

Basu dade dayin sallama ba hjy hauwa ta shigo gidan, da sallama ta shigo dakin mum, mum ta nuna mata waje tare da fadin bismillah ga waje nan, bayan hjy hauwa ta zauna mum tace hmmm hauwa ina cikin damuwa sosai, hauwa tace mai yake faruwa bilkisu kimin bayani nan mum ta fara bama hjy hauwa labari irin abubuwan da jawaheer takeyi itama hjy hauwa salati tayi tare da fadin ikon Allah wannan wani irin sabon al'amari ne haka? Mum tace wlh kema kya fada yarinya kaman wacce tayi gamo da aljanu, hjy hauwa tace gskya nima ina tunanin haka domin inba aljanu ba babu abunda zaisa ta dinga tunanin haka Allah sarki jawaheer ,mum tace toni yanzu miye mafita? Hjy hauwa tace mafita daya shine mu kaita wajan malami ya mata ruqiya kin san akwai *BAQIN ALJANI* *sunan novel dina* da basa bayyana sai suyi tasa mutum yaita abu kaman hauka ko su hana mutum aure duk yanda akayi jawaheer tana tare dasu inko ba haka ba ai ba zata kamu da son wanda bata taba gani ba bata da tabbacin ma zai aureta ,mum tace oh ni bilkisu na shiga uku ,wlh da walaki dan jawaheer da ba haka take ba tama tsani kwallon kafa amma lokaci daya yarinya ta birkice, yanzu yaushe zamu wajan malamin? Hjy hauwa tace bari in kirashi inji yaushe yake nan, doka mai kira tayi ringing uku ya dauka bayan sun gaisa tace mlm dan Allah yaushe kake nan akwai yarinyar kawata da take da matsalan jinnu inaso mu kawota koh Allah zai sa a dace, ban san mai yace mata ba naji tace toh Allah ya kaimu sannan sukai sallama, kallon mum tayi tace yace gobe da karfe hudu mu sameshi a islamiya sannan tare da jawaheer din zamu ,mum tace Allah ya kaimu, hjy hauwa tace ameen wannan abu sai an hada da addu'a, mum tace kedai bari wlh idan kika shiga dakinta gaba daya hotan dan kwallon kafa dinne duk ta manne shi dashi sai kace abun hauka harta cup din da take amfani dashi na kwallon kafa ne duk an manna hotan yaron a jiki rannan tiles din dakinta naji tana fadin zata sa a saka mata mai hotanshi wai a cire mata na dakinta dakyar na hanata sai carpet tasa ta rufe tiles din carpet dinma mai hotan yaron, hjy hauwa tace ikon Allah jawaheer ita tata jarabawan kenan Allah sarki yarinya mai nutsuwa amma lokaci daya ta canza kiyi hKuri insha Allah gobe idan mukaje wajan mlm komai zai zo da sauki insha Allah, tashi hjy hauwa tayi tare da fadin bari in koma gida dare yayi mum tace toh ngd sai goben fita hjy hauwa tayi
Chapter 3 · 0% Book details