Sashe 13
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washe gari da safe tunda jawaheer tayi sallah asuba tayi wanka, ta koma bacci bata farka ba sai wajan karfe goma tana tashi ta kara komawa tayi wanka, tasa wata doguwar riga tare da daura karamin gyalen rigan, kitchen ta nufa ta hada tea dan gidan babu masu aiki tunda su mum suka tafi suma suka wuce, tana cikin shan tea din taji nocking tashi tayi ta nufi kofar tare da tunanin ko waye, tana bude kofar taga mutum a tsaye cikin riga da wando yayi mugun kyau ya hade hannunshi biyu yana kallonta tare da sakar mata murmushi ganin irin kallon da take mai yasa yazo kusa da ita tare da mata peck a goshi yace morning sis, firgit tayi ta fara kame kamen mai zata ce, ganin haka yasa ya kamo hannunta tare da shiga cikin gidan yace nazo ki rakani wajan dad dina yana son ganinki, ido ta zaro tare da nuna kanta alaman ni zai gani, kai ya daga mata tare da fadin yes ke zai gani, matsowa tayi kusa dashi tare da fadin Allah yasa ba laifi nayi ba? Yanda tayi maganan cikin sanyin murya ya bashi dariya hancinta yaja tare da fadin bakiyi komai ba kawai yana son ganinki ne, ajiyan zuciya tayi tare da fadin yaushe zamu? Yace yanzu, tace ok ina zuwa dakinta ta shiga ta canza kaya tasa jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan tayi kyau sosai sak balarabiya, ga kamshi dake tashi a jikinta falon ta nufa lokacin data fito ido ya kura mata yana murmushi ganin irin kallon da yake mata yasa ta danji kunya, kaman ya lura da hakan yace sis kinyi kyau tashi yayi ya janyota tare da daukansu hoto yana fadin bani da pics dinki dama, ya daukesu da yawa sannan yace ta bashi wayanta, mika mishi tayi yayi dialing no dinshi cikin nata, sannan ya kalleta yace bani no dinki na kasarku, murmushi tayi tare da fada mishi ya rubuta, sannan yace suje, motarshi suka shiga wacce cikin motan kaman daki seat din motar ma kanshi abun kallo ne, ga tv har biyu a manne a motan dayan camera ne amma sai yayi kaman tv duk wani abu da akeyi a waje yana kallo ta ciki, jawaheer ta kara tsorata dashi domin tasan lallai m samir ba karamin mutum bane lallai haduwansu hadin Allah ne, Allah ya amshi addu'anta dole ace ganinshi tashin hankali ne amma sai gashi Allah yasa ta ganshi cikin sauki, wani hawaye ne ya gangaro mata, jin hannunshi tayi akan fuskanta yana goge mata, lokaci daya ta dago kai suka hada ido, sunyi wajan minti daya suna kallon juna, kowa da abunda yake sawa a ranshi, shine yayi karfin halin kawar da idonshi tare da janyota jikinshi yana shafa mata bayanta yana fadin jawaheer mai yake damunki? Cikin wata irin murya tace ina farin ciki da Allah ya hadani dakai cikin sauki, lallai haduwa na dakai akwai wani boyayy...... Shuru tayi domin taji abun ya mata nauyi, yace inaji akwai me? Tace babu komai murmushi kawai yayi tsayawan motar ne yasa ta gane sun zo inda zasu, fita sukayi m samir ya kamo hannunta zasu shiga tare tayi sauri ta janye hannunta kallonta yayi ba tare da yace mata komai ba, ganin irin kallon da yayi mata alaman tambaya yasa ta fara fadin kar dad yaga ka riqeni zaice banda kunya, murmushi yayi sai yaji ta burgeshi sosai, haka suka shiga cikin gidan koda suka shiga ya nuna mata waje ta zauna gina ta fito suka gaisa ta kawo mata coffee jim kadan sai ga dad da m samir, dad ido ya kura mata ganin suna isowa yasa ta tashi ta tsaya a tsaye har dad ya karaso dad yace ta zauna mana zama tayi a dan takure tare da gaida dad din ya amsa cikin sakin fuska tare dayi mata tambayoyi akan iyayenta tana bashi amsa dad ya yaba da tarbiyanta sosai kuma yaji ta burgeshi dan haka ya saki jiki da ita yana ta janta da fira sosai, suna cikin haka wayanta yayi kara dubawa tayi taga mum ce dauka tayi bayan ta gaida mum cikin harshen hausa tace mum zan kiraki tare da kashe wayan, tana gamawa m samir yace ta tashi su tafi, wata leda ta ciro cikin jakarta ta ajiye a gaban dad tare da fadin dad kayi hakuri babu yawa, dad rasa bakin magana yayi lallai yarinyar nan tana da kirki tarbiya ladabi sannan al'adunta abun burgewa ne, dad yana ta mata godiya, har mota dad ya rakasu tare da fadin ta kulan mishi da yaro sannan in komai yayi dai2 shima zai zo nigeria haka suka tafi cikin jin dadi, suna mota m samir ya kira sunanta jawaheer ta dago suka hada ido tayi saurin kawar da ido, kara kiran sunanta yayi alama ta waigo ta kalleshi, kin waigowa tayi, ganin haka yasa ya janyota jikinshi suna hada ido ta rufe idanta wanda hakan ya bashi daman kallanta dakyau tare da aiyana abubuwa da dama a ranshi......
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 18
Gaba daya ya gama karema jikinta kallo yayin da duk wani sassa na jikinshi ya mutu wani irin yanayi ya shiga mai wuyan musaltuwa jawaheer tana da kyau na bugawa a jarida tana tarbiya wacce za'a so ace mutum ya sameta a matsayin mata sai dai kash baya jin sonta, idanshi ne ya sauka akan lebanta wanda kallo kawai zakai mata ka gane yana da laushi ido shima ya lumshe tunawa da ranan da yayi kissing dinta, bai taba shiga cikin wani irin hali mara misaltuwa ba kaman ranan duk da ba'a hayyacinta ya mata ba, inda tana cikin hayyacinta kuma da yardanta hakan ya faru da ya zaiji?.... Karan wayan jawaheer dinne yasa ta bude ido wanda shima yayi dai2 da bude nashi caraf suka kara hada ido wanda wannan karan sun kasa daukewa daka kallon junansu har wayan ya tsinke, shidai yasan baya son jawaheer sonia yake so amma yana jin wani abu a tare da jawaheer wanda bayaji akan sonia..... Karan kiran nata ne ya kuma katsesu wannan karan dauka tayi taga mum dinta, tace mum ...... Mum tace inata jira ki kirani kinki kira ya maganan dawowan naki gobe? Kallon m samir tayi taga yana danna waya, tace mum gobe zan dawo amma bana tunanin abuja zan sauka,mum tace kaman ya ina zaki? Tace yola zani mum tace what?... Kina da hankali kuwa uban me zakiyi a yola jawaheer wlh zanyi mugun saba miki, ki tabbata gobe kin sauka a abuja inba hakaba zaki hadu da fushina wlh, tace mum pl...... Kit mum ta kashe wayan jawaheer kallon wayan ta tsayayi tana mamaki toh miye abun zafi dan tace zata yola, bama an barta tayi wata daya bane a nan ai bata ma kai wata dayan ba, jin hannun m samir tayi a kanta yana fadin what r u thinking sis? Murmushi ta saki tare da fadin babu komai, a hankali ya furta nagode da kyautarki da kika ba dad dina i really appreciate it, bata fuska tayi tace nima fa dad dina ne, yaji dadin magananta, domin yana son dad dinshi duk wanda yake son dad dinshi toh shima yana son shi, a haka har suka karasa gida gidanshi ya shiga itama ta shiga nata.
Yanzu karfe 8 na dare a kasar spain amma zukata biyu sun kasa sukuni domin kuwa ko wanne yana burin ganin dan uwansa, jawaheer tana mugun san ganin m samir cikin daren nan, haka shima ta gefenshi babu wacce yake burin gani sai ita amma shi a nashi ganin ya danganta hakan ne da daukinshi na zuwa nigeria kuma itace zata kaishi, tashi yayi yasa riga ya fita, tana kwance tana tunanin m samir taji ana mata nocking tashi tayi taga ita sai rigan bacci dai2 gwiwanta ta nufi kofa, tana budewa taga flower a wajan amma babu kowa, dubawa farayi ko zata ga mutum, amma bataga kowa ba dan haka ta dauki flower din tayi shuru lokaci daya kuma ta shiga ciki dashi, dan karamin kwalin data gani ta dauka ta fara karantawa kaman haka..... *Hey am hare missing you u r d best sister in d world* ido ta lumshe domin yanzu tasan waya ajiye mata wani irin farin ciki taji yana shiganta, wayanta taji yana kara da sauri ta nufi bedroom dinta ganin number din da yake kiranta yasa ta dauka da sauri amma saita tsinci kanta da kasa magana, muryanshi taji yana fadin kinyi kyau cikin night gown kiyi bacci da wuri kin san gobe zamu tafi, tace ok yanzu zanyi bada dadewa ba, murmushi yayi tare da fadin ok sis good night tare da kashe wayan, wani irin murmushin murna tayi tare da rungume wayar a jikinta sai kace m samir dinne a gabanta ta rungume haka, ranan bacci tayi cikin nishadi haka shima ta gefenshi.