Sashe 28
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 39-40
Da sauri ta dago kai ta kalle shi, murmushi yayi tare da fadin yes jawaheer u r my sister bani da wata yar uwa mace sai ke, so kinga dole in soki, ajiye ajiyan zuciya tayi tare da lumshe ido dan ba haja tai zatan jiba, tashi tayi tare da fadin saida safe, shima tashin yayi yace sis bacci yanzu miye time? Tace na gaji ne sosai, yace ok good night, fita tayi ya bita da ido harta rufe mai kofar sannan ya lumshe ido tare da buga hannunshi akan dayan hannun yace damn, shima kwanciyan yayi tare da tunanin jawaheer din tare da alkawarin neman mata mum dinta a duk inda take a fadin kasar nan.
Koda ta shiga daki kuka ta fashe dashi tare da fadin lallai na yarda m samir bazai taba sona ba, Allah ka jarabceni da son wanda baya sona amma ina roqanka kasa in cinye wannan jarabawan, shuru tayi tare da fadin lallai wannan shine maganin matsalata, wannan ne karo na farko data taba tunanin tayi aure ko zata cire m samir a ranta, lallai shine mafita amma komai zanyi sai naga mum dina zanyi aure inyi nesa dashi gaba daya da wannan tunanin bacci yayi gaba da ita.
Washe gari m samir tun karfe 7 ya fita shida khalil da security dinshi, direct wajan hukumar shiga da fice suka nufa, inda suka basu international passport din mum din jawaheer, tare da kudi masu yawa akan su nemo bayanai akanta, ce musu sukayi su dawo nan da sati daya, hakan akayi suka tafi bayan yawan mutanen da suke ta cincirindon son daukan hoto da samir dakyar dai suka shiga mota suka bar wajan akan nanda sati daya zasu dawo ko kuma su zasu nemeshi sun daiyi exchanging number, yawo suka dinga yi ranan.
Jawaheer kam tunda ta tashi tayi wanka, tasa wata atamfa mai ruwan ja da ash yayi kyau atamfar anyi dinkin riga da skirt saiya fito mata da surarta das a jikin kayan tayi bala'in kyau duk da ba makeup a fuskanta, wani karamin gyale ta yafa ta fito ta sami mum ita daya a falo, tace ina kwana mum? Amsawa mum tayi cikin sakin fuska tare da tambayanta ya gajiyan hanya, tace alhmdlh mum hanya babu dadi, mum tace ina zaki naga kaman fita za kiyi, tace eh mum yau zan shiga skul mun koma tun last week, mum tace kai jawaheer kina wasa da karatu tun last week kuka koma shine kikai shuru baki fara zuwa ba, yanzu kin san lecture nawa kikai missing? Tace mum karki damu attendance ne matsalan kuma nasa ana daukan min, mum tace toh shikenan dan Allah ki daina wasa kije kici wani abu kafin ki tafi, tace mum zanci a skul, babu yanda mum batayi ba amma taki ci tace bata jin yunwa, fita tayi ta wuce daya daka cikin motar gidan ta shiga mai kiran prado, ita da kanta take tukin har cikin makarantar,faka motarta tayi sannan ta nufi department dinsu, tun daka nesa ta hango yan class din nasu daka gani akwai lecturer a ciki domin duk sun bada hankalinsu wajan kallon waje daya, tana isa kam taga lecturer ne a ciki, dan haka ta shiga cikin sanyin jiki, kallonta lecturer din yayi kaman zaiyi mata magana sai kuma ya fasa, ji yayi tace mishi morning amsawa yayi sannan ta nemi waje ta zauna, kowa yayi mamakin dabai koreta ba dan yau kwananshi uku da fara basu darasi sannan duk wanda yazo idan ya shiga baya bari ya zauna, bayan jawaheer ta zauna ya kuma kallonta tare da sakin murmushin dashi kanshi bai san yayi ba, ganin itama ta mayar mai da martani yasa ya gane abun da yayi, da yake ya iya duniyanci saiya basar yaci gaba da lecture har lokacinsa yayi, sannan ya kalli jawaheer yace daka yau karki kara shigo min class indai na rigaki shigowa, kai ta daga alaman naji, sannan ya fita, tsaki tayi tare da dauko wayanta tana dan dannawa, kiran dr ne ya shigo kaman ba zata dauka ba, komai ta tuna kuma ta dauka tare da fadin hello, ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin jawaheer wai nayi laifi ne aka daina daukan waya ta? Uhm kawai tace yaci gaba da fadin jawaheer naje adda tace min wai kin koma jiya, shine ko sallama babu, tace kayi hakuri tafiyan ne yazo a bazata, yace bakomai da fatan anga sako na, dan shuru tayi kafin tace uhm, murmushi yayi sannan yace ina fatan za'a bani dama? Tace Allah ya taimaka ya shige mana gaba, wani irin dadi yaji tare da fadin kenan an bani dama, kai yau ina farin ciki Allah ya dai daita mu, bata ce komai ba sai murmushi da tayi, wani lecturer ne ya shigo tace ina zuwa zamu fara lecture yace ok tare da kashe wayan, sai lecture ake musu amma ita sam bata san mai ake fada ba, domin tayi nisa cikin duniyar tunani ba komai take tunani ba sai na amince ma dr akan yaci gaba da nemanta har Allah yasa su fahimci juna tayi hakan ne da zuciya daya domin tana da burin ta sami miji tayi aure dan ta cire m samir a ranta duk da tun jiya take ta kokarin tusa ma kanta kin shi amma hakan ya faskara, lallai koda banga mum dina ba indai muka fahimci juna dole inyi aure in huta, ji tayi ana mata magana, wata yarinya ce kana ganinta kasan suma suna da arziki, jawaheer firgit tayi taga lecturer din ya fita tace kai ashe har an gama, yarinyar tayi murmushi tare da fadin sunana zarah, yau na fara zuwa lecture saboda nayi ciwo sai nayi differing da yanzu ina 3lv amma yanzu ina 2lv, jawaheer tace Allah sarki Allah ya baki lfya, murmushi zarah tayi tare da fadin baki fadamin sunanki ba, tace jawaheer murmushi zarah tayi tace suna mai dadi zarah ta amshi no din jawaheer tare da fadin in akwai lecture zata dinga fada mata, sannan tace duk abunda jawaheer bata gane ba ita zata dinga nuna mata, nan jawaheer tayi godiya tare da fadin an gama lecture din yanzu? Zarah tace a'a akwai wanda zai zo karfe hudu, jawaheer tace kai bari inje inci wani abu yunwa nake ji, zarah tace muje tare toh, fita sukayi tare suka je wani restaurant a cikin skul din, fried rice jawaheer tace a bata, ita kam zarah snacks ta amsa da drinks suna ci suna fira har suka gama, fita sukayi suka zauna wajan wata bishiya ko wacce na danna wayarta, wayan jawaheer aka fisge daka hannunta da sauri ta dago taga ko waye khalil ta gani dariya tayi tare da fadin bros mai kazo yi? Yace zo muje ki gani, zarah ta dago kai tare da kallon khalil gaidashi tayi jawaheer tace bros dina ne, tace ashe yayanmu ne, dariya yayi sannan yace ma jawaheer ga mota can kije ana jiranki ni bari in zauna a nan muyi fira da zarah, dariya tayi sannan ta nufi motar dan a zaton ta dad ne, tana budewa taga m samir zama tayi a cikin motar tare da rufewa shine a mazaunin driver daka gani shine ya tuka motar, kallonta yayi tare da fadin baki so gani na ba koh? Tace a'a , yace mai yasa kika daure fuska? Tace babu komai, murmushi yayi tare da fadin jawaheer yau baki damu da inda na shiga ba, baki kira niba, tace bani da abunda zance maka ne, yace ok toh bari in tafi, bata bude kofar ba sannan bata motsa ba, ya kuma cewa zan tafi, kallonshi tayi da idonta daya rine kadan kawai take jira tayi kuka, janyota yayi jikinsa yace karki sake kice zaki fito da wannan hawayen, jawaheer na rasa mai yasa ko kadan bana son ganinki cikin damuwa, bana son inyi nesa dake na saba dake cikin lokaci kadan, gobe zan tafi inaso plz koda na tafi kici gaba da riqemin kanki karki bama kowa daman shiga rayuwanki, dagowa tayi ta kalleshi dan bata gane mai yake nufi ba, murmushi yayi tare da fadin nan gaba kadan zaki fahimta abunda nake nufi, but yanzu ina son ki riqemin kanki ban son ko wani namiji ya shigo cikin rayuwanki, naso mu tafi tare sai naga koda munje banda tym nd ban son in barki cikin kadaici, shuru tayi tana tunani toh mai yake nufi kar inbar wani ya shiga rayuwa na? So yake in zauna banyi aure ba..... Katseta yayi da fadin zanyi missing dinki sosai, murmushi tayi tare da fadin nima haka, yace taya zan gane? Murmushi tayi tare da fadin komai kaji na fada a kanka dagaske nake kuma hakan nake ji, a musulunce mace zata iya fadama namiji tana son shi, amma a al'adance abun kunya ne, samir a kasar ku na fada maka ina sonka, amma ka nunamin inyi hakuri naji kuma nayi duk da ban cire raiba, amma a yanz..... Shuru tayi yace yanzu me?? Na hakura dakai ina son nima in sami mai sona inyi aure bada dadewa ba, kallonta yayi yana dan nazari kafin yace zaki iya auran namijin da baya sonki? Tace zan iya indai ni ina sonshi, murmushi yayi tare da fadin mai kike tunanin zai faru bayan auren? Tace zaman hakuri, yace har zuwa wani lokaci zaki ta zaman hakuri dashi, tace bazan iya sani ba, amma idan hakan ya faru zuciyata zata yanke a lokacin, yace ok naji zaki iya aurena bayan kin san bana sonki? Wani irin hawaye ga zubo mata, tace zan iya burina a kullum in kasance dakai a koda yaushe, yace jawaheer shikenan nayi miki alkawarin zan aureki amma inaso ki sani ban taba kallonki a matsayin budurwa taba, sai yar uwata, inaso kiyi tunani akai indai kin amince nanda wata biyu za muyi aure in kuma baki aminceba shikenan kiyi tunani akai, shuru tayi na wani lokaci sannan tace bana tunani akan sonka a kullum tunani na shine in sameka a matsayin miji dan haka na amince, yace ok zan fadama dad yau sai a fara komai duk abunda kike bukata sai ki fadamin, amma ina so ki sani indai kika shigo babu saki kar nan gaba kice baki son zaman, murmushi tayi tare da fadin bana tunanin baki na zai iya fadin haka,yace good zamu koma gida anjima sai mu karasa magana dama ke nazo in gani, tace ok sannan ta fara kokarin bude kofar amma yaki buduwa, kallonshi tayi alaman ya bude mata, yace haka zaki faramin babu wani abu sai kawai ki fita, rufe ido tayi tana dariya sannan ta matsa kusa dashi ta mishi peck a goshi, dariya yayi sannan ya bude mata motar ta fita, da ido ya bita har ta karasa wajan su khalil da suke ta fira shida zarah, tace toh saika tashi ku tafi dariya yayi tare da cema zarah sai munyi waya, tace ok, sannan ya tafi, jawaheer kallon zarah tayi tace badai har an kulla luv ba? Zarah tace haba luv a minti nawa, dariya suka sa dai2 lokacin wannan lecturer din yazo yace ma jawaheer tazo yana son ganinta, bayan ta matsa kusa dashi yace ga no dinshi yana son ta kirashi, bata yayi tasa sannan ta koma wajan zarah tana fada mata abunda yace mata, zarah tace haba nayi mamakin dabai koreki ba, ashe ya kamo fish, dariya sukayi har 4 yayi suka shiga lecture basu fitoba sai 6 gida ta nufa direct a gajiye ta shiga gida babu kowa a falo dan haka tayi dakinta, tana shiga toilet ta nufa tayi wanka wardrobe dinta a kusa da toilet dinta yake kaya tasa sannan ta fito tana fitowa taga mutum a dakin yana kalle kalle, kallonta yayi rai a bace sannan yace jawaheer jiba dakin ki duka pics dina ne harta carpet dinki, indai kina sona mai yasa kike kula wasu mazan?? Ido ta dan zaro alaman wana kula..... Tace ni yaushe kum...... Ya isa ban son jinki dazu waye naga yana baki number kina sawa?? Shuru tayi kaman ba zatayi magana ba, can tace lecturer dinmu ne fah, yace lecturer number din mai yake baki?? Tace yace in kirashi ne zai mun magana, ido ya lumshe ji yake kanshi na mishi wani irin tafarfasa lokaci daya idanshi ya kade yace mai zaki mishi idan kin kira shi? Tace nima ban sani ba, kallonta yayi kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita fuuuuuuuu, dakinshi ya nufa zama yayi akan gadon dakin shidai yasan bawai son jawaheer yake ba, kawai yana tausaya mata sai yasa yake son ya aureta sannan baya son tana nesa dashi, to mai yasa nake kishi idan wani yana mata magana?? Wata zuciyar tace saboda kana sonta da sauri yace nop, kawai dai dan zan aureta ne dole kuma inyi kishi a kanta,karan wayanshi ne yasa ya dauka yaga dad din su khalil ne dauka yayi dad din yace mishi samir gani na dawo ina falo, yace ok dad ga ninan, tashi yayi ya fita ya nufi falon, samun dad yayi da mum akan dinning dad yace samir ya gida gobe ne tafiyan koh? Yace eh dad, dad yace masha Allah, Allah ya taimaka, yace ameen, yace dad dama inaso inyi maka magana nida jawaheer mun fahimci juna, kuma...... Dan shuru yayi dad yace inaji, yace muna son muyi aure in kun amince, dad cikin murmushi yace alhmdlh alhmdlh abu yayi kyau, mum tace toh yanzu ya za'ayi, amma inaga da an jira an duba iyayenta koh? Dad yace a'a in ba'a gansu ba fah, haka zatai ta zama? Kinga dole kuwa tayi aure, mum tace hakane, m samir yace dad plz ban son bikin ya wuce wata daya, mum harara ta sakar mai tare da fadin toh mara kunya, kai ya sosa tare da tashi yabar wajan suka bishi da dariya, dakinshi ya koma ya kwanta haka kawai yake jinshi cikin farin ciki da annashuwa, haka har bacci ya daukeshi,.