Sashe 19
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Koda suka isa asibitin, suka karasa dakin inda suka iske jawaheer na sallah shi kuma m samir na danna wayanshi ba komai yakeyi ba sai game, dan bashi da sim card din nigeria bai samu ya siya bama, ganin sun shigo yasa ya tashi da sauri yana fadin sannu da zuwa mum, cikin harshen turanci amsawa tayi cikin sakin fuska, sannan tace mai jiki anji sauki kenan, yace eh alhmdlh, sai a sannan ya gaida su mlm da abubakar, mlm murmushi yayi tare da mika mai hannu danshi baya jin turanci, amma abubakar naji, mlm yace ni wannan yaran naku ban iyashi ba, duka suka saka dariya, mum tace ma m samir ga kakanshi shine babanta, ga kuma yayanta ta nuna abubakar, nan m samir ya kara gaidashi tare da fadin uncle ina farin cikin haduwa daku, abubakar yace nima haka uncle dinka yana cikin masoyanka danni dan barcelona ne, kuma kai nake so, dariya m samir yayi tare da fadin thanks my uncle, dai dai lokacin jawaheer ta idar da sallah, itama gaida mlm tayi cikin harshen hausa, amsawa yayi tare da fadin ya jikin naki? Tace da sauki alhmdlh, sannan ta gaida abubakar shima ya amsa cikin sakin fuska, nan mlm ya zauna kusa da jawaheer suna ta fira yana ta janta da surutu tana ta dariya m samir kuma ya matsa kusa da uncle dinshi yana fadin wai mai yasa take dariya mai ake fada mata haka? Dariya abubakar yayi yace wasa yake mata yana fadin shine zai aureta amma itace zata biya sadaki dan taimaka mata zaiyi, shima m samir din dariya ya farayi yi, tare da fadin uncle nima ina son koyan wannan yaran naku, abubakar yace ai babu wuya sai in fara koya maka, gashi naji ance gobe zaku tafi, kallon jawaheer yayi yace sis mu dan zauna a nan na kwana biyu mana, murmushi tayi tace ok duk yanda kace bani da zabi, yaji dadin abunda tace yana son biyayyan jawaheer tana son abunda yake so, mum ce tace au nama manta taci abincin kuwa?? M samir yace eh taci amma bada wani yawa ba, mum tace jawaheer kin taba ganin ana ciwo babu cin abinci?? Tace mum nafa ci kadan na rage, murmushi mum tayi dai dai lokacin dad ya shigo dauke da ledoji a hannunshi, mum ta tashi ta amsa tare da ajiyewa kayam fruit ne dasu kaji gassasu, mum taba jawaheer kaza daya ta mika ma mlm da abubakar mlm yace a'a shi tare da matarshi zaici dariya duka sukayi m samir shima yaci kazan yana ta fadin kazan akwai dadi suna tamai dariya yanda yake ta santi, dad yace jawaheer kinji sauki koh? Tace eh dad sai dai bana jin dadin komai amma ganin mum da kakana yasa naji dadi sosai, kowa ya fahimta abunda take nufi wato shiryawan mum dinta da mahaifinta yasa taji dadi sosai, kowa dake dakin saida yaji tausayinta tare dayi mata fatan itama Allah ya hadata da iyayenta, dad yayi murmushi tare da fadin Allah ya kara miki lafiya bari muje mu kwanta dare yayi, duka kowa ya fita amma banda m samir da mum, m samir yana son yi mata magana amma bazai iyaba dan mum na wajan haka ya fita tare da fadin good night, ji tayi kaman ta bishi, koda ya fita ya tarar dasu a waje, abubakar yace ma m samir a gidanshi zai kwana, security dinshi sukace ma abubakar dan Allah yayi hakuri an basu tsaronshi ne idan wani abu ya faru dashi zasu shiga matsala, duk yanda abubakar yaso m samir ya kwana a gidanshi haka ya hakura akan gobe zasu hadu, koda m samir ya koma hotel din daya sauka wanka yayi ya kwanta amma bacci yaki zuwa, sai juyi yake tayi gaba daya tunanin jawaheer yake tayi wanda ya hanashi sakat, ya rasa dalilin da yasa yake tunaninta har yake kokarin hanashi bacci abunda bai tabayi ba kenan ko sonia da yake so baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a yanzu, dan tsaki yayi tare da fadin tausayinta nake ji sai yasa nake tunaninta.....
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 29-30
Haka yaita tunani kala2 yayinda yake ta tursasa ma zuciyarshi akan tausayinta yake kawai, wasa2 har wajan karfe biyu amma babu alaman bacci a idonsa sai tunanin jawaheer gaba daya ma kanshi ya kulle yama rasa mai yake ji a kanta, ganin babu baccin a idonsa ga tunanin yaki barinsa yasa ya tashi ya shiga toilet yayi alwala, sallah yazo yayi tare da roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi a rayuwanshi, ya dauki lokaci mai tsawo yana roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi, kafin ya tashi ya koma gado yana kwanciya bacci ya daukeshi.
Ta gefen jawaheer ma haka abun yake bata so m samir ya tafi ba, ita inda so samu nema dashi ya kwana da ita amma sai dai hakan bamai yihuwa bane, babu abunda take sai tunaninshi tare dason qara ganinshi, duk da sau da yawa zuciyarta tana kara nuna mata tayi baya dashi dan ba sonta yake ba, amma ta kasa, a yanda takeji inda tana da halin cireshi a ranta data dade da cireshi, itama haka taita tunani har bacci barawo yayi awon gaba da ita.