Sashe 16
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Jawaheer kam ko motsi batayi, m samir iya tashin hankali ya shiga gaba daya ya fita cikin hayyacinsa, mum ce ta shigo dakin domin a lokacin anata kiran sallah la'asar, kama hannunshi tayi wanda ya rike na jawaheer dashi, dagowa yayi da sauri wanda yake zargin jawaheer dince amma sai yaga sabanin hakan, mum ce cikin kuka take mai magana cikin harshen turanci tace kaje kayi sallah,baiyi magana ba sai tashi da yayi ya fita dan yin sallah, haka su mum sukai ta zama amma shuru bata farka ba, abun ya damesu sosai gashi har wajan karfe biyar yanzu gaba daya hankalinsu a tashe yake, mahaifiyar mum ce tace nikam bilkisu itama wannan din yarinyar kice? Mum zatai magana taga kaman jawaheer tana motsi da sauri ta nufeta tana kiran sunanta tare da fadin jawaheer ganin idon jawaheer din a bude yasa ta furta alhmdlh da sauri ta fita lokacin su dad na waje da m samir dad na ganinta yace bilkisu lfya kuwa? Tace ta farka zan kira dr ne, dad yace bari in kira shi, m samir da mum suka koma dakin, m samir suna shiga ya nufeta ganinshi yasa ta sakar mishi murmushi amma ta kasa magana, shima ya kasa furta mata komai sai murmushi da yake ta sakar mata shima, dr ne ya shigo dakin wanda yasa m samir niyan barin wajan amma ta rike mai hannun alaman ya tsaya, dr ganin haka yayi murmushi tare da fadin lovers, matsawa dr din yayi ya fara dubata tambayanta ya farayi amma bata bashi amsa da baki sai dai ta daga mishi kai kota girgiza mai kai, hankalinsu ya tashi sosai ganin taki magana dad yace dr mai yasa bata magana? Dr yace nima abunda nake son sani kenan amma karku damu zatayi, dr yace amma alhmdlh jikin da sauki nayi mamaki ta tashi ba tare da wani matsala ba, gskya ku kara godema Allah, dad yace toh dr ni yanzu magana kawai nakeso tayi, dr yace madam kice wani abu plz, ido ta lumshe alaman karma ya dameta, mum ta matso kusa da ita, tana fadin jawaheer plz kiyi magana, bude ido tayi ta kalli mum lokaci daya hawaye ya zubo mata sannan bakinta ya fara rawa tace mum, kowa ya kura mata ido ta kara matse hannun m samir sannan taci gaba da fadin mum m samir danki ne na cikin ki? Mum dan Allah ina son sani ance sunan mum dinshi khausar ba sunanku daya ba mum dan Allah ki fadamin maike faruwa wlh mum ban san mai yasa na tashi ba amma haka Allah ya tsara dan Allah mum ki fadamin miye tsakaninku ko zuciyata zata samu salama daka radadin da takeyi a halin yanzu, mum kuka ta farayi tare da fadin jawaheer zan fada miki komai kaman yanda kike son ji duk da banso fada miki ba, amma inason in kinsan gskya karki juyamin baya karki gujemu duk rintsi duk wuya.......
TUNA BAYA.....
Garin yola garine na fulani mu uku iyayena suka haifa a duniya ni daya ce mace a wajansu, yayyina maza ya abubakar sai ya abdullahi saini bilkisu wacce naci sunan kakata ake cemin khausar, mahaifina mlm kabiru shine limamin anguwanmu mutane suna girmamashi mahaifiyata kuma nafisa, muna kiranta da adda, ita daya ce wajan mahaifinmu duk wani gata da dan gata yake samu suna nuna mana duk da alokacin ba'a karatun boko bawai ba'ayi bane a'a anayi sai dai ba'a bashi muhimmanci, mahaifina koda haiyuwa akayi kasancewan shine liman shine yake radama yaro suna, sannan komai mai gari zaiyi saida saninshi, tunda na taso nake tallan nono domin wannan dabi'an fulani ne musamman wanda suke kauye, akwai dan mai gari wanda yake sona bayaji sosai gashi kashe mutum a wajanshi ba komai bane, sannan iyayena tun ina karama suka bashi ni dan haka irin tasu al'adan yake ana haifanki za'ayi kamunki, a bama wani ke ma'ana anyi miki miji tun kina karama, gashi kuma koda bakwa son juna baku isa ku karya alkawari ba, tunda na taso na tsani auwal, gashi yana bala'in sona, ko yazo wajena bana wani bashi fuska, akwai wani ma'aikata da nake kai nono inda na hadu da muhd mahaifin samir lokaci daya muka saba harya fara koyamin turanci daka baya ya fara sona, ya sami mahaifina akan yana sona, inda ya nuna mishi bazai hada zuri'a da farin fata ba wato bature bai fito ya fada mishi anyi min miji ba, babu yanda baiyi ba amma mahaifina yaki, irin son da muke ma junanmu wata rana naje wajanshi dan saboda shi gaba daya aka hanani tallan nono, na sata jiki naje, inda mukaci kukanmu har yakai daya fara ban hakuri yana sharemin hawaye sanadin da shaidan ya rinjayemu kuka ta saki sosai sannan taci gaba mun aikata sabon Allah, tunda na tafi ban kara fitowa ba har saida aka gano inada ciki hankalin iyayena ya tashi sosai nan sukai ta buguna tare da yayyina inda sukace in ban fadi wanda yamin ba sai sun kasheni, jin naki magana sukace wlh zuwa dare in ban fadaba sai an jefeni gashi kowa a gidan lokacin ya shareni babu maijin tausayi na, haka na sata jiki na samu muhd nake fada mishi abunda ya faru, mai makon inga yayi fada sai daga hannu yayi yana godiya tare da fadin rabo rabo lallai koba ta hanyar aure ba inda rabo sai an samu, kuka na fara mishi akan yabar garin dan wlh zasu iya kasheshi da farko yaki yarda sai dakyar ya amince dan saida na mishi alkawarin baza'a zubar da cikin ba sannan yabar kasar gaba daya, haka na koma gida iyayena suka kara rufeni da duka kaman zasu kasheni waina dauko musu abun kunya, in ban fadi wa yayi min ba sai sun kasheni, da naji wuya tare da tunanin muhd yabar kasar ma yasa na fada musu wanda yamin sun shiga tashin hankali sosai, gashi anje inda yake aiki ance yabar kasar, haka iyayena sukace a zubar da cikin naki yarda babu irin abunda ba'ayi ba amma cikin yaki zubewa, har yan gari suka san labarin abun kunyan dana aikata ko waje bana fita dan gori da zaki abun bama ni daya ba harta iyayena ana musu gori wanda hakan yasa aka cire mahaifina daka liman akaba wani, abun yama mahaifina ciwo wanda hakan yasa kaf yan gidanmu suka kara tsanata har gwara adda tana tausayamin in babana baya gida, ana haka har na haiyu cikin rashin gata, har nayi arba'in cikin dakin datti nake kwana da yarona, kwananshi arba'in da daya a duniya na nemeshi na rasa, nan aka dauka mahaifina ya kashe yaron ya boye, aka tsanemu a garin da kyara zagi wanda mahaifina yayi zuciya tare da fadin inbar gidan sannan inna kara zuwa mai gida Allah ya isa bai yafe min ba, babu irin hakurin da adda bata bashi ba amma yace inta kara magana a bakin aurenta, haka tana gani na tafi yayyina sune masu kara zugawa waina dauko musu abun kunya basa iya shiga cikin mutane, haka nabar gidan cikin dare banda kudi banda kowa, duk wannan abunda akamin ban damuba kaman rashin yarona wanda nake gani kaman mahaifin nawa ne ya daukeshi dagaske din, gaba daya na kara tsanan zaman kauyen ma tare da fadin gwara da aka koreni ma, haka naita tafiya cikin dare harna bar anguwanmu ina cikin tafiya ne cikin sauri saboda tashin hankali ko gajiya banyi ba, wata mota ta rugo a guje saura kadan ta bugeni, Allah ya taimaka, mutumin ya fito yana fadin haba baiwar Allah miye hka bakya duba hanya gashi cikin dare ina zaki, nace duniya zan shiga, yace subhanallah, haba baiwar Allah mai yayi zafi haka, kuka na saki tre da bashi labarin abunda ya faru ya tausayamin sosai inda yace in shiga motarshi muje ban musa ba na shiga sai naga ya nufi anguwarmu, direct gidan mai gari mukaje inda yayi2 in fito naki, haka ya shiga jim kadan saiga mai gari da mutane sun fito inda akasa na fito dole, mai gari yace wannan yar iskan zaka aura bawan Allah ko dai kaine ka mata ciki? Yace wlh ko daya, nan aka tura aka kira mahaifina bayan yazo ya ganni yace baya kaunar ganina, mai gari yace ya nutsu nan aka mishi bayani inda yace shiba mahaifina bane ya sallamani zan iya yin duk abunda naga dama tare da fadin har abada baya bukatar ganina,haka mai gari ya daura mana aure da mutumin da ba'asan ko waye ba......
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 23-24