← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 45

Sashe 18

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jawaheer kam kallonsu take Amma ita daya tasan abunda take saqawa a ranta, shiko m samir idonshi na kanta gaba daya tausayinta yake ji, ya rasa dalili mai yasa yake jinta a ranshi yanzu, amma ta wani gefen yana ganin kaman tausaya mata yake dan shima ya taba shiga irin halinta na rashin mahaifiya lokacin da yasan mum dinshi na raye ba karamin ciwo yaji abu, itace ta zauna kusa dashi tare da kwantar mai da hankali wanda gashi yau sun hadu da mum dinshi duk ta sanadin jawaheer din, gashi kuma sanadin haduwanshi da mum dinshi yasa jawaheer tasan basu bane iyayenta, ido ya lumshe tare da fadin no matter what i will stay by ur side, jawaheer matsawa yayi kusa da ita, kallonshi tayi ta sakar mishi murmushi wanda bata san ya fito ba, shima murmushin ya sakar mata tare da fadin ya jikin naki? Tace naji sauki sai dai bana jin dadin zama a nan, inaso in koma abuja, yace kiyi hakuri gobe zamu tafi, kai ta daga mai alaman toh, adda tace bari inje gida dare yayi kar mlm ya dawo yaga bana nan,nama san yana gidan yanzu inna koma a kawo abinci, dady yace ki bari adda zamu siyo yanzu, nima inaso inga mlm ya kalli mum yace bari muje, jawaheer tace dad, cikin sauri duka suka kalleta, tace kuje da mum itama nasan tana bukatar ganin kakana, kowa dake dakin saida yaji tausayinta, mum tace a'a babu inda zani dawa zaki zauna, tace mum naji sauki kuma m samir zai zauna dani kije kiga kakana, mum wani hawaye ne ya zubo mata tare da zuwa wajan jawaheer ta rungumota tana fadin dan Allah duk wuya karki barni jawaheer ban taba banbantaki da yaran dana haifa ba, jawaheer ina sonki haiyuwanki ne kawai banyi ba amma wlh baki da banbanci da yarana, jawaheer itama cikin kuka tace insha Allah mum bazan taba gudunki ba, bani da wata uwa saike.... Kuka yaci karfinta dakyar ta seta kanta tace mum kije dare nayi, mum kallon m samir tayi tace ka kula da ita nima anjima zan dawo tare zamu kwana da ita, yace ok, sannan suka fita.

Bayan sun fita m samir ya zauna kusa da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer kibar kukan nan haka, ya isa, murmushi tayi tare da fadin yana da amfani domin shine kawai nakeyi inji dadi, ido ya kura mata ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar dakai gefe, kirjinta yana buga mata da karfi duk sanda suka hada ido jin muryanshi tayi yana fadin bakya jin dadi in kina tare dani?? Da sauri ta waigo suka kara hada ido wani tambayan ya kuma jefo mata yace jawaheer mai kikeji in kina tare dani?.......

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 27-28

Idonshi nakan nata yana jiran yaji mai zata ce, yayin da ita kuma tambayan yazo mata a bazata, dan haka yasa ta kasa koda motsa baki balle ta bashi amsa, ganin irin yanayin data shiga yasa ya hura mata iska a fuska wanda yasa ta lumshe ido da sauri, ido ya kara kura mata yana dan murmushi tare da fadin jawaheer kina da kyau sosai, da sauri ta bude ido dan ta gani ko shi dinne dagaske yake fada mata haka, ido ya kashe guda daya kaman yasan abunda yake ranta, yace kina mamaki koh? Gaskiya nake fada miki, kina da kyau mai daukan hankali jawaheer tun sanda na ganki naji kina min kama da larabara ina mai kyautata zaton kina da jini da larabawa, duk namijin daya sameki zaiji dadi sosai, sannan duk wanda ya aureki zanja mishi kunne ya riqemin ke da kyau, wani iri taji domin magananshi ta karshe ya nuna mata bawai yana sonta bane, jin tayi shuru yasa yaja hancinta tare da fadin jawaheer kin sani cikin farin ciki sosai ta sanadinki yau gani ga mum dina, kema Allah ya nuna miki iyayenki, kai ta girgiza tare da fadin bana bukatar ganinsu har abada zanyi rayuwa na ni daya ba tare dasu ba, ido ya kura mata ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar da kanta gefe, yace har cikin zuciyarki kike fadan wannan maganan?? Shuru tayi ba tare da tace komai ba, yace ki bani amsa, kuka ta saki tare da fadin mai zance da yafi wannan? A da ina farin ciki sosai tare da iyayena, amma lokaci daya komai ya canza min tunda nasan basu bane iyayena, ina mamakin mai yasa mum dina ta bada ni, ta tafi ta barni...... kuka yaci karfinta sosai janyota yayi jikinta ya rungumeta yana bata hakuri akan tayi shuru, dakyar ya samu tayi shuru, yace jawaheer inaso koda yaushe ki kasance maiyi ma kowa uzuri, karki yanke hukunci akan abunda baki san miye asalin faruwanshi ba, haka kawai mahaifiyarki ba zata bada keba, lallai akwai wani abu a labarinki, wanda hakan ya zama dole mu nemi mum dinki, jan jikinta tayi a nashi tace nemanta bashi da amfani bani da wani buri daya wuce in sami namijin da nake so, shima yana so na, wanda za muyi rayuwa cikin jin dadi sai sai kash, hakan bamai yihuwa bane, ina tunanin barin kasar nan gaba daya inyi nesa da kowa na wani lokaci, ido ya kura mata yana kallonta harta gama, yace har dani za kiyi nesa dani? Shuru tamai ba tare data bashi amsa ba, yace ina jinki jawaheer? Tace ni kawai so nake in huta, yace ba amsan da nake son jiba kenan, satan kallonshi tayi amma sai akayi rashin sa'a shima din ita yake kallo caraf suka hada ido, ya daga mata akai alaman ina jinki, tace nifa bance zanyi nesa dakai ba, murmushi yayi yace gashi kince za kiyi nesa da kowa, tace ni banda kai nake nufi, wannan karan dariya yayi tare da fadin jawaheer bazan taba barinki ba har sai na sadaki da mum dinki wannan shine alkawarin dana daukan miki, wani hawaye ne ya zubo mata tace mai yasa zaka min haka? Yace saboda u r my sister my best friend, ke kawata ce daka yanzu, wani irin murmushi ta saki lokaci daya tare dayin hugging dinshi tana fadin thanks alot.

Bayan su mum sunje gida dad yaba driver kudi yace yasai abinci yakai masu jawaheer, sannan suka shiga cikin gidan, koda suka shiga falon baki suka zauna, basu dade da zama ba saiga mlm ya shigo falon yana fadin kai yau na gaj..... Bai kai da karasa maganan ba idanshi ya sauka akan bilkisu duk da tayi dan jiki kadan da kuma haske, hakan baisa mlm yaki ganeta ba, da hannu ya fara nunata yana fadin bilkisu, kece? Sai kuma ya daga hannu sama yana ma Allah godiya tare da hawaye wanda kana gani kasan na farin ciki ne, yace khausar matso kusa dani, da sauri mum ta karasa wajanshi itama tana kukan rungumeta yayi yana fadin dan Allah ki yafeni khausar nasan nayi miki ba dai dai ba, ki gafarce..... Tace haba baba ka daina neman gafara na kaifa mahaifina ne, komai kayi a kaina kayi dai dai, mlm yace Allah ya miki albarka khausar sai a sannan ya lura da dady, yace jibrin sannu, nan dady ya gaida mlm cikin girmamawa, mlm ya fara mishi godia akan irin riqon da yayi ma yarshi dan daka gani bama sai an tambaya ba kasan tana cikin kwanciyan hankali, adda ce ta shigo dauke da tray ruwa ne akai da zobo da kofuna, ta ajiye a falon, mlm yace yau ina cikin farin ciki sosai adda tayi dariya tace ina abubakar? Mlm yace yanzu zai shigo yaje anso mi..... Kafin ya karasa sukaji sallamanshi amsawa sukayi su duka ya shigo shima dai ba karamin farin ciki yayi ba na ganin kanwar tashi, nan adda tahau bama mlm labarin abubuwan da suka faru mlm yasha mamaki, yayi shuru can yace ita yarinyar tana asibiti ne da yaron naki? Mum tace eh amma yanzu zan koma dan inaso in kwana da ita gobe wai take son ma mu koma abuja, mlm yace kai da wuri haka muje asibtin tare nima inga yaron da kuma ita mai jikin, haka suka fita harda abubakar adda kawai suka bari a gida.
Chapter 18 · 0% Book details