← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 45

Sashe 12

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan ta kashe wayan ne ta kalli m samir daya zuba mata ido yana kallonta, saurin kawar da kanta gefe tayi, murmushi yayi tare da fadin wannan wani yare naji kinayi? Tace hausa, kasa fadin hausa yayi dan haka abun ya bata dariya, yace ya akeyi yana son ya iya, tace babu wuya mu a nigeria shine yaran da kowa yakeyi akasarin mutanan kasata koda wata kabila ne zaka sameshi yana jin hausa koda babu yawa domin hausawa sunfi yawa a kasar, yace a nigeria yare daban daban akeyi? Tace eh akwai yare kala kala, akwai fulani, hausa, igbo, yaruba, tibi, igala, idoma, ibra, kurama, gwari, da sauransu, yace kai yare da yawa haka a kasa daya kuma duka yan kasar ne? Tace eh duk yan kasar ne, yace wow inaso inga wa innan yaren, ke miye naki yaren? Tace fulani ce ni, dan shuru yayi sannan yace dayan yaran da naji kinayi ba naki bane kenan? Tace eh, yanda take mishi bayanin abun na sashi cikin nishadi yayin da take ta kara bashi labari akan kasarta shi kuma yana jin dadi, ganin irin kallon da yake mata yasa tayi shuru tare dayin kasa da kanta tana wasa da hannunta, murnushi yayi tare da kiran sunanta yace jawaheer dago kai tayi suka hada ido tayi saurin yin gefe da idonta, domin indai suka hada ido wani irin yanayi take shiga mai wuyan fassaruwa, yace kece mace ta farko da nake son yin fira da ita, idan ina magana dake inajin dadi sosai, i will like you to be my sister, murmushi tayi tare da fadin thanks alot yau ina cikin farin ciki daka daukeni a matsayin kanwarka, insha Allah zakai farin cikin zamana kanwarka tare da alfahari dani, mika mata hannu yayi alaman su gaisa, tashi tayi ta nufeshi tare da bashi hannu yace i luv you sister, shuru tayi domin ta lula wata duniyar inama ace yau wannan kalman daya fada mata a matsayin masoyiyyarshi da bata san wani irin farin ciki zatayi ba, hawaye ne ya fara zuba a idonta, jin hannunshi tayi yana goge mata da sauri ta dago ta kalleshi, shima dai ita din yake kallo, tace yau ina cikin farin ciki ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa na, wannan kukan da nakeyi na farin ciki ne, yau gani ga ka, kafin in ganka an fadamin ganinka tashin hankali ne amma da yake Allah mai tausayin bayinsa ne sai ya hadani dakai ba tare da nasha wahalan da ake fada ba, sai yasa ake cewa kar bawa ya cire rai da ikon Allah, na tabbata addu'ata ce Allah ya amsa sai yasa ya hadamu cikin sauki, yace hakane sister babu abunda Allah bazai iya ba, komai ya faru da bawa ya dauka a matsayin kaddara ne a rayuwanshi...... Shuru yayi lokaci daya kuma yace tabbas dad dina bashi da laifi dan an sameni bata hanyar aureba, lallai haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canza hakan, laifi daya dad dina yayi daya raba mum dina dani, jawaheer tace shima yana cikin kaddaranka, kallonta yayi ta daga mishi kai alaman eh tace haka Allah ya tsara maka sannan gashi ta sanadin haka mun kara samun kusanci haduwa na dakai shima yana cikin kaddaranka........

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 17

*ina yinku masoya novel din jawaheer kaman yanda kuke son novel din jawaheer nasha kira da message kuyi hakuri na jina shuru insha Allah zan dinga muku posting kullum koda ba yawa😆*

Yace kaddarana?? Kai ta daga mishi alaman eh, tare da fadin gashi ta sanadi na zaka kasata nigeria, murmushi yayi tare da fadin hakane harna kosa inje koh Allah zaisa inga mum dina, inko hakan ta faru ban san wani irin farin ciki zanyi ba, jawaheer tace insha Allah zaka gan..... Bata karasa ba tayi shuru tana kallonsa shima din ita yake kallo cikin sanyin murya tace kana da pic dinta?? Shuru yayi can yace a'a bani dashi, tace sunan anguwansu a yola din fah? Shima yace bai sani ba, jawaheer tace toh taya zamu nemota?? Wannan ba abu bane mai yuhuwa dole muna bukatar sunan anguwansu ko kuma hotan ta, wani irin zufa ne ya keto ma m samir wanda gaba daya shi baiyi tunanin haka ba dan yana ganin yana zuwa nigeria zaiga mum dinshi toh taya ma zai ganta shida bai santa ba, bai taba ganin hotanta ba, hannunsa ya buga a dayan hannunshi tare da tashi ya kalli jawaheer yace zanje wajan dad dina ya fadamin sunan anguwan su, coz i only know her name, fita yayi da sauri, duk da dingishi yakeyi, koda ya fita security dinshi na nan tsaye suna jiranshi, yace ku dauko mota muje gidan dad, daya ne ya tafi sai gasu da mota har biyu ya bude ta farkon ya shiga, kai tsaye gidan dad dinshi ya kara nufa, a falo yaga dad din nashi a zaune idanshi yayi ja, yana ganin dan nashi ya tashi da sauri ya rungumeshi yana kuka, jikin m samir yayi sanyi tare da tausayin dad din nashi, cikin kuka dad din ya fara magana samir yanzu zaka gujeni koh? Zaka koma wajan mum dinka gaba daya, bazan bar hakan ya faru ba, dad din mum dinka yaki bani ita bai lura da irin son da nake mata ba, dan kawai ni farin fata ne bai lura da cewa duk musulmai daya bane, samir har yanzu ina son mum dinka sai yasa nake masifar sonka ban san damuwa a tare dakai in wani abu ya sameka inaji kaman mum dinka ya sama, plz dnt leave me, m samir ya danja jikinshi daka na dad din nashi ya fara magana kaman haka dad bazan taba gudanka ba kaine mahaifina nasan irin son da kake min amma dad plz ka barni inje inga mum dina koda once ne in my lyf, tasan danta bai mutu ba sannan tasan danta baya mugun hannu, na tabbata har yanzu bata cikin nutsuwa tunda danta ya barta, dad din kai ya girgiza yace ina tsoran kaje kaki dawowa son, m samir yace dad indai ka fadamin inda take one week zanyi kawai in ganta in dawo kasan inada wasa nan da sati biyu, dad din shuru yayi can ya nisa yace sunan anguwansu guyuk idan kaje kace a nuna maka gidan liman, murmushi m samir yayi najin dadi yace ashe kakana liman ne a anguwansu, dad din yace eh, sannan yace toh taya zaka kaida baka san kasar ba? Yace dad akwai wata yar nigeria tare zamu, dad yace wacece a ina ka santa? Murmushi yayi tare da fadin haba dad nifa duk wanda nace maka na sani ba abun mamaki bane, dad yace hakane amma ya akai tazo wajanka harta ganka kuka hadu kuka saba, dariya m samir yayi yace hadin Allah ne, dad din murmushi yayi tare da fadin ina son ganinta, m samir yace gobe zan kawo ta bari in sanar da minister zan tafi nigeria jibi suyi arranging dad din yace ok m samir tashi yayi tare dayi ma dad din sallama.

Tunda m samir ya fita jawaheer taji wani iri amma taji dadin sabawansu lokaci daya ido ta lumshe tana jin nishadi, burinta har yanzu bai wuce ace yau ya yarda zai aureta ba ita koda zai aureta baya sonta zata so haka, amma tunda yace a matsayin kanwa ya dauketa hakan ma abun alfahari ne a wajanta wasu ma signing dinshi suke nema su samu amma abun yaci tura ita kam gata gashi har kissing dinta ya taba yi wani murmushi ta saki cikin jin dadi haka har bacci ya dauketa.
Chapter 12 · 0% Book details