← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 45

Sashe 35

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta fita ya kwantar da set din motar ya kwanta bai kashe motar ba dan ya kunna ac, pictures din jawaheer yake ta kallo a wayanshi yana murmushi lokaci daya ya furta u wil be mine very soon, jin kaman ana kokarin bude motar yasa ya dago dakai ya ganta ita da zarah, bude mata yayi ta shigo zarah ta gaidashi ya amsa tare da fadin gobe zaku tafi koh? Tace eh insha Allah, yace ok ki kulan min da ita fah sosai, dariya zarah tayi tace baka da damuwa indai dan wannan ne, yace ya gode tare da fadin in kun dawo sai inji ya kuke irin naku bikin zarah tace ok zaka ji komai da komai dariya yayi sannan sukai sallama, jan motar yayi suka bar skul din, mai makon suje gida saiya biya dasu wajan wani shan ice cream wanda turawa da manyan masu kudi suke zuwa wajan, mutane na ganinshi suka rugo da gudu suna daukan hoto dashi tare da basu takarda yayi musu signing saboda yawan mutane ko ice cream din ma basu shaba ya samu ya kubce ya shige mota, ita kam jawaheer dariya tai tayi yanda taga ya silale ya shige mota, kallonta yayi yace wannan dariyan fah? Tace babu komai kawai naji ina son yi ne hancinta yaja tare da fadin saina cire miki shi, dan kara ta saki tare da fadin akwai zafi fah, hararanta yayi tare da fadin ai na sani, baki ta turo, tuki yaci gaba dayi yana fadin mutum bashi da daman yin rayuwan da yake so sai mutane sun dameka, mtsww ya saki dan gajeran tsaki, jawaheer tace uhm toh ai mutane rahma ne, yace haka ne amma ai ba irin haka ba, sunyi tafiya mai nisa ta daiga bashi da niyan zuwa gida tace wai ina zamu? Yace zan sai daki ne, dariya ta saki tare da fadin tab lallai ma, cikin wani hotel suka isa, yace fito muje. Bata musa ba ta fito suka shiga wani daki suka shiga inda ya tsaya yana nocking, jim kadan aka bude dad dinshi ne hugging dinshi yayi tare da fadin dad yakake? Dad mai makon amsa sai kiran sunan jawaheer yayi da fadin shigo mana, shiga tayi cikin jin kunya ta sami waje ta zauna cikin kujeran dakin, hotel din ciki da falo ne, gashi ya hadu sosai, gaida dad tayi ya amsa cikin fara'a cikin jin kunya tace dad tun tuni nace ya kawo ni yace wai ka koma, wani irin kallo samir ya mata wanda yasa tayi saurin kasa dakai, dad kuma yace baka kyauta ba samir, shuru yayi ba tare da yace komai ba sunyi fira sosai dad dinshi yana son jawaheer sosai dan ya yaba da tarbiyanta da hankalinta uwa uba rainan bilkisu ce, dad din yace yaushe zaka spain din? Yace ran friday zan tafi inna gama kuma sai in tafi saudiya bazan dawo ba sai an daura auren daka nan sai mu koma spain din dan acan za muyi dinner, dad yace Allah ya taimaka an kawo card din ne? Yace eh an kawo dad yace ok nima idan aka daura auren zan tafi kwa sameni can, samir yace dad tare zamu tafi akwai private jet da za'a diba kowa mai cin mutane 120 dad yace ok ba damuwa, sai wajan karfe daya dad ya tashi shida samir dan zuwa masallaci, bayan sunyi sallah sun dawo suka tarar da ita tana sallah itama, bayan ta idar suka ma dad sallama suka tafi, suna tafiya cikin mota ya dan kalleta tare da fadin yaushe kika ce in kaiki wajan dad? Tace toh ai baka fadamin wajanshi zamu ba kuma ya kamata ka fadamin inyi mishi wani abu, tace yauwa mu ma bar wannan maganan tafiya za kayi shine baka fadamin ba, yace eh haka naga dama, shuru tayi ba tare data kara cemai komai ba, har suka karasa gida, a falo ta tarar da khalil da kabeer ozil da mum suna fira, tace ozil kai fa yanzu kayi wuyan gani, yayi dariya yace aikin dana samu akwai wuya wlh, tace sannu da gida mum, dai dai lokacin shima ya shigo falon zama yayi kusa da mum ozil ya fara tsokananshi da ango indai za'a ganka toh tare za'a ganku, dariya kawai yayi, kallon yanda yake da ido yasa jawaheer ta gane yana jin yunwa dan haka ta nufi dinning ta zubo mai abinci ta daura a plate ta daura a center table ta janyoshi gabanshi kallonta yayi yace thanks, sannan ya fara ci, mum kam tana jin dadin yanda suke nunawa juna kulawa sosai, khalil yace sis idan kun tafi ki siyomin phone a can naso muje tare amma banda time, jawaheer tace ok ka dauki excuse mana sai mu tafi, yace dad ai ba barina zaiyi ba wlh aikin nan akwai wuya shi bros umar ya huta wlh, dariya kabir yayi yace kalleka ai gwara naka aikin akan nawa, mum tace kun daiji jiki yara sai son jiki miye wahalan aikin zama ne fa a office ga ac sai signing shike nan fah, dariya jawaheer tayi tare da fadin mum wlh ni nama fi su dauriya, samir dai jinsu kawai yake yana cin abincinshi amma bini bini ya kalli jawaheer, ya rasa mai yasa ako da yaushe yake son ya kasance kusa da ita, jawaheer tashi tayi ta shiga kitchen ta hada ma dad abinci kalan na kasar su, dana nigeria kuma, mum ta shigo kitchen din tace baki za muyi yau kenan? Tace a'a mum za'a kaima dad ne, mum ta gane wanda take nufi dan haka tayi dariya ta fita, bayan ta kammala ita da kanta ta fita taje takai mai yana ta sa mata albarka, gida ta dawo ta shige dakinta, tana kwance taji nocking dan haka ta tashi ta bude, kallonta yayi daka sama har kasa ya dan cije baki, sannan ya shigo dakin binshi tayi a baya, zama yayi akan kujeran dakin mai dauke da hotanshi, yace nazo yin godiya ne, tace name? Yace dad yace kin kai mai abinci mai dadi, nagode, bata fuska tayi tare da fadin kaman ya ka gode nima fa dad dina ne, yaji dadin yanda tayi magana dan yana son dad dinshi yana kuma son mai sonshi, tashi yayi yazo kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinshi yace hakane sorry na tuba a daina fushi murmushi tayi tare da kokarin matsawa, janyota ya kuma yi tare da fadin haka za muyi sallama din kin san fah gobe zaki tafi in kin dawo kuma ba gani na za kiyi ba sai ranan biki, baki ta dan turo tare da fadin Allah ya taimaka, yace ameen tare da ja mata hanci ta saki kara mai dan sauti tace akwai zafi fah, yace dagaske? Daure fuska tayi alaman taji haushi yace idan kina fushi kinfi kyau, dariya tayi tace ba wani nan, shima dariyan yayi yace dagaske nake, jawaheer kina da kyau tako ina, murmushi tayi cikin jin dadin yabon da yake mata, duk da tasha jin ana fadin tana da kyau ita da kanta tasan ta hadu, amma idan taji a bakin samir tafi jin dadi, jin hannunshi tayi akanta yana shafawa ido ta lumshe, jin muryanshi tayi yana fadin saida safe tunda ba za'ayi min sallama ba, da sauri ta bude ido tare dayin hugging dinshi tace gashi nayi maka ko akwai wata sallama da tafi wannan? dariya yayi tare da girgiza kai yace bazan ce komai ba yanzu, itama dariyan tayi tare da kokarin jan jikinta daka nashi, tashi yayi ya mata peck a goshi yace sai da safe naji mum tace 10 zaku tashi zanyi kokari in tashi muyi sallama, tace ok fita yayi ta rufe kofarta ta kwanta tana tunanin irin kulawan da zata bashi in sunyi aure, har bacci yayi awon gaba da ita.

Tunda yayi sallah asuba bai koma ba, wajan 8 ya fito ya nufi dakinta yayi nocking ta bude kallonta yayi yaga tayi kyau tasa wata jallabiya pink, yace har kin shirya? Yace eh tare da fadin barka da safiya bai amsa ba sai jakar daya mika mata yace gashi saiki kara nasa an canza miki kudin dubai ne, tace wanda ka bani ya isa fah, fuska ya tamke yace bana son musu inna baki abu ki amsa kawai koda bakya so inna tafi saiki kai bola, amsa tayi tare da fadin kayi hakuri ba haka nake nufi ba, kafada ya daga alaman ke kika sani, yace in kin dawo zaki sami card a gida tace ok, tare da fadin nagode, kallonta yayi ji yake kaman yayi hugging dinta ko ya dan sami saukin abunda yake ji a halin yanzu, ganin inya ci gaba da kallonta komaj zai iya faruwa yasa yace in kun tashi tafiya saiki fadamin tace ok, falo ta nufa lokacin yayi dai dai da shigowan zarah da dan karamin akwatinta rungume juna sukayi sannan suka sami waje suka zauna, suna fira basu dade ba mum ta shigo falon gaidata sukayi tace saiku kai kayanku mota 10 zamu tashi kafin mu kai yayi, suka amsa da tam jawaheer itama ta shiga ta dauko kayanta tasa a mota sannan sukai breakfast, bayan sun gama ta kira samir tace zasu wuce falo ya fito ya gaida mum sukai sallama su mum suka fita jawaheer ce kadai a falon tace mun tafi janyota yayi yasa bakinshi cikin nata ya tsotsa na wajan second biyar sannan ya saketa tare da fadin ki kulan min da kanki, jiki a sanyaye ta fita dan ya kashe mata jiki, shima daki ya koma driver yaja su har airport suna zuwa suka shiga jirgi karfe goma dai dai suka daga zuwa kasar dubai siyayyan kayan akwati.
Chapter 35 · 0% Book details