Sashe 22
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Washe gari da safe jawaheer ta tashi da wuri, ita ta share tsakar gidan tare da hada kayan wanke wanke ta wanke su tas, adda ta fito tace jawaheer keda baki da lafiya inake ina aiki? Mai makon ta bata amsa saita gaidata da fadin ina kwana adda, murmushi adda tayi tace lfya ya karfin jikin naki? Tace alhmdlh naji sauki, adda tace haka akeso Allah ya kara mana lfya, tace ameen yar tsohuwa, dariya adda tayi tace aina fiki kyan jiki, jawaheer tace wa tab aida ban sami samari ba, adda tace ina samarin tunda kika zo banji anyi sallama ba, niko sanda ina budurwa zo kiga layi, jawaheer dariya take tayi tana fadin ba wani layi kakana kadai ke zuwa inna aureshi nasa ya sallameki dan kin mai tsufa, mum ce ta fito tana dariya tare da fadin ina kwana adda, adda ta amsa cikin fara'a tare da fadin kinga yar nema sauki ya samu zata damemu da surutu, mum dariya tayi dan harga Allah taji dadin yanda jawaheer ta sake yau har take ta fira, wanda rabonta data sake irin haka tunda tasan basu bane iyayenta amma yau gashi tana ta surutu, mum tace adda ina zan sami waina shi nake son ci yau, adda tace shine tun jiya baki magana ba aida anyi yau,kira abubakar ya siyo miki, tace toh daki ta koma ta dauko wayanta ta kira abubakar, sannan ta dawo tsakar gida inna adda da jawaheer keta kulla alale, suna fira, ita hannu tasa ta taya su, har suka gama jawaheer ta daura akan murhu, har alalan yayi suka faraci amma banda mum dan tana jiran waina, sallaman abubakar ne yasa su duka suka daga kai, amsawa sukayi sannan ya shigo ya ajiye cooler din tare da gaida adda, itama mum gaidashi tayi sannan itama jawaheer, bayan ya amsa yake tambayan jawaheer ina m samir bai zo bane? Tace eh bai zo ba uncle, murmushi yayi tare da fadin bari inje in shirya yau yace yawo zamu tare, mum tace yadai kamata shima yaga gari da irin al'adunsu, harya tashi zai fita ya dawi tare da tambayan ina mlm mahaifinsu kenan, adda tace yana bacci, yace mai gari jiya ya ganni yake tambaya na wai dagaske khausar ta dawo gari, nace mishi eh yace shine mlm bai fada mishi ba, nace toh nima ban san dalilin hakan ba nayi tafiya ta, mum tayi dan murmushin takaici tare da fadin naga kasar nan ta kowa ce kuma kowa zai iya zuwa inda yake so, koda can baya rashin sanin yanci nane yasa akamin haka, adda tace Allah dai ya kyauta suka amsa da ameen, sannan abubakar ya fita, jawaheer kam bayan ta tattare kayan da suka ci abinci ta wanke daki ta koma tayi kwanciyanta tare da tunanin m samir, haka taita zama a daki har wajan karfe daya ta fito tayi alwala ta koma tayi sallah, bayan ta idar taji mum na kiranta fita tayi tace mum gani, mum tace kije kici abinci mana, kin shige daki ko dai jikin ne? Tace a'a mum tashi tayi taje ta zuba abinci kadan ta zauna kusa da mum tana ci tana tunanin ina ma mum ce mamanta ta gaskiya da tafi kowa farin ciki, ajiye abincin tayi dan taji yana mata daci, mum tace badai wai har kin koshi ba? Tace eh mum bana jin yunwa sosai, shuru mum tayi dan tasan halin jawaheer ba'a matsa mata akan abu yanzu ta fara kuka, jawaheer damuwa ya mata yawa na rashin ganin m samir haka taita zama har yamma amma shuru bai leqo gidan ba, har mum da dad suka fita koda dad yazo yace ta bisu taki yarda ta bisu tace suje, tana zaune a falo adda ta zauna kusa da ita, duk tana lura da jawaheer tace jawaheer nikam wani irin so kikema wannan yaron haka? Jawaheer tayi dan murmushi tare da fadin adda niwa nake so? Adda tayi dariyan manya tace kaji ja'ira, bayan keda bakinki kin fada munji ko kin manta ne? Jawaheer tace kai ku tsofaffin nan bakwa mantuwa wlh, adda tace jawaheer naga kaman shi bawai yana sonki bane, irin yanda ke kike sonshi, amma zan baki shawara duk da nasan miye so ya kuma akeji dan nima auran so nayi duk da a lokacin ba'ayi, hada ku akeyi sai akaci sa'a muna son juna, ya kamata kibama wani namiji dama dan ya shiga cikin rayuwanki sannan ki nunama samir kema a matsayin dan uwa yake a wajanki yanda shima yake nunawa, ji jaraba wannan abun guda biyu idan kikayi zan kara miki wasu, jawaheer tayi dariya tace zan gwada yar tsohuwa suna zaune kam sai gashi wani yaro yayi sallama, wai ana kiran jawaheer, kallon juna sukayi ita da adda, sannan adda tace kaje kace tana zuwa, yaron ya fita jawaheer tace adda taya zani bayan ban san ko waye bane? Adda tace sai yasa nace kije ki gani, tashi tayi daka ita sai dogon wando da top amma yakai mata giwa sai wani dan shara sharan gyale ta yane kanta dashi, fita tayi taga wata mota kiran matrix tsayawa tayi sai taga an bude motar wannan dr din ta gani wanda ya dubata a asibiti, da murmushi akan fuskanshi yace bismillah ki shigo ciki mana, tace nan ma ya isa ai yace ba mutunci bane mu tsaya a waje...... Hasken mota ne ya hasko su, motocin m samir ne da security dinshi tun daka nesa ya hangosu suna tsaye, bayan motar ta tsaya ya fito zai wuce dr yace m samir tsayawa yayi tare da fadin dr ya aiki? Dr yace lfya tare da miga mai hannu suka gaisa hada ido sukayi da jawaheer wani irin kallo ya mata mai kama da harara, sannan ya shige ciki, dr yace shigo muyi magana, jiki a sanyaye ta shiga ciki,yace nazo inji ya jikin ki? Tace na warke nan ya fara mata surutai wanda gaba daya bama jinsa take ba, shiko m samir yana shiga yaga babu kowa sai adda ya gaidata da hausa tana ta mamaki tare sa fadin sai anjima kallo ta bishi dashi dan mamaki harya fice bata ce komai ba, koda ya fita yaga sun shige mota tsaki yayi tare da kawar da kanshi gefe ya shige mota akaja suka bar wajan.......
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 33-34
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 33-34