← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 45

Sashe 36

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwanan su jawaheer 7 a dubai suka dawo ba kayan akwati suka siya ba kawai harda kayan daki dan mum tace mata ya siya gida koda sunzo nigeria, akwati talatin da shida suka siya, ko wanne makil yake da kaya, atanfa materia english wear etc... Jawaheer tana kewan samir sosai gashi tunda suka tafi sau biyu sukai waya, taga katin bikin saura sati daya tayi mamaki ita ba kawaye gareta ba dan haka zarah ce taita rabo ta dai bama yan class dinsu, mum ta dauko mai gyara ta fara gyara mata yar tata, kun san farar mace babu wuya abu ya amsheta fatar jawaheer tayi laushi tayi silbi gwanin sha'awa har wani sheki takeyi da walkiya, ga kirjinta ya kara cika domin masu gyaran gaske mum ta dauko mata, anata hidiman biki ita jawaheer abunda yake damunta shine rashin wayan da basayi tunda sukayi a dubai yace mata shima yana spain zai raba kati, basu kara waya ba, gashi wayanshi baya shiga..... Yau za'ayi mothers day wanda mum ta shirya a wani haddan hall wanda saika amsa sunanka zaka iya kamashi manyan mata sun taru sosai masu hannu da shuni amarya saboda bala'in kyau dakyar na ganeta yan class dinsu sunyi mata kara sunzo matan dan event din na mata ne, sannan sunce zasu spain din harda mazan, anyi taron mothers day wanda mawaka daban daban suka baje basirar su, anci ansha kowa yaji dadi ga calender da aka raba wanda zarah ce ta hada musu cikin pics dinsu da jawaheer ta tura mata kwanaki sunyi kyau sosai mutane da dama sunyi mamaki da suka ga mijin nata suna ta fadin sun dace ashe dan kwallo ne kai ta sami mai mugun kudi, bayan sun koma gida saiga kiran samir da sauri ta tashi tayi toilet dan akwai kawayensu na class dinsu a dakinta dauka tayi cikin murya kaman zatai kuka tace hello, yace dear maiya sameki? Tace bakai bane kaki kirana ka kuma kashe waya, yace sorry dear jibi ina nan tafe uwar haka jibi kin zama tawa koh? Dariya tayi tare da fadin insha Allah ina ma auren soyayya mukayi kana so na kaman yanda nake sonka aida abun yayi armashi dariya yayi yace wani irin armashi? Tace mai zaka siyomin? Yace mai wayau kiban amsan tambaya na, dariya tayi danya gano ta tana son canza maganan ne, tace nima ban san amsa ba, yace zaki sani inna dawo bada wasa zan miki ba, dariya tayi tare da kashe wayan...... Jawaheer na gayyatar kowa da kowa daurin aurenta fans😀

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 51-52

Kiranta ya kuma yi dauka tayi yace naga pics kinyi kyau sosai, tace waya turo maka? Yace zarah nasa ta tura min pics din duk event din da akayi dariya tayi tare da fadin nasan banyi wani kyau ba zolaya na kake, yace uhm idan na dawo zan tabbatar miki da kyan da kikayi dariya ta kara saki tare da fadin sai anjima nabar mutane, yace mutanan sun fini ne? Tace a'a yace gud sai ki tsaya dan ban gama jin muryanki ba, tace uhm janta yayi da fira sosai sannan ya barta sukai sallama fita tayi zarah tace har an gama soyewan dan gulma waya shine a bayi, dariya tayi tare da fadin ehdin ina ruwanki ban san gulma, sauran sukai dariya tare da tashi suka mata sallama ita dama zarah yau tazo sai bayan biki zata koma, tare zasu kwana, raka su sukai har wajan gate akan sai sunzo gobe kamu, ciki suka koma jawaheer tace wai miye tsakaninki da khalil ne? Zarah tace mutunci jawaheer tace uhm in tayi wari maji, dariya zarah tayi suna cikin haka mum ta shigo dakin hannunta dauke da wani cup taba jawaheer tace ta shanye amsa tayi ta shanye sannan mum ta amshi cup din ta fita jim kadan sai ga kayan fruit an kawo musu, zarah ta amsa suka fara sha.

Yau za'ayi kamu tun karfe biyu aka farama jawaheer makeup ba'a gama ba sai wajan 5 danma tayi alwala kafin a fara saida tayi sallah kafin aka fita zuwa wajan kamu kwalliyan yau tafi ta jiya, a wajan taga adda dariya tayi domin taji dadin zuwanta haka aka sa lalle duk abunda akeyi zarah na daukan ma samir tare da videos anci ansha an kashe naira kaman ba gobe, harda mutanan da ba'a gayyata ba sunzo yau domin kawai ansan dan kwallon kafar da duniya takeyi dashi shine zai auri yar nigeria abun yaba ma mutane da dama mamaki amma duk wanda yaga amaryan sai yace eh gaskiya sun dace domin itama ba'a baya ba wajan kyau koda zarah ta tura ma samir hotuna ganin yanda tayi wani irin bala'in kyau abun ya bashi mamaki uwa uba yaga ta kara girma da cika, ji yake kaman yayi tsuntsu ya dawo gida amma ba hali sai gobe, ranan gani yayi lokaci baya mishi sauri burinshi kawai ya dawo yaga jawaheer dinshi, bayan an gama komai aka koma gida jawaheer dakin da adda ta sauka ta tare tace adda shine sai yau zaki zo? Adda tace ni rabu dani ja'ira sai inji shuru tunda kika tafi sai kawai naji ance wai zakuyi aure shin yaushe kuka fara soyayya ne haka har abun yayi karfi? Dariya tayi tare da fadin to ni ta ina zan fara bada amsa? Adda tace tako ina, labari taba adda yanda abubuwa suka kasance har da amincewan da yayi zai aureta, adda ta nisa tare da fadin hmmm samir kenan ni nasan yana sonki idanshi kawai za'a kalla a ga sonki a ciki, dariya jawaheer tayi tace uhm adda nidai banga komai ba, wai ni kam adda ina dr ne? Adda tace kwanki yazo gida na, nake fada mishi maganan aurenki ai, jawaheer tace eyya kwanaki ya kirani yace min zaizo bai zoba na kirashi lokacin wayanshi a kashe, adda tace kai mutumin nan yana sonki shima sosai Amma zabin Allah koda yaushe muke nema, jawaheer tace haka ne adda tah, adda tace ni karki samin ciwon jiki miko min jakata, tashi tayi ta dauko mata jakar tata, adda ta bude ta ciro wata leda, gora ne guda hudu, taba ma jawaheer gora daya tace gashi maza shanye, tace miye wannan kuma? Adda tace dallah shanye ban son surutu dariya tayi tare da fadin toh mutum zaisha abunda bai sani bane, tsaki adda tayi tace kyaji dashi, bude goran tayi ta kafa kai ta shanye, adda ta kara mata wani, duka gora uku ta shanye, ya rage saura daya adda tace wannan kuma gobe zan baki shi, tace toh yar tsohuwa, nan sukai ta fira tare da bata shawarar yanda zata biyar da mijinta....... Adda tace jawaheer aure ba abun wasa bane, ba abunda za kayi bane yanzu anjima kace bakayi, shi aure anayin shine har abada, dan haka ina mai baki shawara da kiji tsoran Allah ki riqe mijinki da hannu bibbiyu kiyi mishi biyayya yi nayi bari na bari domin aljannarki na karkashin kafarshi yin biyayya ga miji na kara mishi son matarshi, sannan duk inda kike ki zamto mai riqema mijinki mutuncinsa, zaisa mijinki ya yarda dake karki kuskura ki bashi hanyar da zai fara zarginki, domin zargi yana lalata aure, tayi ma jawaheer nasiha mai ratsa jiki inda daka karshe tace mata shi zaman aure hakuri ne gaba dayanshi kin san duk abunda akace bauta sai anyi hakuri, sun dade suna fira kafin ta tafi dakinsu taga zarah nata bacci abunta wayanta taga yana wuta da sauri ta duba taga 11 miscall sa sauri ta bude taga duka na samir ne, kiranshi tayi kashe wa yayi ya kirata da sauri ta dauka tambaya ya jefo mata da fadin ina kika shiga? Tace ina dakin adda, yace tazo ne? Tace eh dazu tazo shine naje muna ta fira, murmushi yayi tare da fadin shine kika manta dani koh dan kinga adda, tace ko daya kana raina koda yaushe kasan ni ce nake sonka kaga kenan bazan manta dakai ba, yaji dadin magananta sannan yace wani irin so kike min? Tace sonda nake maka bazai iya misaltuwa ba, amma ka bari a hankali zaka fahimta, ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin gobe ina nan tafe mai zaki tanadar min? Tace mai kake so? Yace ke kawai nake son gani dariya tayi tare da fadin saurin mai kakeyi? Yace nayi missing dinki sosai uhm kawai tace, murmushi yayi tare da fadin bari in barki sai na dawo goben, tace ok Allah ya kawo min kai lafiya ya amsa da fadin ameen, itama kwanciya tayi tana tunanin samir dinta yanzu gobe shikenan mun zama mata da miji.
Chapter 36 · 0% Book details