← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 45

Sashe 38

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mum din jawaheer ta kalli samir tace wani shirye shirye za kuyi kuma yanzu? Yace dinner ne amma a spain za ayi da yau kuma so mu wuce can ma dan dinner din gobe ne, nadia tace eh toh sai a shirya koh tunda kun tsara hakan, hakan ko akayi aka fara hadama jawaheer abubuwan bukatanta harda kawayenta aka akai airport cikin masu tafiyan harda adda😀 jawaheer ita da m samir suna mota daya driver na jansu, hannunta ya riqe tare da matsewa yace kin kara kyau da girma miye sirrin? Fisge hannunta tayi dariya yayi yace nayi laifi kenan? Kai ta girgiza alaman a'a, tace ban san da wani baki zan maka godiya ba, amma zan dan gwada nagode daka sadani da mum dina yau ya kasance min ranan farin ciki ranan da aka daura min aure kuma ranan daka kara min wani farin cikin nima Allah ya bani ikon faranta ma.... Toshe mata baki yayi da hannunshi sannan ya matsa kusa da ita yace yau nima zaki bani abunda nake so, tureshi tayi ya fara dariya ita kam ta rufe fuska har suka isa airport suka shiga jirgi, jirgi biyu ne aka basu dan mutanan sunyi ma jirgi daya kadan dan naga harda yan jawaheer fans group a tafiyan da yan hausa novels da yan maryam obam novels da sauransu...... Kowa ya shiga jirgi aka daga zuwa kasar spain duk yawan mutanan nan a hotel aka saukesu sannan ance suci komai kyauta duk abunda sukeso ga kudi da aka basu gaskiya sudai shar yan biki, ita kam jawaheer da mum, dinta da dad dasu adda gidansu na kasar suka sauka, jawaheer da mama take kiran mum dinta, jawaheer na makale da mamanta shiko samir gidanshi ya nufa yana shiga yaga sonia abun ya bashi mamaki hugging dinshi tayi tare da fadin congratulations na tayaka murna, abun ya bashi mamaki musamman da bata nuna komai ba akai, dakinshi ya nufa ya fada toilet dan yayi wanka bai dade ba ya fito yasa wasu kananan kaya sunyi mishi kyau sosai, ji yayi yana son jin muryan jawaheer dan haka ya dauki wayanshi ya doka mata kira, amma a kashe dan tsaki yayi tare da fadin bata sa sim dinta na nan ba, tashi yayi ya fito baiga sonia ba dan haka ya fice direct gidansu jawaheer din ya nufa inda ya samesu su duka a falo suna ta fira, shima zama yayi aka fara firan dashi, mama ta lura da jawaheer yake son gani dan haka ta kalleta tare da fadin jawaheer tashi ku dan zaga mana, tashi tayi shi kam dadi yaji, tashi yayi shima suka fita, wajan wata bishiya suka je a bayan gidan, zama sukai a kasa ya janyota jikinshi tare da fadin na rasa mai yasa bana son inga ina yin nesa dake, in nayi nesa dake sai in dinga jin wani iri, dariya tayi tare da fadin toh fah, toh mai yasa hakan ke faruwa? Yace shine nake so ki fadamin miye sirrin abun, hannunta ya riqo yana shafawa bata ce komai ba ganin haka yace jawaheer yau zan tafi dake koh? Da sauri ta dago tare da fadin dan Allah ka rufa min asiri, tamke fuska yayi yace kaman ya keba matata bace? Ina da iko inyi duk abunda naga dama dake babu wanda zaice min danme, tace hakane amma ai saika bari a kawo ni kaman yanda al'adanmu yake, yace ni bana son wani al'ada tunda ba addini bane, baki ta dan turo alaman taji haushi bata ankara ba taji bakinshi cikin nata, kissing dinta yake sosai tun bata mayar mishi da martani harta fara, sunyi wajan minti biyu suna tsotsan bakin junansu sannan ya saketa ta lumshe ido, ido ya zuba ma fuskanta yana kare mata kallo, lallai nayi dacen mata kyakyawa mai addini yar gidan mutunci, Allah na gode maka daka bani jawaheer a matsayin mata, gaba daya jikinta yayi weak bude idonta tayi taga ita yake kallo tayi sauri ta kuma rufewa dariya yayi tare da dagota daka jikinshi yace oya tashi muje yunwa nake ji, tace akwai abinci a ciki bari in kawo ma, yace nop muje akwai inda zamu ci, tace ok ina zuwa ciki ta shiga jim kadan sai gata ta fito ta canza kaya ido ya bita dashi komai jawaheer tasa yana amsanta, motarshi suka shiga shike tukawa har wani katon hotel ciki suka shiga, direct restaurant din hotel din suka nufa, masu abincin suka basu list na abincin suka nuna ba'a dade ba aka kawo musu, sunci sunsha sannan suka tashi wani daki taga ya bude gabanta taji ya fadi, amma haka ta daure ta shiga, bayan sun shiga kwanciya yayi akan gadon dakin tare da kallonta yace kunna min ac din, kunna mai tayi sannan ta sami waje ta zauna cikin kujeran dake dakin, kallonta yayi tare da bude mata hannunshi alaman tazo inda yake yi tayi kaman bata ganshi ba, ya lura da hakan yayi dan murmushi tare da tashi ya dauketa cak ta fara zillo amma ko a jikinshi kan gadon ya ajiye ta, tazo zata tashi ya janyota jikinshi tare da fadin muyi bacci, a hankali tace ni bana jin bacci, bai kulata ba sai kara manneta da yayi a jikinsa, bai dade ba bacci ya daukeshi yayi bacci sosai har wajan magrib tashi yayi tare da salati jin ana kiran sallah yasa ya tasheta da sauri tare da fadin tashi kiyi sallah, fita yayi ya nufi masallaci shima, koda ya dawo yaga ta ciro wani zanin gado ta yafa tayi sallah dashi, bayan ta gama yace su tafi, shiryawa tayi suka fita, bayan sun shiga mota yace mata gobe karfe hudu masu gyaraki za suzo, saiki zama ready suna tafiya yana mamin wakar da yasa na nicki minaj, har suka karasa kofar gidansu ya sauketa shima ya karasa nashi, koda ta shiga ta gansu a falo sai taji kunya amma sai basu nuna sun sam tana yiba, sai adda da tace sai yanzu bata ce komai ba ta sami waje ta zauna kusa da mum, tace mum gobe 4 masu makeup za suzo yace in shirya mum tace Allah ya kaimu, tashi tayi ta musu saida safe sannan ta wuce dakinta, tana sallah isha'i ta kwanta bacci.

Washegari tun da safe gidan ya kacame anata gyare gyare duk da ba taro za'ayi a gidan ba, lokaci kadan gidan yayi kyau ga kamshi na tashi tako ina, jawaheer sai wajan 10 ta fito adda ce ma take ta buga mata kofa sai yasa ma harta fito, bayan ta fito adda tace mutum ya kwanta yaita bacci har yanzu, tace kai adda bazaki bar mutum ya huta ba wlh, adda tace malalaciya ni ban taba ganin amarya mai son jikinki ba anya ma zaki dinga dafa mai abinci kuwa? Jawaheer tace haba girki sai kace zamaninku salati adda ta saki tace amma ko wannan zamanin naku ba abun arziki kuka koya ba, toh a ina zai dinga cin abincin? Tace wajan saidawa adda taita bala'i wai taya zata bae mijinta ya dinga cin abincin saidawa saboda lalaci, su mum kam babu abunda suke sai dariya, dinning ta nufa ta zuba abinci ta fara ci, sallamanshi taji idonshi na kanta ganin irin kallon da yake mata yasa ta sakar mai murmushi, adda data lura dasu tace mutum dai ya kalli gabanshi kar yaje ya fadi, shi kam ba hausa yake jiba, jawaheer kam ta gane dasu take, dan haka ta kawar da kanta daka kallonshi, taci gaba dacin abincinta, gaida su mum yayi da mama suka ansa sannan ya gaida adda da fadin ina kwana adda? Amsawa tayi da lafiya qalau, itama jawaheer gaidashi tayi da fadin morning, amsawa yayi ba tare daya kalleta ba, zama yayi kusa da mama yace ya kwanan kasar? Mama tace alhmdlh ya shirye shirye? Yace an gama komai babu abunda ya rage, tace toh alhmdlh Allah ya taimaka, ya amsa da ameen khlil da dad da muhd da kabir da umar ne suka shigo cikin gidan, gaisawa sukayi sannan suka zauna anata tattaunawa yanda abun zai kasance samir yace ya gama shirya komai karsu damu, jawaheer bayan ta gama cin abinci barin falon tayi ta nufi dakinta, kwanciya tayi dan bata koshi da baccin ba adda ta tashe ta, amma sai dai kuma me gaba daya ta kasa baccin sai tunani, yau itace a matsayin matar m samir, tashi tayi ta fito falon ta kalli samir tace plz ina aka sauke baki zarah na can tace tare da kawayenmu zasu zauna, gashi ina bukatarta a nan, yace zaku hadu ai daka wajansu nazo nan, na bada kayan da za susa ankai musu ma, tace ok tare da komawa ta zauna akan kujera kusa da adda, m samir tashi yayi ya wuce haka sukai ta fira.
Chapter 38 · 0% Book details