Sashe 15
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Muryan matan ne ya katse jawaheer daka duniyar tunanin data fada, tace sannunku ku karaso mana, wani karamin falo ta kaisu wanda daka gani an ware shine dan ajiye baki, falon sai kamshin turaren wuta yakeyi, jawaheer dai bin matar take tayi da ido, domin abubuwa ne fal a cikin ranta, fita tsohuwar tayi jim kadan sai gata da ruwa ta kawo musu, pure water mai sanyi, sannan ta zauna tare da fadin bismillah, m samir kallon jawaheer yayi wacce idonta nakan wannan tsohuwar,kafin yayi magana yaji matar na fadin sai dai ban shaida ku ba, cikin harshen hausa take magana, m samir bai san mai take fada ba dan haka ya kalli jawaheer tare da fadin tayi mata bayani, jawaheer tace da fatan mun sameki lfya hjy, amsawa tayi da fadin lfya qlau, sannan jawaheer tace dama mun zo neman khausar ne, da sauri matar ta tashi tare da kallon jawaheer lokaci daya kuma ta fashe da kuka tana fadin maiya kawo ku, waya turoku, mai kuka zoyi nan? Mai yasa zaku tunamin da ciwon da yake zuciya ta wanda ya kasa warkewa, kodai ku yan uwan muhd ne wanda ya bata min rayuwan yarinya, baxan taba yafe mai ba shine mutum na farko daya tarwatsa min a halina, ku tashi ku fita, m samir da bai san abunda ke faruwa ba sai kallon jawaheer yake amma yaga kaman matar fada take dan yanda take magana kadai ya isa ya nuna mishi hakan, jawaheer tace kiyi hakuri hjy wlh bada wata manufa muka zo miki ba, hasalima....... Dakata yar nan bana son jin duk wani abu da kuka zo dashi ku tafi kawai ku barni, jawaheer tace dan Allah ki saurare ni wannan da kike gani dan khausar ne kuma jikanki, gaba daya tsayawa tayi tana kallon jawaheer alaman ban san yaudara, kai jawaheer ta daga mata tare da fadin yaron muhd ne wannan a gabanki sai dai baya jin hausa, sai yaren kasar su spanish ko turanci, da sauri ta rungume m samir tana kuka tare da fadin ina kaje wajan shekaru ishirin da suka wuce a ina ka rayu, m samir farin ciki ne fal cikinsa tunda yaga ta rungumeshi alaman sunyi nasara kenan, kuma ya tabbata zaiga mum dinshi yanzu, sakin m samir tayi sannan ta kalli jawaheer tace yar nan fadamin a ina ya taso, nan jawaheer ta fara bata labarin abunda ya faru wanda dad din m samir din ya fada mishi da yanda abubuwa suka faru a baya tare da satoshi da yayi har ya girma a wajanshi, kuka ta kuma saki tare da fadin lallai muhd shine silan tarwatsa min dangina, amma babu komai munyi imani da kaddara wanda a wancan lokacin muka kasa fahimta, shigowan su mum gidan yasa jawaheer da tsohuwar suka fita shima m samir ya rufa musu baya, jawaheer tace mum dad mai kuka zoyi nan? Mum kam kuka takeyi yayin da matar itama take kuka tana fadin bilkisu dama kina raye, gaba daya jawaheer ta shiga rudani sosai dan haka ta matsa wajan dad dinta tana fadin dad maike faruwa ne? Dama sun san juna ne? Dad bai iya magana ba balle ya iya bata amsa, matar ta kamo hannun m samir ta hada dana hjy bilkisu tace ga danki nan bilkisu, jawaheer wani irin duhu ta gani ya rufe mata ido hannu ta daga tana fadin dama yaya nane kai jini nane kai mum dinmu daya ash..... Tif tayi kasa sumamma da sauri sukayi kanta suna fadin jawaheer musamman ma m samir da yafi kowa rudewa lokaci daya domin duk maganan da sukeyi babu abunda ya fahimta dan da hausa sukeyi sai dai ya gane mum itace mum dinshi, ruwa tsohuwar ta dibo ta fara yayyafa ma jawaheer amma ko motsi batayi ba, dan haka hankalinsu ya kuma tashi sosai dad ne yayi karfin halin fadin mu kaita hspt, jin an fadi hspt yasa m samir ya fahimta dan haka ya dauketa cak sukai mota ya shigar da ita yace ma security dinshi suje hspt mafi kusa, tafiya kadan sukayi suka isa wani asibiti inda akai emergency da ita domin ceto rayuwanta, mum babu abunda take sai kuka tare da fadin jawaheer insha Allan babu abunda zai sameki kuka take sosai gaba daya ta kasa zama, shiko m samir gaba daya ya rasa maike mishi dadi, ganin irin kukan da mum take yasa ya nufeta yana bata hakuri lokaci daya ta janyo m samir ta rungumeshi tana kuka mai cin rai, yau ya kamata ace ranan farin ciki ne a rayuwanta amma kash abubuwa sun jagule, ga danta Allah ya hadasu, ga jawaheer a asibiti rai a hannun Allah, sunyi wajan awa daya kafin dr ya fito da sauri m samir ya nufeshi yana tambayan ya jikin nata, yace suje office dinshi, binshi sukayi har office dr din sai kallon m samir yake yana mamaki kaman ya sanshi m samir ne ya katseshi da fadin dr ya jikin nata? Dr yace munyi iya kokarin mu sauran sai a barma Allah, dan harta farka tana fadin ashe yayana ne shikenan burina bazai cika ba, nono daya muka sha...... Tana cikin fadin haka ta kara suma ko numfashi baya fita amma yanzu mun sa mata oxygen numfashin ya fara fita, gaskiya tana cikin mugun damuwa wanda ba'a so mutum yakai irinshi domin sai anyi sa'an gaske mutum yake tashi idan yayi irin wannan abun, dayan biyu ne ko ka tashi da ciwon barin jiki ko kuma zuciyarka ta buga ka mutu, yanzu dai sai mu jira ta farka mu gani, hankalinsu gaba daya ya tashi m samir wani irin son jawaheer yaji yana shiganshi wanda bai taba jin irinshi ba sai a yanzu amma yana ganin hakan a matsayin dan tana kanwarsa ne jininsa wanda saida dr yayi bayani ya fahimta dan da turanci yayi, ashe duk son da take mai ashe yayanta ne shi lallai Allah mai iko ne, mai kuma yanda yaso, mum zuciyarta cike take da damuwa dad ma kam ba'a magana dan yafi kowa shiga cikin damuwa domin yar lelenshi wacce yafi so kaf yaranshi itace yau a kwance a gadon asibiti tana cikin yanayin rayuwa ko mutuwa gashi dr yace babu tabbaci, lokaci daya ya kalli mum yace anya ba zamu fitar da ita waje ba? Idan wani abu ya sami jawaheer bazan iya juran gani ba,mum tace nima haka nake tunani muyi magana da dr din. Koda aka fadama dr shawara ya basu akan suyi hakuri har zuwa gobe su gani sannan koda wajan suka kaita babu abunda zai canza, tare da fadin gwara ma suyi hakuri su barta a nan, dad yace bari dai suga zuwa goben tare da tambayan dr zasu iya ganinta? Yace eh su shiga amma karsu dameta da hayaniya, shiga sukayi dakin gaba dayansu, tana kwance akan gadon dakin ansa mata oxygen baka jin karan komai saina oxygen din da karan ac duk da ac a kunne yake jikinta babu abunda yake sai zufa, lokaci daya fuskanta yayi fayau tayi rama kaman wacce tayi ciwon kwana biyu bakinta yayi fari, mum ta kalli dad cikin kuka tana fadin kalli yanda ta koma yanzu2 anya jawaheer ba mutuwa za tayi ba, na shiga uku ni bilkisu....... Kuka yaci karfinta sosai dad ya jata suka fita m samir shima kukan yake tare da share mata zufan dake goshinta jikinta yayi wani irin dumi gashi kuma kaman babu jini yanda yaji jikin nata yayi wani irin tashin hankali ya kuma shiga tare da fadin wani irin ciwo ne haka lokaci daya?kallan fuskanta yayi yaga tayi haske tayi fayau gabanshi yaji ya fadi tare da fadin no zaki rayuwa my sister kuka ya saki sosai......
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 21-22
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 21-22