← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 45

Sashe 17

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu abunda nake sai kuka, bayan an gama daurin auren mai gari ya kalleni yace daka yau kar in kara shigowa wannan garin domin kar in lalata musu yara, haka muka tafi muka bar garin cikin dare, babu komai a raina sai tsanar garin da yan garin tare da mahaifina, haka muka shiga cikin garin yalo inda anan gidan mijina yake duk da bamai karfi bane sosai amma yana da rufin asiri yana da mota golf guda biyu daya ana mishi haya daya kuma shi yakeyi da kansa, yayi karatun boko rashin aikin yine yasa ya fara jan mota, iyayenshi sunyi mamakin auren da yayi amma da yake suna da tawakkali duk da abun ya bata musu rai ace yayi aure bada saninsu ba, haka suka hakura dan mamanshi ta dade da rasuwa wajan matar babanshi ya taso, suna nunamin gata sosai haka shima duk da yasan labari na, ina mamakin mai yasa ya yarda ya aureni, wata rana muna fira yake fadamin wai ya taba ganina ina tallan nono tun daka lokacin yaji yana sona, amma sanin al'adun mu na fulani yasa ya boye komai dan yasan kauyenmu kana jariri ake maka miji, sai kuma gashi yanzu kin zama matata, ina kokarin kyautata ma mijina, domin kaf duniya banda kamanshi dan ina ganin yafi kowa kaunata, shekara daya da aurenmu na haifi dana namiji santalele inda aka sa mishi sunan baban mijina wato umar, lokacin daya cika arba'in matar data riqe mijina ta rasu, munyi kuka sosai, tun bayan rasuwanta baba shima ya fara ciwo sosai, tsakaninsu wata uku shima ya rasu, kai munji mutuwar baba sosai, inda gaba daya zaman garin yalo ya ishemu dan dama ni bana son garin ina dai zama ne kawai, haka muka tattara muka koma kaduna muka sami gida muna haya, shekara biyu tsakani na kuma haifan da namiji muka sa mishi khalil, a lokacin mijina ya sami aiki a banki, lokaci kadan rayuwanmu ta fara canzawa, daka wajan aiki aka dawo dashi abuja inda aka bamu gida karami za'a dinga cirewa cikin kudin aikinshi, haka muketa rayuwa cikin kwanciyan hankali tunda na haifi khalil ban kuma samin ciki ba, abun yana damuna dan ina son samun yarinya mace, su umar har sun fara zuwa makaranta, wata rana munje anguwa nida mijina, motarmu tayi faci, nan ya fara kwance taya yana gyarawa ni kuma ina tsaye kusa dashi saiga wata mata tana ta gudu da alaman wasu ne suka biyota, tana zuwa wajanmu ta mika ma mijina kwali tana fadin dan Allah gashi akwai komai da komai a ciki ka ceci rayuwar yata daka fadawa halaka, tana fadin haka tabar wajan ta wuce da wajan minti biyar lokacin har mun shiga mota muna jimami tare da fargaban maita bamu, saiga wasu mutane da makamai sunzo sun wuce da gudu suna fadin miyi sauri karta bace mana, jin haka yasa muka gane kasheta suke son yi, haka muka karasa gida muka shiga da kwalin budewan da zamuyi muka ganki kina bacci abunki tare da magudan kudade dollars na amurka, mun tsora sosai wata takarda muka gani anyi rubutu kaman haka..... *salam ga duk wanda ya tsinci wannan yarinyar inaso ya riqemin ita amana wlh yar sunna ce bata hanyar zina aka sameta ba banda lokacin yin bayani sosai kar lokaci ya kure min, sunanta jawaheer duk wanda ya dauketa yayi amfani da wannan kudin na bashi halak malak, idan na rayu zan dawo neman yata wata rana in kuma sun kashe ni, shikenan* kallon juna muka fara nida mijina yace bazai dauki kudin ba zai kaiki wajan police dan yana tsoro ni nayi ta nuna mishi yayi hakuri mu taimakeki mu riqeki amanace mahaifiyarki ta bamu, da farko kaman taso ta ajiye kine sai Allah ya hadamu ta bamu, dakyar ya yarda lokacin da mukaje canzo kudin naira million dari ne kudin dai2 wlh munyi mugun firgita da yawan kudin, tun daka lokacin ya fara business da kudin yabar aikin banki rayuwa ya canza mana sosai, wlh jawaheer ina masifar sonki na dauki son duniya na daura miki haka mijina da nake ganin yafi kowa sonki domin yace tunda ya sameki Allah ya bude mishi kofofin arziki baya son ganin fushinki ko kadan munsha yin fada akanki nida shi, idan kikai abu na miki fada to in raina yayi dubu saiya baci sai yasa kika fi sabawa dashi dan yana yawan tafiya dake wlh ina takaicin fada miki bamu bane muka haifeki..... Kuka jawaheer take sosai lokaci daya ta fara fadin yanzu ba'asan inda iyayena suke ba, na shiga uku shikenan bani da wani gata a duniya mai yasa mum dina bata tafi dani ba, anya ma ta auren aka sameni kuwa kaman yanda ta rubut.... Mum ce ta toshe mata baki duk wanda ke wajan saida ya tausaya mata m samir shima hawaye yake amma bai bari sun gani ba dan da turanci mum ta fada mata komai, wani irin tausayin jawaheer yaji yana shiganshi sosai, shi gashi yaga mahaifiyarshi tare da taimakonta lallai shima ya zama hakki a kansa ya neman mata iyayenta, lokaci daya ya kalli mum yace mum babu wani shaida da za'a gane inda iyayenta suke? Mum tayi shuru can tace akwai international password da hotan mamanta a jiki, da sauri yace yana ina?? Mum tace yana gida abuja, yace mum plz mu koma yau can abuja din, mum tace dare yayi sai dai gobe, jawaheer kam bata komai sai kuka, adda itama fa fara rarrashinta tare da fadin yakamata tayi tawakkali insha Allah zaki ga iyayenki, dakyar jawaheer tayi shuru amma babu komai a ranta sai tarin bakin ciki da takaici yanzu basu dad banr iyayenta inta tuna hakan sai taji kaman tai ihu dan baki ciki, muryanta su mum sukaji tana fadin international password din wani kasa ne? Mum tace saudiya sannan ina tunanin itama yar can ne dan balarabiya ce ita, jawaheer bata kuma cewa komai ba, inda mum take tambayan adda ina mahaifinta adda tace hmmm labari mai tsawo amma bari in baki.......

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 25-26

Mum tace maiya faru adda?? Adda tace bayan kin tafi na bujire ma mahaifinki akan bazan yarda ba dole a dawo dake gida yace sai dai in biki in kuma na biki a bakin aurena, muna zaune aka kirashi mai gari, bai dawo ba sai can cikin dare yazo yana fadin an miki aure kuka nasa ina fadin haba mlm kai yanzu baka san kaddara ba? Wlh abunda ka aikata ko wanda baije islamiya ba bazai aikata ba, kaine limamin wannan garin mlm mai yasa bazaka dauki kaddara ba? Mai yasa zaka yanke wannan danyan hukuncin wlh mlm ka manta da nauyin dake kanka na amanar da Allah ya baka na yaranka, yanzu da kuka mata aure kasan wata aura?? Miye sana'an mijin?? Dan gidan mutunci ne?? Duk baka saniba, kai dai burinka tabar inda kake saboda kunyar data dauko mata wanda bai wuce ya fada kan kowa ba, mlm ina iliminka?? Da har zaka bari wai magan ganun mutane suyi tasiri akanka harka manta da kaddara bayan Allah yace muyi imani da kaddara khairan wa shairan, Kai ka sani ko wannan jarabawan da Allah ya maka inka jure shine silan shiganka aljanna, amma saika kasa jurewa....... Kuka mlm ya saki yana fadin kaico na kaico na lallai yau na yarda da manzon Allah yace gwara ka auri mace mai addini, yau gashi matata ta tunasar dani abunda na manta saboda kunyar duniya , yau idan Allah ya dauki rayuwa na mai zance mishi, lallai ban kyauta ma bilkisu ba, ban mata adalci ba, yanzu ina zan ganta?? Adda cikin kuka tace nasan ganinta zaiyi mana wuya amma ni burina ka gane ka kuma fahimta amma alhmdlh tunda ka gane, nasan ko mu dade ko mu juma wata rana zata dawo garemu insha Allah kawai mu tayata da addu'a duk inda take Allah ya kareta, abun ya mata yawa ga batan yaronta ga koranta da akayi kai wannan wani irin ibtila'i ne, mlm yace wlh koni inayi mata duk abunda nayi bada son raina ba, lallai nayi dana sani wanda bashi da amfani a yanzu Allah yasa mijin data aura ya riqemin ita da amana, adda tace ameen ,mlm yace zanyi ta bincike har in gano inda take, adda tace Allah yasa a dace, tun daka wannan ranan mlm yake ta tunaninki kullum burinshi ya ganki yaga wani hali kike ciki, abubakar yayi aure yana da yara biyu, maryam da abdullahi sunan yayanki aka samai suna kiranshi da hamman, shi kuma abdullahi ya sami aikin mota yana zuwa gari2 yayi hatsari ya rasu munji mutuwarshi sosai, abubakar yake mana komai na rayuwa duk da shima bawai yana da wani karfi bane, mahaifinku ya saida shanayenshi ya gyara gidan nan tare da fara sana'a a kasuwa yana saida su hatsi wanda shida abubakar suke zaune suke saidawa tunda babban shago ne, duk da mahaifinki ba wani lfya gareshi ba kullum burinshi ya ganki ko ya sami labarinki amma shuru har yanzu, kinji abunda ya faru bayan tafiyanki, amma bilkisu ban taba tunanin zaki rabu damu ba tsawon wannan lokaci, tace adda kiyi hakuri wlh ina son inzo duk da nasan har yanzu baba yana fushi dani, amma inna tuna shida kanshi ya koreni sai inji bana son zuwa amma kullum kuna raina kuma kuna cikin addu'a na koda yaushe, Allah sarki ya abdullahi lokaci yayi Allah yaji qanka ashe bazamu sake haduwa ba, adda ta kalli dady tace Allah ya biyaka yanda ka riqe min yarinya tsakani da Allah kaima Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, dady ya amsa da ameen.
Chapter 17 · 0% Book details