← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 45

Sashe 25

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonshi tayi da sauri tare da zare ido, hada ido sukayi yayi saurin kawar dakai tare da tamke fuska, dan murmushin takaici tayi tare da kokarin jan hannunta daka nashi amma ta kasa danya riqeta tam, ganin tana son ya saketa yasa ya kara janyota jikinshi ta fado kanshi, zama sukai akan gado ya kura mata ido na wani lokaci sannan yace miye tsakaninki da dr din nan?? Da sauri ta kalleshi, ganin babu wasa a tare dashi yasa tace babu komai, yace toh mai yazo yi wajanki? Tace yazo ya gaisheni ne kawai, kai ya daga alaman yaji, sannan ya tashi tare da fadin muje muci abinci sai a kaiki gida, da sauri ta tashi kallonta yayi tare da fadin saurin me kikeyi haka? Tace inaso ne inje gida na gaji, baice mata komai ba yayi gaba itama ta bishi, fadama security din inda zasu kaishi yayi, wajan wani hadaddan cin abinci suka nufa, bayan sun zauna a private waje ta kalleshi tace mai yasa baya cin abincin hotel din? Yace hakanan, masu kawo abincin ne suka zo suka tsaya suna jiran su fadi abunda suke so, kallonta yayi yace kalan abincin da kika ci rannan nake so, dariya tayi tace ma mai kawo abincin ya kawo tuwon semo, da farfesun kaza, ita kuma ya kawo mata rice nd stew da garden salad, tafiya yayi jim kadan saiga abincin ko wanne fara cin nashi yayi, ita kam ci take sosai dan sai yanzu ta tuna tun safe babu abunda taci suka fita, har suka gama ta tashi zasu fita ta riqe cikinta tare dayin yar kara, da sauri ya karasa wajanta tare da riqeta yana tambayanta lfya? Tace cikina ke murda min, cikin tashin hankali yace bari muje hspt, tace a'a zai daina bari in huta kad..... Bai gama sauraranta ba ya dagata cak ya fita da ita har mota yace suje hspt wani asibiti suka nufa, nan akai emergency da ita ganin yanda ya daukota yasa suka zata ko emergency ne, dr ne ya shigo dakin ya fara dubata, yace baki ci abinci da wuri ba da kika tashi ci kuma sai kika ci wani abun mai yakon ki fara shan tea, magani dr ya bata tasha, tana sha ko minti biyar batai ba cikin ya daina, sannan dr din ya sallamesu, suna mota ya kalleta yace ya cikin? Tace naji sauki sosai, ido ya kura mata can yace maganan tafiyan mu gobe saiki shirya dan da wuri zamu wuce, tace daka bari mun dan kara kwana biyu a nan, kuma banji mum tayi maganan tafiyan ba, yace dazu mukayi da ita so dan haka tace babu damuwa saiki shirya, shuru tayi ba tare data kara cewa komai ba, ita inda so samu ne ta zauna ta kara kwanaki a nan, suna karasawa kofar gida ta hango dr yana zaune akan motarshi yana danna wayanshi, m samir ya ganshi kallo daya ya mishi ya kawar dakai tare da kallonta yace sai yanzu nasan abunda yasa bakya son tafiya, nd kin dameni zaki tafi gida ashe shike jiranki, tace wlh ni ban san zai...... Shut up ya daka mata tsawa inma kin sani in baki sani ba wannan ba damuwa na bane, the only thing i hate shine karya, kince babu komai tsakaninku mai yazo yi yanzu??? Tace nima ban sani ba kuma bai cemin zaizo ba, yace bani phone dinki, mika mai tayi da sauri ya amsa ya duba yaga wayan a kashe, kallonta yayi tare da miqa mata wayan amma taki amsa ya ajiye mata a jiki tare da fadin mai yasa kika kashe wayan?? Tace hakanan kawai, yace ok tambaya na karshe miye tsakaninki da wancan dr din?? Tace babu komai yazo gaida nine ran nan, yace yanzu kuma mai yazo yi?? Tace nima ban sani ba, janyota yayi jikinshi tare da bude kofar gefenshi ya fito ita ya janyota ta fito ta kofar daya fita daura hannunshi yayi akan kafadanta tare da janyo dayan hannunta yana wasa dashi yajata suka fara tafiya, dr dake zaune m samir yace dr yakake? Dr ya dago yaga jawaheer maqale a jikin m samir nan idanshi ya canza launi dan tsabagen kishi, dakyar ya iya amsa ma m samir, sannan yaja jawaheer sukai ciki, dr kam wani irin takaici ne ya cika shi, suna shiga gidan ya saketa tare da tureta yayi ciki, binshi tayi da ido tana mamakin mai yasa yayi mata haka? Miye dan dr yazo wajanta, shiga itama tayi jiki a sanyaye ta samesu a falo har dashi, suna magana da mum ita kuma adda tana taba mlm labarin gidan, jawaheer gaidasu tayi bayan sun amsa adda tace dr yazo nemanki tun dazu, tace eh na ganshi, wani yaro ne ya shigo da kaya wai gashi a bama jawaheer inji dr, m samir jin an kira sunan jawaheer kuma ance dr ya gane sakon daka dr dinne, dan haka ya tashi da sauri ya amshi ledan, chocolate ne dasu biscuit tsaki yayi tare da bama yaron yace ya tafi dashi, yaron duk da baiji abunda yace ba ya gane ance yaje an bashi ne, mum tace ya zaka bashi bayan na jawaheer ne, yace mum kayan zaki ne kuma ita tana fama da ciwon ciki,so naga babu amfanin amsa, in kuma tana so sai in siya mata wasu, mum wani irin kallo tamai tare da fadin waya gaya maka cikinta na ciwo? Nan yaba mum labarin abunda ya faru da taci abinci, mum tace ai wannan ba komai bane kuma zata iya shan chocolate din, yanzu idan dr yaga yaron ya fito da kayan baziji dadi ba, yace mum wannan ba damuwan mu bane, ita kam jawaheer tana kwance akan cinyar adda ta daura akanta a kai, duk tana jin abunda suke fada tadai yi shuru ne, tana tunanin irin wannan sabon salon na samir, adda tace jawaheer abinci na kitchen fah, tace na koshi adda, mlm yace mai kika ci? Tace munci abinci kafin mu zo nan, nan mum ta basu labarin abunda ya faru da jawaheer cikin harshen hausa, nan suka fara mata sannu, shidai da ido yake ta kallonsu, dan baji yake ba amma ya dan fahimta ya gane mum ta fada musu abunda ya faru da jawaheer dinne, tashi tayi ta zauna tare da rungumo adda tace zanyi kewarki addata, banso tafiya gobe ba, adda tayi dariya tace nima haka idan aka tafi sai kuma yaushe? Ido suka hada da m samir ya sakar mata wani irin mugun kallo, tayi saurin kawar dakai tare da fadin bazan dade ba zan dawo adda ta, haka sukai ta fira daka sun hada ido dashi ya watsa mata mugun kallo, daka karshe dai tashi tayi ta shiga ciki, bata dade da shiga ba shima ya wuce, hada kayanta tayi tayi, lokaci kadan ta gama hada kayan sannan ta kwanta dan ta huta, tunawa tayi da wayanta dake kashe ta tashi ta dauko ta kunna tana kunnawa saqo ya shigo cikin wayan, budewa tayi dan taga dr ne ya mata saqon ga abunda yace nan *haba jawaheer keda nake daukanki mai hankali da nutsuwa mai yasa zaki biyema wannan farin fatan bayan kin san irin tamu tarbiyan ba irin tasu bace kalli yanda yake wani riqeki kaman wani maharraminki haba jawaheer, tunda na fara ganinki nake sonki kuma soyayyan aure nake miki bawai na wasa ba, inaso ki bani dama mu fahimci juna sannan iyaye su shiga ciki, ina fatan zaki amsa bukata ta ngd daka dr nazir* tana gama karantawa ta lumshe ido lallai dr nazir namiji ne da duk wata mace zatai burin samu a matsayin namiji sai dai ita kash m samir ya sace mata zuciyarta tare da ruhinta bata ganin kowa sai shi, ya kamata ta fadama dr nazir gaskiya.... Dan shuru tayi lokaci daya ta tashi ta fita mum ce kawai a falo, tace mum ina adda? Mum tace tana kitchen fita tayi ta nufi kitchen din inda ta sami adda na zuba dan wake a tukunya wanke hannu itama tayi tazo tana taya adda jefawa tare da fadin adda kina son danwake sosai, dariya adda tayi tace ai akwai dadi ne, jawaheer tace lallai nikam bai cika damuna ba, adda tace kin bar dadi, tace ya akayi keda mutumin naga kaman dazu yana ta miki mugun kallo sannan an aiko miki da kaya daka dr ya kyautar, nan jawaheer ta bata labarin abunda ya faru bata boye mata komai ba, adda tayi dan murmushi tace jawaheer kici gaba da kula dr tunda har yace yana sonki, tace adda shifa m samir din fa? Adda tace yace yana sonki ne?? Shuru jawaheer tayi adda tace kiban amsa mana, tace a'a bai ceba amma ina fatan yace min haka, adda tayi dan murmushi tare da fadin jawaheer ke yarinya ce har yanzu baki san mai duniya take ciki ba, kawai inason kiyi duk wani abu da nace miki indai kina son ki tabbatar da zaki sami m samir ko bazaki sameshi ba, kar ki zauna zaman jiranshi kiyi biyu babu, idan m samir yana sonki dole yayi kishin ki, inko baya sonki komai za kiyi babu ruwanshi, dan haka ji shigo da dr cikin rayuwanki sannan koda kun koma wani abu ya faru ki dinga fadamin tace toh adda ta, haka sukai ta jefa danwaken har adda ta tsame tasa musu suna fira suna ci.
Chapter 25 · 0% Book details