Sashe 37
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Rana dai bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji masu iya magana, yau take friday ranan daurin auren jawaheer da samir da misalin karfe daya da rabi aka daura auren akan sadaki naira dubu dari wanda dubbanun mutane suka shaida cikin daurin auren harda shugaban kasar spain da manyan yan kwallon kafa da abokan arzikin samir duk sunzo tare da masoyanshi shugaban kasar nigeria shine wakilin jawaheer, an daura aure mutane sun watse ana ta san barka, tunda aka daura auren aka fadama jawaheer wani irin faduwa taji gabanta nayi ga jikinta yayi mata wani irin nauyi ta rasa gane wani irin yanayi take ciki farin ciki take ko akasin hakan, tana zaune a dakin adda ta kwanta adda ta shigo tana fadin kinzo kin kwanta a nan ga mutane can anata tambayanki har samir dinma ya dawo ashe kina nan, bata motsa ba balle tayi magana, jin muryanshi tayi ya shigo dakin lumshe ido tayi yau itace rana ta farko da take jin kunyan hada ido dashi, kiran sunanta yayi da jawaheer tashi kiga kyautar da nace zan baki ranan daurin auren mu, kamar karta tashi amma ta tashi taga wata mata amma tasa nikaf da wani namiji kallo daya zaka masa kasan balarabe ne, namijin ya fara fadin Allahu akbar wlh wannan yarki ce nadia ga kaman ku nan sak, jawaheer kam ta shiga rudani, matar ta cire nikaf jawaheer bata san lokacin data saki ihu ba tare da nuna matar da hannu dan tabbas itace a wannan hotan na passport lokaci daya kuma tasa kuka tare da fadin dama kina raye shine baki taba nema naba? Matar ta matso kusa da ita tana kuka dai dai lokacin mum da dad suka shigo dad yace tabbas itace ta bamu jawaheer, matar tace jawaheer shekaru ishirin da biyu yanzu ina fama da ciwo wanda ba komai yaja min ba sai tunanin kina wani hali, a ina zan ganki na bata tsawon wannan lokacin da tunanin inda zan ganki iyayena sunce in cireki a raina dan sun san hala kin mutu amma naki yarda da hakan, sai gashi a yau tunani na ya zama gaskiya ta nuna m samir tace lallai jawaheer kinyi dacen miji shine ya sadani dake Allah yayi ma aurenku albarka, jawaheer cikin kuka tace mai yasa kika bayar dani mai yasa kika gujeni tun ina yar karama ta? Matar ta nisa sannan ta sauke ajiyan zuciya tace yanzu zan fada miki.....
TUNA BAYA.....
sunana nadia ahmad yar kasar saudiya iyayena mu biyu suka haifa nida yayana muhd, mun taso cikin gata da kulawa kasancewan mahaifina mai kudi ne shi sosai, ummi na tana ji dadi fiye da komai nata tun ina yar karamata ake fadamin inada kyau, tun banyi wayau ba nake da burin zama doctor sau tari in ummi ko abba na tambaya na mai zan zama sai ince doctor haka na taso da son zama dr har na gama secondary skul dina na fara jami'a inda na sami course din da nake so wato dr, zan karanci fannin zuciya hawan jini da suger, a lokacin maza da dama suna rubibina amma bana basu dama, domin karatu nasa a gaba, gashi iyayena duk abunda nace shi sukemin har yayana yayi aure amma ni ban taba tunanin yin aure ba harna kammala karatu na fita da first class gwamnatin saudiya ta bani aiki duk da dad dina yaso ya gina min asibiti na kaina nace a'a kasata zanma aiki, ana cikin haka wani dan uwan abba na yazo yace yana sona naki yarda abba na har yayi fushi tare da fadin ya kamata ace nayi aure, nace mishi zanyi amma ba yanzu ba, ana cikin haka shugaban kasar nigeria a lokacin yazo da mahaifinshi asibitin da nake aiki wanda a lokacin ciwon zuciya yake nice dr din da zan dubashi, cikin ikon Allah na fara dubashi yana samun lafiya, ashe president muktar kabir sona yake lokacin kasancewan mahaifin nashi ya dade a asibtin yasa muka saba dasu, harya samu sauki aka sallameshi bayan sun koma muna waya akai akai harya fito ya fadamin abunda ke ranshi a lokacin nima banyi musu ba na amince mukai ta soyayya har magana taje wajan iyayena inda suka nuna su sam bazan auri dan nigeria ba sai dai in auri dan kasata, haka naki yarda na bijire musu har abinci na daina ci na daina sha na rame sosai, ganin haka yasa sukace sun amince amma duk abunda ya biyo baya babu ruwansu, hakan yamin dadi ba tare da tunanin komai ba nace na amince, haka akayi bikin mu aka tawo dani nigeria muka sauka a villa, inda matarshi take mai suna hauwa, matarshi ta amsheni hannu bibbiyu hakan yamin dadi, saida mukai sati biyu muna amarci kafin ya koma kan kujeransa wanda yaba mataimakinsa na wucen gadi, mutane da dama suna ta bani kyauta dan inyi musj hanya wajan mijina, daka baya ya hana dan baya son kowa ya sanni, haka na daina fita amma ita uwar gidanshi kowa ya santa, haka muke zama dashi bai taba haiyuwa ba, ina zuwa kam na sami ciki, tun daka lokacin na fara ganin sauyi wajan kishiyata yayin da mijinmu ke murna, a lokacin ta fito da kishinta karara harda kanin mijinmu yake biye mata ita tana tsoran in haiyu in mijin mu ya mutu in fita gado tunda ita ance ba zata taba haiyuwa ba, shiko kanin mijinmu yna tsoron in haiyu a hanasu gado, hka suka tsangwameni, wata rana president yayi tafiya suai hatsari a jirgi babu wanda ya rayu, gashi a ranan na haiyu, a gida aiko inata wajan window din daki na naji hauwa da kanin mijinmu suna fdin suje su kashe abunda na haifa, babu shiri naje dakina na dauko kudade nasa da password dina nayi sauri nayi rubutu, na fita daka gidan ashe sun ganni suna ta bina shine na hadu da wa innan bayin Allah na basu ke da nufin koda sun kama ni, ni daya zasu kashe, amma Allah bai basu sa'a ba na tsere, dakyar na samu akamin password da wuri nabar kasar na koma saudiya wajan dangina, koda na fada musu abunda ya faru, abba ya fadama gwamnatin saudiya ta kwatar min yancina yanzu hauwa da kanin mahaifinki suna bursuna za suyi shekara hamsin da aiki mai tsanani tunda sunyi niyan kisan kai Allah bai basu dama ba, har yanzu ba'a raba gadon mahaifinki ba saboda baki dawo ba kuma hauwa na prison, nasha zuwa nigeria ko zan ganki amma babu wani labari sai shekaran jiya wannan bawan Allah yazo min da maganarki da farko ban yarda ba saida muka ga pics dinki ya kuma fadamin shine zai aureki, naji ddi sosai domin shiba karamin mutum bane sananne ne, kuma naji dabi'unsa masu kyau ne ta nuna mutumin da suka zo tare tace ga yayana , rungumeta jawaheer tayi tana kukan murna tare da kara godema Allah da aka haifeta ta hanyar aure nadia taita ma su dad godiya bayan an kimtsa dad ya dauko kudi yaba nadia yace ga kudin da kika bamu lokacin, kai ta girgiza tare da fadin dawainiyar da kukayi da jwheer banda abunda zan biyaku wannan kudin naku ne halak malak, dad yana ta mata godiya, samir kam sai kallon jawaheer yake yana bukatar su kebe amma taki tashi kuma ta lura da hakan.......
*maryam obam*
*JAWAHEER*
*STORY AND WRITEEN BY......*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*wattpad @maryam-obam*
*WWW.Maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*
Page 53-54