Sashe 41
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Gaba daya kowa dake falon yayi jigum, kowa jiran tashinsu yake, har wanda yabi mlm ya dawo ya basu abunda ya bashi ya kawo ya karayi musu bayani, adda tace a shafa musu mai din kafin su farka, hakan akayi aka shafe musu jiki dashi, sunyi a kalla wajan awa uku suna bacci, jawaheer ce ta fara farkawa tare dayin salati, ganin samir kusa da ita jikinshi duk jini yasa ta rude tare da fadin sunanshi da samir maiya sameka haka, su mum ne suka karaso inda take suka riqeta kuka take sosai tare da fadin mum maiya sameshi dan Allah kuce ya tashi, karan hayaniyarta ne yasa ya farka ido ya kura mata yanda take kuka bai san lokacin da yayi hugging dinta ba dukansu sauke ajiyan zuciya sukeyi, lokaci daya kuma suka saki juna suna murmushi gaba daya sai yanzu yaji ciwon jiki na damunshi na wurgin da yasha haka itama gaba daya jikinta ciwo yake, adda tace sai kuje kuyi wanka aje asibiti wannan ciwukan a baku magani tunda jini na zuba, taimaka mata yayi ta tashi mum ta amsheta tace mishi ina ne dakinta? Nuna mata yayi mum ta riqeta sukai ciki, bayan sun shiga shima yayi nashi dakin, mum ce ta tayata cire kayan jikinta sannan tace toh maza kije kiyi wankan shiga toilet din tayi bata dade ba ta fito fuskanta duk a jagule mum tace yadai? Ko jikin ne? Tace mum bazan iya wankan nan ba wlh nasa ruwa a jiki na kaman nasa garwashi zafi jiki na yake ni na rasa garin yama naji ciwon nan ba, mum tace toh kisa kaya muje haka, bude wardrobe din dakin mum tayi ta dauko mata riga da wando tare da after dress mum ta dauko turare ta feshe mata jiki dashi, sannan suka fito koda suka fita basu ga samir ba zama sukayi suna jiranshi, basu dade ba sai gashi ya fito cikin wani riga mai gajeran hannu na yan kwallo, da dogon wando, yayi kyau goshin shi dai ya fashe amma wankan da yayi yasa jinin ya dan rage zuba, fita sukayi su duka bayan sunje asibitin aka duba su aka basu magani, mum tace suje gidanta hakan akayi mum tace abar jawaheer a nan harta warke, samir bai so haka ba amma babu yanda ya iya dole ya hakura, mum ta bashi maganinshi tace ya dinga amfani dashi kullum ta mishi bayani sosai yanda zai dinga yi, amsa yayi sannan yace zashi gida yaje ya huta, fita yayi ya nufi gidan, dakinshi ya nufa ya shafe maganin a jikinsa sannan ya kwanta bai dade ba bacci yayi awon gaba dashi, itama haka ta gefen jawaheer bata dade ba bacci yayi awon gaba da ita.
Jawaheer na samun kulawa sosai wajan mum, ga zarah itama ta dawo gidan dan duk an tafi da yan bikin kowa ya koma sai zarah ce kadai ta rage wacce zasu koma tare dasu mum jibi, jawaheer na zaune a falo tana shan kankana da adda ta bata, samir ya shigo babu kowa a falon sai ita dan haka ya kura mata ido yanda take shan kankanan kaman ba zata shaba, ji tayi kaman ana kallonta ta dago dakai suka hada ido, murmushi ta saki shima mayar mata da martani yayi tare da nufanta ya zauna kusa da ita yace dear ina mutanan gidan? Tace suna ciki mama da mum kuma sun shiga kasuwa kai ya daga tare da fadin wai yaushe zasu bani matata ne? Dariya tayi tare da fadin tare dasu zan tafi nigeria tunda kasan har yanzu bawai na gama warkewa bane, wani irin kallo ya mata wanda ya sata yin dariya mai sauti,yace wasa ma kike yi, ni hakuri na ya kare kawai aban matata mu tafi yau tare,kamo mata hannu yayi yace ke bakya jin tausayina yanda nake kwana ni daya? Abun dariya ma ya bata sai kace sun saba kwana tare toh da dawa yake kwana, in banda fitina irin nashi miye na kosawa su koma gida shida bawai sonta yake ba kawai dai ya aureta ne, katse mata tunani yayi da fadin plz kice masu mum zaki bini yau, ido ta zaro tare da fadin rufamin asiri, yace ok to ni zan fada musu, dariya tayi tace uhm Allah ya taimaka, jan hancinta yayi tare da fadin tunda bakya so nima bazan yi magana ba suna cikin haka saiga su mum sun shigo tashi yayi daka kusa da jawaheer tare dajin kunyan yanda su mum suka gansu dan hannunshi nakan kafadanta, yi sukai kaman basu gani ba,gaida su mum sukayi bayan sun amsa mum tace mishi ya jikin yace da sauki, itama mama tambayarshi tayi ya amsa mata da jiki da sauki, mama tace jawaheer sai ki shirya kibi mijinki yau, mum tace mai makon ki bari ta kara warwarewa, mama tace a can ta warware ni banga amfanin zaman nata ba a nan tunda mu jibi zamu wuce, zarah ce ta fito mama tace yauwa zarah hada mata kayanta suzo su tafi gida, zarah ta amsa da toh tare da gaida samir sannan ta wuce ita kam jawaheer fuska ta tamke ya lura da hakan amma saiya basar sai sun tafi zaiji dalili, zarah bata dade ba ta gama hada mata kaya tare da adda suka fito tace ma jawaheer tazo, bayan sun shiga ta miqa mata gora tace oya shanye amsa tayi tana fadin ni ban cika son irin wannan abun ba wlh aita bama mutum tarkace, adda tace ke kika ga tarkace ni ban ganshi ba ja'ira, bayan ta shanye ta miqa ma adda goran, adda tace toh kardai a manta da addu'a sannan a riqe ibada sallah akan lokaci kuma banda wasa, tace insha Allah sannan ta fita, sallama tama su mum suka karayi mata nasiha sannan zarah ta rakata har mota bayan ta bude mata ta shiga sukai sallama yaja suka wuce.