← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 45

Sashe 14

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari tun karfe 7 jawaheer ta dan ta makara da sauri ta shiga toilet tayi alwala sannan tayi sallah tare da neman gafaran Allah, bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga, tare da hada sauran kayanta, tana gamawa kiran m samir ya shigo wayanta dauka tayi da sauri tana gaidashi amsawa yayi cikin murmushi tare da fadin zan turo a dauki kayanki 9 zamu wuce tace ok, basu dade da gama wayan ba taji nocking dan haka ta nufi kofan ta bude security dinshi ne suka shigo suka kwashe kayanta yayinda suka rufe komai na gidan da farin kyalle gudun kar kayan suyi kura tunda za'a bar gidan, bayan sun gama ta bisu suka tafi gidan m samir tare a falo ta ganshi shida dad dinshi cikin girmamawa ta gaida dad din nashi ya amsa cikin sakin fuska tare dayi musu addu'an samun nasara akan abunda zasu nema, fira suka farayi har 9 din yayi suka fito inda dad din m samir yake ta fadama jawaheer ta kula da m samir domin ya yarda da ita, tace insha Allah, da haka har suka nufi Airport, nan mutane suka fara ihu ganin m samir yayin daya rike jawaheer a makale dashi yan jarida nata dauka domin suna ganin budurwanshi ce duk yanda sukaso yace wani abu amma bai ceba koda suka zo shiga jirgi daukanta yayi ya daurawa sannan shima ya hau suka haura tana gaba yana binta a baya, daka shi sai security dinshi guda goma suka shiga jirgin aka rufe domin private jet ne, kusa da jawaheer ya zauna basu dade da zama ba masu aikin jirgin suka zo tambaya mai suke so, kallon jawaheer yayi yace ta fadi abunda take so, coffee tace kawai shima yace a kawo mai coffee din, kallon juna sukayi sukai murmushi wanda a dai2 lokacin jirgin ya daga domin zuwa nigeria....... Hmmmm ku biyoni dan jin yanda zata kaya ga m samir a nigeria

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 19

Sai wajan karfe biyu jirginsu ya sauka a airport dake yola, fita sukayi, suka fara tafiya yayin da security dinshi ke zagaye dashi, nan mutane suka ganeshi musamman matasa nan aka fara ihu tare da daukanshi hoto, yana ta daga musu hannu,haka har suka samu suka fita, motoci ne makil a waje sodoji ne da yan sanda suka zo daukansu da motoci na alfarma, tare suka shiga mota daya shida jawaheer, sannan security dinshi suka shiga sauran, hotel aka kaishi kai tsaye dan sun so su fara kaishi government house yace a'a su kaishi inda zai sauka yana son hutu, hotel din gaba daya aka mishi booking babu kowa a ciki sai su kadai an zagaye hotel din da jami'an tsaro, domin kuwa kasar spain ta bada ajiyan m samir ga gwamnatin nigeria, shugaban kasa da kansa yasa governor din yola yayi mishi komai da komai, jawaheer kam abun mamaki yake ta bata koda yake ba abun mamaki bane dan he is a biggest celebrity in d world wannan ba komai bane, sai da yakai jawaheer har dakin da zata sauka sannan shima ya shiga nashi mai kallon nata dakin, yana shiga ya fada toilet dan yin wanka, koda ya fito daka wanka, yasa boxer tare da daura jallabiya yayi sallah, koda ya idar cire jallabiyan yayi, kwantawa yayi dan ya huta, bai dade ba bacci ya daukeshi.

Ita ko jawaheer tunda ta shiga dakin take jinta wani iri na farko dai ba yunwa takeji ba dan taci abinci a jirgi, sannan ita ba rashin lafiya ba, gadai ta nan ne dai, wannan ne zuwanta yola na farko duk da ya kasance garin iyayenta ne shi, amma bata taba zuwa ba, sau da yawa takan rasa mai yasa iyayenta basa son koda firan garin yola ayi musu, musamman ma mum tafi tsanan mahaifar tata, lallai akwai wani abu amma kodai miye kiyayyar tayi yawa haka, dan murmushi tayi tare da fadin may be ma ba wani babban abu ya faru ba suka dauki karan tsana suka sama garin tare da watsar da danginsu gaba daya dama ance fulani nada riko, tashi tayi itama tayi toilet tayi wanka, sannan ta fito tasa kananan kaya riga da wando, tare dasa hijab dinta dan yin sallah azahar, bayan ta idar ta dauko wayanta tasa sim dinta na nigeria, kaman jira ake kiran mum dinta ya shigo wayan kin dauka tayi dan tasan indai ta dauka tasan tana yola sunanta sorry, amma da tayi tunanin rashin fadama mum din nata zai iya daga musu hankali suyi ta tunanin tana ina, dan haka kiran na tsinkewa ta tura ma mum message kamar haka..... *mum na dawo nigeria amma kiyi hakuri ina garin yola nida m samir muka zo, mum ki tayani da addu'a burina ya cika a kanshi duk da nasan kina min, tana gama rubutawa ta tura mata* koda saqon ya shiga wayan mum ihu ta saki tare da tafa hannu tana fadin lallai jawaheer yau ta wuce gonarta ta nunamin ban isa da ita ba, dad dake zaune kusa da ita yace haba bilkisu miye haka mai kuma ya faru? Kasa magana tayi sai miqa mai wayanta tayi amsa yayi shima ya karanta, salati yayi tayi tare da fadin mai yasa jawaheer zatai haka? Mum tace dole in tafi yola ina tsoran kar tarihi ya mai maita kansa, dad kallonta ya tsayayi tare da fadin koma dai miye kiyi mata addu'a sannan maganan zuwanki yola bai taso ba zanje da kaina in dauko ta, mum tace a'a tare zamu tafi, ganin yanda ta dage yasa dad fadin zasu tafi taren amma gobe da safe, mum badan taso ba dan taso su tafi yau din nan kar abunda take boyewa ya fito fili.

Washe gari tun karfe biyar su mum suka nufi airport dan mum ta matsa sosai,koda suka je airport din saida suka jira dan jirgin karfe 7 zai tashi, kallo daya zaka ma mum kasan tana cikin tashin hankali yau itace zata yola wanda a kalla shekara ishirin da wani abu da suka wuce rabonta da mahaifarta Wani irin hawaye mai zafi ne ya zubo mata a ido, shiga jirgi aka farayi suma suka tashi suka shiga, nan aka rufe jirgi ya daga zuwa garin yola.

Jawaheer tunda tayi sallah asuba, tayi wanka tasa wata doguwar riga gaba daya tun jiya bata cikin yanayi mai dadi, ta rasa dalili ga gabanta dake ta faman fadi, jin nocking tayi dan haka ta tashi jiki a sanyaye ta bude kofar murmushi ya sakar mata yayin data lumshe ido dan kamshin turarenshi ya bugan mata hanci wanda yake kara sa taji ya narkar mata da zuciya, wani irin kyau taga ya karayi yi mata sosai, duk da bawai wani canji yayi ba hasali ma riga da wando ne jikinsa kaman kullum kananan kaya, duka babu wanda yayi ma dan uwansa magana sai itace tayi karfin halin fadin morning, bai amsa ba sai hannunta daya kama sukai dakinshi tare, bayan sun shiga ya zaunar da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer maike damunki? Daga kai tayi ta kalleshi taga shima din ita yake kallo dan haka tayi saurin yin kasa dakai tare da fadin babu komai kawai.... Sai kuma tayi shuru, jin muryanshi tayi yana fadin kawai me? Tace gabana keta fadi ban taba jin irin yanayin da nakeji yau ba, murmushi yayi tare da fadin ki yawaita fadin innalillahi wa inna'ilaihira jiun, kai ta daga alaman toh sannan ya kalleta tare da fadin zamu anguwan da dad dina ya fadamin tunda bakya jin dadi ki zauna muje mu dawo, kai ta girgiza tare da tashi tace a'a tare zamu duk inda zaka a cikin kasar nan ina tare dakai,murmushi yayi tare da jan hancinta sannan yace kinyi breakfast? Kai ta girgiza alaman a'a wayan dake dakin ya kira ya fadi abunda yake bukata, bai wani dade ba aka kawo abunda yace, tea da chips nd egg aka kawo, tare sukaci sannan suka fita, motocin da aka kawo su jiya nan suka shiga inda jawaheer ta fada musu inda zasu tace guyuk in anje kuma ace gidan liman, kai tsaye driver din suka nufi hanya, hannun jawaheer na rike dana m samir yana kallon garin yanayin garin ya mishi kyau in yaga abu bai gane ba saiya tambayi jawaheer ta fada mishi, da haka har suka iso anguwan, babu laifi anguwan nada kyau, da tambaya har suka isa kofar gidan, koda suka isa jawaheer ce ta fito tace bari ta fara shiga, yace a'a tare zasu, haka suka shiga cikin gidan,babu laifi gidan yana da kyau duk da ba wani girma gareshi ba, sallama jawaheer tayi, wata yar dattijuwa ta amsa tace waye? Ku shigo, bayan sun shiga jawaheer taga tsohuwar fuskanta dauke da glass dam taji gabanta ya buga da karfi domin sak fuskan mum dinta sai dai kuma wannan tsohuwa ce ita ta girmi mum dinta sosai lokaci daya ta shiga rudani.......

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 20
Chapter 14 · 0% Book details