← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 45

Sashe 5

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe hudu dai2 mum ta nufi dakin jawaheer cikin shirinta ganin jawaheer tayi tana zaune tana kallon waya nufanta tayi tana fadin jawaheer kinyi sallah kuwa? Tace mum ina fashin sallah ai, mum tace ok toh maza ki tashi ki shirya zaki raka ni, tace mum kije kawai bana jin fita yau kaina na ciwo, mum tace haba jawaheer fitan nan danke zanyi fah, tace mum ina zamu? Mum tace kedai ki tashi ki shirya ban san dogon zance, bata fuska tayi tare da fadin wlh mum kaina ciwo yake dakin bari gobe mu fita ,mun tace kin san bana son shirme koh maza ki tashi kisa hijab muje, kallon mum tayi tace hijab kuma ina zamu haka? Kodai wani ne ya rasu? Mum tace babu wanda ya rasu kawai wajan da zamu ne bana bukatan ki bini saida hijab, badan taso ba ta shirya tare da saka hijab din, mota suka shiga mum tace jawaheer ta zauna a gaba, hjy hauwa zata zauna a baya ita da mum ,bayan sun shiga driver yaja gidan hjy hauwa suka biya suka dauketa sannan suka nufi islamiyyan, hjy hauwa tace driver yayi parking bayan ya tsaida motan suka fito amma banda jawaheer mum tace jawaheer ki fito mana bude motar tayi ta fito shiga islamiyyan sukayi inda aketa karatu wani office suka shiga suka zauna babu kowa a ciki jim kadan sai ga wani mutum yazo ba wani babba bane amma kana ganinshi kasan mlm ne dan irin shigan da yayi, gaisawa sukayi sannan hjy hauwa tace mlm ga kawata nan sannan ga yarinyar nan sai a sannan jawaheer ta dago ta kalli mlm din, mum tace mlm dan Allah a mata ruqiya domin aljanu ne nake tunanin suka shigeta, jawaheer da sauri ta kalli mum din nata ta fara hawaye tare da tashi tsaye......

*maryam obam*
[04/01, 14:50] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*
*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 6

Ta kalli mum tace mum mai hakan ke nufi? Mum kallon aljanu kike min kuka ta saki mai karfi tare da fadin mum nifa lafiya na qalau bani da komai kaman yanda kike tunani kallon mlm din tayi tace mlm ka kalleni dakyau nayi kama damai aljanu ko tabin hankali? Matsowa tayi kusa da mlm ya danyi baya kadan tare da fadin auzubillah karki matso kusa dani haram, mum ta tashi ta rikota tare da fadin zoki zauna jawaheer kwace jikinta tayi daka na mum tace mum bazan iya zama ba, amma inaso mlm ya cire miki zargin da kike min yanzu, kallon mlm tayi da yayi shuru yana kallon ikon Allah, tace mlm mai zaka min ka nuna ma mum dina ni lafiya na qalau, mlm yayi gyaran murya tare da fadin da farko dai ki zauna zanyi miki yan tambayoyi kadan, zama tayi akan kujera tare da kallon mlm tace inaji, mlm yace ya sunanki? Tace jawaheer, kai ya daga alaman yaji yace kina mafarkin ruwa ko wani yana saduwa dake kai ta girgiza alaman a'a, yaci gaba da tambaya kina mafarkin gaki a daji ko kuma ana binki tace a'a, nan dai yaita mata tambayoyi tana bashi amsa harya gama ya dauko wani magani ya bata yace tasha, bata musa ba ta amsa tasha bayan ta shanye tace mlm shikenan? Yace eh an gama, tace mlm bari kaji wani abu kasan miye matsalata? Shuru yayi ba tare da yace mata komai ba tace mlm Allah ya jarabceni dason wani mutum wanda badan nan kasar bane dan kwallon kafa ne nasan zaka iya saninshi sunanshi M samir, mlm a kullum inna kwanta ina ganinshi yana kuka tare da fadamin yana da wata matsala amma idan abun ya fito kar in gujeshi duk wuya in zauna dashi sannan yamin zai aureni duk wuya yace in daure ni tashi ce, ban taba fadama kowa wannan ba kullum sonshi na karuwa a raina duk da a kullum ina kokarin in cireshi a raina amma na kasa, abun kaman kara karuwa yakeyi kullum tun bana iya fadama iyayena harna fara fada musu abunda ke cikin raina dady dina ya fahimceni amma ita mum dina ta kasa itace mahaifiyata ita ya kamata tafi kowa fahimta na tasan wani hali nake ciki ya nake ji, amma mum ta kasa fahimta na saita fara min kallon aljanu da tabin hankali wanda hakan yana batamin rai mum dina tana nesa dani wanda hakan yasa nafi sabawa da dad dina akan mum dina shuru tayi domin kukan da yazo mata lokaci daya, wajan yayi shuru na wajan second biyar sannan taci gaba da fadin kiyi hakuri mum ina fadin hakane dan kisan abunda yake damuna, ban taba soyayya ba sai akan M samir duk da bai san inayi ba, sometimes nakan so incire abun a rai na har inyi kokarin sauraran wasu amma na kasa, tashi tayi tace mlm nasan kai zaka iya fahimta na wlh bana tare da wani cuta illa ciwon so wanda nasan idan ban sami abunda nake soba zai iya zama ajalina, nasha kallo a fina finai irin abubuwan da so yake haifar wa dariya nakeyi ko ince karya ko hauka, domin ina tunanin hakan bazai taba faruwa da gaske ba, ashe ba haka bane, yau gashi abunda nake ma dariya nake ganin karya ne gashi ya faru a kaina har nima ana min kallon mara hankali, ni nasan wannan yana cikin jarabawan rayuwa na, mlm pls make my mum to understand dat i dnt have any jin tana fadin haka ta fita, duka da ido suka bita mum kasa magana tayi mlm yace hjy yarinyarki bata da aljanu kaman yanda kike zargi sannan bana tunanin tana da tabin hankali lafiyanta qalau, kawai tsabar son mutumin nan ne yasa mata take haka which kuma abunda na fahimta kaman bata da kawaye wanda take fada musu matsalanta ku take fadama wa amma dad dinta yana fahimta har yake biye mata amma ke kina nuna mata kaman ta sami tabuwa, kuma ita a nata ganin kune ya kamata kusan wani hali take ciki tunda kune iyayenta, hjy ya kamata ki dinga janta a jiki kina bata shawar wari wanda zata fahimta koda tana firan dan ball din da takeso ki daina nuna mata kyara hakan yakan sa yaro ya tsani kanshi yaga kaman iyayenshi sun tsaneshi yana da kyau ka maida danka abokinka ta yanda zaku dinga bama juna shawara jan yaro a jiki yana sa komai zaiyi saiya fadama iyayenshi sannan nunama yaro kyara yana sa ya dinga boye abubuwa da yawa wanda in ba'ayi wasa ba nan gaba za'ayi dana sani wanda ba'a fata, jikin mum yayi sanyi tace ngd mlm tabbas hakane jawaheer bata da kawa ko daya na tabbata inda tana da kawa da tare zasu dinga shawara rashin kawar ne yasa take fada mana ni kuma sai inki fahimta in dinka mata kallon hauka, mlm kasan ba komai iyaye suke dauka ba amma yanzu da naji maganan ka na fahimci komai yaronka ya fada maka koda shirme ne ka nuna masa kulawa akai, nan suka ma mlm godiya tare da bashi kudi yaki amsa yace dan Allah yayi baya bukatan kudi saida mum tace babu kyau maida hannun kyauta sannan ya amsa suka wuce, a mota suka sami jawaheer tana ta kuka, mum cikin tausayin yar tata suka karasa motar bayan sun shiga mum tace jawaheer kiyi hakuri kibar wannan kukan batai shuru ba har suka sauke hjy hauwa suka wuce bayan sun shiga gida da sauri jawaheer ta shiga gida tana kuka a falo taga dad dinta nufanshi tayi tana sauke ajiyan zuciya, cikin damuwa yake tambayanta mai aka mata? Bata bashi amsa ba sai kukan da take tayi mum ce ta shigo falon ganin dad yace bilkisu mai aka mata haka? Kodai wannan magan ganun naki kike ta fada mata? Hjy bilkisu cikin damuwa tace kayi hakuri da abunda zan fada maka yanzu inaso kamin adalci sannan ka fahimce ni, wlh nayi hakan ne dan ina zargi amma daka baya saina fahimci kuskurena, munje wajan wani mlm ne a islamiya domin ina zargin aljanu jawaheer take dasu, dad yace what? mum tace kayi hakuri ka gama saurara na shuru yayi amma fuskanshi a tamke nan mum ta bashi labarin abunda ya faru, dad baice komai ba sai kama hannun jawaheer da yayi yace tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci sannan ki fara shiri jibi zamu tashi zuwa spain bata san lokacin data tashi ba dan murna lokaci daya kuma tace dad r u serious? murmushi yayi tare da fadin yes jawaheer bana daukan abunki da wasa komai naki inaso inyi miki yanda kike so hugging dad dinta tayi tare da furta u r d best dad in d world tana fadin haka ta nufi dakinta.

Kallon mum dad yayi yace bilkisu na rasa mai yasa gaba daya kika canza bakya jin duk maganan dana fada miki, yanxu kinji dai abunda mlm din yace Allah yasa ki dauka kiyi amfani dashi, tace kayi hakuri insha Allah komai ya wuce sannan wannan abunda ya sami jawaheer na jarabawa zan kara dagewa wajan roqan Allah akan ya zaba mata mafi alkhairi a rayuwa, yace yauwa ko kefa, dan murmushi tayi tare da fadin kasan ita daya ce yarinya ta mace duk wannan abunda kaga inayi duk sonta yaja hakan tunda babu mai so yaga nashi ya shiga wani hali, dad yace hakane sai muyi ta addu'a sannan tare na mana visa harda ke zamu tafi jibi da khalil mum tace tafiyan family ne kenan gaba daya dariya dad yayi yace mun dade bamuyi irin tafiyan nan ba gaba dayan mu, tunda muka dawo daka saudiya bamu kara fita mu duka ba naso muje harda umar babban dansu kenan, amma yace shima zaiyi tafiya, mum tace Allah ya taimaka, ya amsa da ameen...... Toh jawaheer za'a spain koya zata kaya???

*maryam obam*
[06/01, 01:05] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
Chapter 5 · 0% Book details