← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 45

Sashe 39

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wajan 5 masu makeup suka zo, saida tayi alwala kafin ta zauna aka fara mata, ana cikin makeup din aka kira sallah, saida tayi sallah akaci gaba, kwalliya ake mata na kece raini, wedding gown aka sa mata, jin kiran sallah isha'i yasa tace a cire mata abun kanta tayi sallah, haka suka cire tayi sannan suka kara gyara mata, wow fadin irin kyau din da tayi bata lokaci ne, bazai ma iya faduwa ba, bayan an gama aka rufe mata fuska suka fita cikin wata dangareriyan mota suka shiga da ita, a ciki ta sami samir shima yasha suit fari irin kayanta fari, kallonta yayi tare da fadin wow my princess kinyi kyau sosai, murmushi tayi ba tare da tace komai ba, driver yaja mota suka tafi bayan sun karasa dangareren hall din tare suka jera da kawayenta da suka sa black gown mazan ma haka har cikin hadaddan hall din, zama kowa yayi inda karan kida ke tashi masu rawa nayi, amarya da ango akace su fito su zo suyi rawa, hannu ya miqa mata ta miqa mai nata suka fara rawa gwanin sha'awa zarah taki yarda tayi rawa da kowa saboda khalil na wajan, bayan amarya da ango sun zauna nan aka fara basu gift suna amsa, cikin masu bada gift din harda sonia wacce taba zarah ta amsa tayi godiya, murmushi sonia tayi tare da komawa ta zauna, anci ansha gaba daya kayan aka kwashe akai mota dasu, yanda aka tsara daka dinner zai tafi da ita, ita bata ma san hakan aka tsara ba, saida aka gama suka shiga mota, wani dangareren gida suka nufa bayan mota ta faka yace ta fito fita tayi sukai ciki, gidan ya hadu sosai a falo suka tarar da gift din da aka basu, gaba daya anyi raping dinsu, gasu manya wanda sonia ta bata ta dauko shine karamin ciki, zata bude samir ya amsa ya fara budewa zobuna ne guda biyu masu shegen kyau ko wanne an rubuta S&J ma'ana samir da jawaheer kamo hannunta yayi yasa mata daya shima yasa nashi, tunda yasa mata ta zauna a kasa murmushi yayi tare da kokarin dagata amma tayi wani irin wurgi dashi wanda saida ya bugu da bangon dake kusa dashi, cikin tsoro da mamakin irin tureshi din da tayi ya fara kokarin tashi nufanshi tayi ta shake mai wuya tare da fadin yau zan kashe ka, lokaci daya kuma ta saki dariya tare da kara jefar dashi wannan karan akai ya bugu harda jini ya fara zuba, dariya ta saki mai karfi tare da sauti gashin kanta duk ya mimmike tsaye........ Toh fah muje zuwa

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 55-56
Chapter 39 · 0% Book details