← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 45

Sashe 6

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 7

Jawaheer shiri take sosai domin tafiya spain ko abinci bata iya samu taci dan murna sai dad yayi dagaske take ci, kaman yanda dad yace jibi zasu tafi hakan ta faru domin dai rana bata karya inji masu iya magana, yau jirginsu ya daga zuwa kasar spain.....

Su jawaheer an sauka a kasar spain tunda suka sauka ta lumshe ido tana jin wani irin nishadi tare da farin ciki sai take ganin kaman gata ga M samir nan, wata katuwar mota ce taxo ta daukesu da kayansu wani gida suka nufa gidan sama, bayan sun karasa gidan suka shiga komai na gidan an rufe da farin kyalle saboda kura cirewa sukayi suka zauna a kujeran falon, hjy bilkisu ta kalli mijin nata tace wannan gidan fah nadai san baka da gida a kasar nan, murmushi yayi tare da fadin saboda jawaheer na siya, munyi waya da ambassador akan ina son gida a kasar nan shine ya hadani da wani kin san shi yana asibiti, toh wannan gidan ma mutumin yace nayi sa'a harta yan kasar sun kasa siyan gidan dan yayi kudi da yawa, mum tace ah lallai kam ai dole dan gidan ya hadu gskya duk da banga ko ina ba, jawaheer ta tashi tare da fadin bari inga gidan khalil shima binta yayi nan sukai ta zagaya gidan wanda yasha kayan more rayuwa ga gidan kato a kalla dakuna sun kai bakwai a gidan, mum tace ma dad naga su turawa basa irin gida haka babba, yin katon gida sai balarawa, dad yace suma yanzu turawan sun fara, jawaheer ce ta fito daka wani daki tana fadin dad ni wannan ne dakina na riga na zaba, dad yace ok dear duk inda ya miki nan zaki dauka, khalil yace dad ya kamata a bata daki a kasa ne, kafin dad yayi magana ta amshe da fadin sai kace namiji zan zauna a kasa dad shi zai zauna a kasa ya dinga gadi yaga masu shiga da fita, khalil yace ni din zan zama mai gadin nufota yayi da nufin ya kamota ta fara gudu shima yana binta dad da mum dai dariya sukayi mum tace kuna jin karfin jikinku ne sai yasa kuke ta wannan gudun, saida suka gaji dan kansu suka zauna suna maida numfashi, dad waya yayi aka kawo musu abinci tare da masu aiki biyu turawa duk ta hanyar mutumin da ambassador ya hadasu dashi, saida suka huta sannan alhaji jibrin mai dala ya shirya dan zuwa duba ambassador a asibiti, harda su mum da jawaheer jawaheer tayi shigan riga da wando sai tasa boyfriend jacket akai mai tsawo tare da yafa karamin gyale a kanta ta nada shi kaman hijab, duk da batai makeup ba tayi kyau sosai, cikin wata sabuwar jeep suka shiga nan driver yaja su suka nufi hspt din, kafin su shiga dakin da ambassador yake saida aka basu wani kaya suka daura akan nasu domin haka ka'idan asibitin yake, bayan sun shiga suka sami ambassador yana jin jiki duk da yana dauriya amma kana kallonshi kasan ciwo nacin shi, alhaji jibrin mai dala yace sannu ambassador ya jikin ya amsa da fadin da sauki alhmdlh, nan suma su jawaheer suka gaidashi ya amsa da fadin jikin alhamdlh, alh jibrin yace dama haka kake jin jiki? Ambassador yace ai jiki yayi sauki ma sosai akan da, cikin tausayi alh jibrin yake kara fadin Allah ya kara ma lfya, ambassador yace ameen, amma lfya kuwa PA dina yace kana ta kira cikin damuwa? Alh jibrin yace ah a ka barshi kawai inka warke mayi magana, ambassador yace haba haba ka fadi mana kai ka sani koh zan tashi, alh jibrin yace zaka tashi mana insha Allah, dama akan maganan dan kwallon kafa din nanne M samir wlh kaga yarinya ta ga tanan ya nuna jawaheer wacce tayi tsuru tana sauraransu, ita take son ganinshi, ta hanamu sukuni, ambassador yayi shuru yana ji har alhji jibrin ya gama sannan ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin babban magana, alh jibrin yace kaman ya? Ambassador yace gsky ganin M samir yana da matukar wuya kaman a nigeria ne talaka yace yana son ganin shugaban kasa kaga hakan bamai yuhuwa bane a garesa, inaga kaman ma wannan zaifi sauki, domin M samir yana daya daka cikin matasa masu kudin duniya ganinshi zaiyi matukar wuya dama wani ne daka cikin yan kwallon dana hadasu, sai dai ta ganshi in za suyi wasa a cikin fili, jawaheer fita tayi da sauri tana kuka tare da fadin shikenan bazata sami ganin M samir ba shikenan burinta da mafarkinta zai zama karya kenan mota ta shiga ta zauna tana ta rusgan kuka driver din da aka hadasu yana ta kallonta ta mirror cikin tausayi, gashi babu daman ya tambayeta ko lfya,

Haka su dad suka shigo motar suka sameta tana ta rusgan kuka, nan dad ya fara aikin rarrashi amma kaman kara zugata yake dan haka ya barta in sunje gida ya rarrasheta dakyau, koda suka isa gida fita tayi tana kukan dukansu suna tausaya mata musamman dad, zata wuce daki khalil ya rikota yana fadin haba lil sis mai yasa zaki sa kanki cikin damuwa haka? Cikin kuka tace bakaji abunda ambassador yace ba tunda ambassador bazai iya hadani dashi ba bana tunanin zan iya ganinshi tako wani hanya, shikenan komai nawa ya tsaya, bazan sami cikan burina ba bros ina son M samir a kullum da burin ganinshi nake kwana nake tashi indai ganinshi zaiyi wuya har haka kenan mafarki na ya zama karya..... Kasa tayi tana kuka cikin tausayi dad ya matso kusa da ita yace jawaheer kiyi hakuri insha Allah na miki alkawarin ganinshi tako wace hanya, kai ta girgiza tare da fadin dad baka ji abunda ambassador yace ba gwara in koma nigeria in nemi ganin shugaban qasa zaifi min sauki akan ince ina son ganin M samir, dad bana tunanin zanyi tsawon rai domin duka tunani na da jini na yana tafiya da M samir a kullum, zuciyata tana bugawa da tunaninshi dad in har ganinshi zai zama wahala a gareni miye amfanin rayuwa na? Ganin kowa yayi shuru yana kallonta yasa ta danyi murmushi wanda ake cewa yafi kuka ciwo tace dad nasan kuna min kallon rashin hankali ko wani abu makamancin haka, nasan koda kai bakamin mum tana min, amma abunda nake son ku fahimta shifa so ba karya bane wlh da ana cire abu a rai da tun tuni na cire shi na huta amma Allah ne yasa min sonshi wanda nasan shine kaddarata Allah yamin komai na rayuwa ban rasa komai ba komai nake so ina samu amma abu daya ya gagareni samu shine farin ciki na wato M samir, na yarda Allah baya bama bawa komai dole saiya jarabceka, wasu Allah kan basu dukiya da komai sai ya hanasu haiyuwa wasu kuma sai suzo a talaka abinci ma dakyar suke samu amma sai Allah ya azurtasu da haiyuwa lallai babu yanda Allah bayayi lumshe ido tayi wanda ya kada yayi ja, tace dad bana son zama a kasar nan inaso mubar nan da gaggawa nasan bazan iya cire M samir ba amma zan koma kasata inje inyi ta jinyar zuciyata har lokacin mutuwa na yayi...... Hmmm muje zuwa

*maryam obam*
[08/01, 17:32] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 8

Shuru tayi tana kuka.. Mum ta matso kusa da ita tare da rungumota tace kiyi hakuri jawaheer tun farko abunda nake so ki fahimta kenan amma yanzu alhmdlh tunda kin fahimta, ba komai bawa yake soba yake samu a rayuwa duk kudinka duk gatanka akwai abunda yafi karfinka, sannan Allah yakan jarabci bayinsa ta hanya da dama idan kayi hakuri sai ya zama hala silan shiga aljannanka, nasan abunda kikeji jawaheer amma inaso kiyi tawakkali kiyi kokarin cire M samir da tunaninshi a ranki duk da nasan ba abu mai sauki bane gareki, amma ki gwada kiba wani chance ya shigo rayuwanki zaki rage duk tunanin M samir,...... Murmushi tayi wanda ake cema yafi kuka ciwo tace mum bana tunanin zan iya hakan domin son M samir a jini na yake bana tunanin zan daina sonshi har sai ranan dana daina numfashi.... Mum tace jawaheer ki gwada bama wani dama zaki manta dashi ...... Tace shikenan mum zan gwada tana fadin haka tayi dakinta ta kwanta tana kuka.

Dad ya kalli mum tare da fadin miye mafita? Mum tace mafita daya shine mu koma nigeria ka zaba mata wani ta aura zata cire duk son wannan mutumin da nasan bazai taba auranta ba, dad shuru yayi can ya nisa yace Allah kasa mu dace, duka suka amsa da ameen khalil shima dakinshi ya shige haka su mum.

Jawaheer tunda ta shiga daki take kuka har bacci ya dauketa,cikin baccin ne tayi mafarki...... Gata da M samir cikin wani garden wanda an saka kujeru da shape din heart kallonta yake tayi yana mata murmushi lokaci daya kuma ya tamke yace mai yasa kinzo kusa dani kike son ki kara yin nesa dani? Ko kin daina so nane? Tana kokarin yi mishi magana ya tashi cikin fushi yayi gaba tashi tayi tana binshi da sauri tana kokarin ta bashi hakuri amma yayi mata nisa, farkawa tayi duk tayi zufa sai faman sauke ajiyan zuciya take lokaci daya kuma tasa kuka tare da fadin bazan tafi ba bazan bar kasar nan ba har sai na ganka kaman yanda kake bukata cikin kuka take fadin Allah ka nuna min M samir da gaggawa Allah ka tausayamin badan halina ba, Allah kasan ina son wannan bawan naka tsakani da Allah, Allah ka tausayamin koda bazai aureni ba Allah ka nunamin shi a zahiri kuka ta kara saki mai karfi.
Chapter 6 · 0% Book details