← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 45

Sashe 7

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan su jawaheer biyar a spain bata fita ko ina, kullum tana gida tana kuka tare da roqan Allah ya nuna mata M samir in alkhairi ne a rayuwanta dad yace su shirya jibi zasu tafi dama sati daya za suyi, jawaheer tace dad babu inda zani, dad yace kaman ya? Tace dad sai naga M samir zan bar kasar nan, mum ji tayi kaman an daba mata wuka dan takaici cikin damuwa tace haba jawaheer kece fa kika ce mubar kasar nan sai yasa mukace sati daya kawai za muyi dan Allah kiyi hakuri kizo mu koma zamanki a nan baida wani fa'ida domin babu abunda zai kara miki inba takaici da bakin ciki ba, jawaheer ki taimaki rayuwanki tare da namu kibar wannan mutumin munfi kowa kaunarki ke bakya tunanin halinda muke shiga idan muka ganki cikin damuwa haba jawaheer ko so kike ki kashe mu da naki damuwan? Kuka jawaheer ta fara tare da fadin kiyi hakuri mum nima bada son raina nake haka ba, wlh mum zuciya tane take sani aikata duk wannan abun nasan kuna sona fiye da tunani na sai yasa kuke hakuri da duk wani abun dana kawo kuke dauka mum kodan farin cikin ku zanyi kokari in manta da komai amma dan Allah ku tafi ku barni a nan na wata daya nayi alkawarin in banga M samir ba wlh zan dawo sannan inaso inna dawo ku bani auren duk namijin da kuka zaba min, zan rungumi kaddarata nayi alkawari mum, wani guntun hawaye ne ya silalo a fuskan mum na tausayin yar tata inama tana da hanyar ganin M samir dayau saita sada yarta dashi kodan tayi farin ciki lokaci daya kuma ta rungumeta tana shafa mata baya tare da fadin kiyi hakuri jawaheer ni mahaifiyarki ce bana son ganin damuwanki duk kankantansa sai yasa wani lokacin nake miki abu wani iri amma badan bana kaunarki bane a'ah duk saboda kar kisa kanki cikin damuwa bana so ki zauna a kasar nan ke daya, jawaheer ke mace ce kuma kina da rauni bawai ban yarda dake bane a'a tarbiya ya zama abunda ya zama sai yasa naki yarda ki fita karatu waje nace ki zauna a abuja kiyi inkin gama ki dawo gida, dan Allah jawaheer kiji tausayina ki bimu jibi mu koma tare badan niba, cikin kuka tace mum baki taba tambayana abu na kasayi miki shiba a rayuwa ko inyi miki musu, amma wannan karan kiyi hakuri mun bazan biku ba M samir ya fadamin kar inyi nesa dashi in zauna..... Mum salati tayi cikin kuka tace a ina kika hadu dashi harya fada miki hakan? Tace cikin mafarki na mum yayi fushi dani saboda nace zan bar kasar nan, mum tace jawaheer anya lafiyanki qalau kuwa? Yanzu ke mafarkin ne kike yarda dashi? Murmushi jawaheer tayi tare da fadin mum nasan mafarki ba gaskiya bane amma akwai wanda yake zama gaskiya wannan mafarkin da nayi inaji a jikina gaskiya ne shima yana jin wani abu a tare dani, cikin takaici mum tace dan Allah tashi ki bani waje sannan wlh jibi dake zamu tafi kinji na rantse dakinta ta nufa tana kuka.

Wata baturiya ce ta fito daka cikin jirgi kallo daya zaka mata ka gane tana da kyau sosai bata da tsawo sosai tasa riga da wando fuskanta tasa glass kanta tasa brown attachment jan dan karamin akwatinta take har wajan da taga wani ya rike abu mai sunanta SONIA alaman ita yazo dauka cikin harshen turanci tace mishi hi am sonia yace mata ok nan suka nufi inda aka faka mota ya bude mata ta shiga direct asibiti suka nufa, wani daki ya nuna mata ta shiga tana budewa taga M samir a ciki yana zaune shi daya yana duba wayanshi da sauri ta nufeshi tayi hugging dinshi tare da fadin nayi missing dinka ya jikinka, lolaci daya kuma tasa kuka dagota yayi yaja mata hanci tare da fadin bana son kukanki naji sauki dana ganki saina kara samun lfya so stop crying kin san bana san ganinki cikin damuwa dan murmushi tayi tare dasa bakinta cikin nashi tayi kissing dinshi na wajan minti daya sannan ta sakeshi tace i really miss u murmushi yayi tare da fadin i miss u too inga tunda kin zo zan koma gida saiki dinga kula dani kai ta girgiza tare da fadin babu inda zaka sai abunda dr yace cikin dariya yace i luv you so much baby u r my happiness, manneshi tayi a jikinshi dad dinshi ne ya shigo dakin kallo daya ya musu yaji tsanar yarinyar .......

No editing kuyi hakuri da typing error😀

*maryam obam*
[09/01, 21:41] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 9

Sonia tana ganin dad din M samir ta ganeshi dan ta sanshi a hoto, mika mai hannu tayi shima bata yayi sannan tace hi am sonia from england am samir girl i know dat he told u about me but iz good to introduce by my self, dad din tsayawa yayi yana kallonta duk da bawai ya dauki hakan da wani abu bane dan turawa ne su sun saba ganin fiye da haka amma shi mahaifin m samir musulmi ne kuma yana kishin addininsa sai yasa baya sha'awan ya auri wacce ba musulma ba, abun takaici ma ita wannan gata ba musulma ba kuma yar kasar england dad din fita yayi tare da fadin ni na tafi sai zuwa anjima, dad bai dade da fita ba dr ya shigo ya duba shi m samir yace yana son tafiya gida dr yace ya bari gobe sai ya tafi gidan dan yau za'a cire mai abunda aka samai a kafa, kai ya daga alaman ok, bayan fitan dr sonia ta kalli m samir tace mai yake damun dad dinka ko bashi da lafiya ne? Yace maita gani? Dan murmushi tayi tare da fadin naga ina mishi magana ya daure fuska kaman baya so na? M samir dariya yayi yace ba haka bane dad yana da sauki a hankali zaki fahimci haka, kallonshi tayi tace badai a gidanku zamu zauna ba koh? Yace mata a nan zamu zauna kina da matsala da haka ne? Tace eh bazan iya zama gida daya da dad dinka ba, dan shuru yayi yana nazarin magananta tare da tunanin abunyi.... Katseshi tayi da fadin in kuma baka da wajan sani zan tafi hotel, murmushi yayi tare da fadin no ba zaki hotel ba kece fa matar da zan aura komai kike so dole inyi miki akwai gidana sai muje can ki dinga kula dani har in gama warkewa, kai ta daga mishi alaman gamsuwa sannan suka canza firan da maganan yanda zasu tsara auransu in sun tashi yi.

Jawaheer gaba daya duniya ta mata zafi, maganan mum take ta tunawa da tace dole tare zasu koma, gashi dad dinta yana ji baice komai ba, dan tsaki tayi lokaci daya kuma ta tashi tayi toilet wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar riga english wear tare da yafa karamin gyalen kayan, duk da batai makeup ba tayi kyau sosai idonta yayi zuru2 alaman tana cikin damuwa, falo ta fito taga mum a zaune ita da khalil, tace mum zan fita in dawo, mum cikin jin dadi tace ko kefa jawaheer ai gwara ki saki ranki dan murmushi tayi khalil yace muje tare nima inga gari ita da khalil suka fita a kafa har sukaje wani katon super market gaba daya rigunan da m samir yake sawa ta dinga jida da duk wani abu da akwai pic dinshi a jiki, tare da daukan ball har guda biyar khalil tausayi yaji tana bashi domin yana gani wannan abun na jawaheer ya wuce yanda yake tunani in tayi wani abu kaman ba ita ba, har ta gama khalil bai dauki komai ba yana kallonta cikin damuwa, kallonshi tayi tace yadai babu abunda zaka siya kai? Ajiyan zuciya yayi tare da fadin babu abunda zan siya muje mu biya kudin mu wuce, bayan sun biya kudin wasu daka cikin ma'aikatan suka tayasu fitar da kayan khalil ya tsayar da taxi akasa kayan suka wuce gida, koda suka isa gida mum da dad suna falo, jawaheer ajiye kayan hannunta tayi sannan ta nufi inda dad yake ta zauna tana fadin dad plz kazo muyi magana dan Allah dad ka tashi muje, dad dariya yayi tare da fadin ok muje, tashi yayi suka fita mum ta girgiza kai tare da fadin Allah ya baki lfya.

Jawaheer kallon dad tayi tace dad dan Allah ka tausayamin karka bari mum tace zata tafi dani, kasan ban samu abunda nazo garin nan danshi ba,plz dad ka tausayamin ka bari inga m samir ,dad yace jawaheer kiyi hakuri ganinshi ba abu bane mai sauki amma kizo mu koma insha Allah nayi miki alkawarin sadaki dashi amma sai kinyi hakuri kin bani lokaci kadan, kai ta girgiza tana hawaye tace dad ka tausayamin badan niba dad idan na koma gida wlh tunani zai kasheni tunani zaisa in mutu zuciya ta zata buga dad wata daya kawai nake bukata wlh dad in ban ganshi ba nayi alkawarin zan dawo sannan bazan kara yi muku maganan shiba duk da nasan ba abu bane mai sauki amma zanyi shuru har sonshi ya kashe ni, dad jikinshi yayi sanyi yasa hannu yana share mata hawaye yace kiyi hakuri jawaheer kinji mum dinki ta rantse amma zan mata magana kinji? Kai ta daga alaman eh.

Washe gari jawaheer ta shirya cikin riga da wando tasa wani karamin gyale ta rufe kanta sannan tasa boyfried jacket akan kayan yau babu laifi ta shafa powder tayi kyau sosai saita fito kaman balarabiya wata karamar jaka ta dauka ta rataya, falo ta fito babu kowa hakan ya mata dadi sosai dan bata son tambaya, taxi tahau ta fadamai inda zata hospital din da ambassador yake aka kaita sauka tayi ta biya kudin taxi din ta shiga asibitin a dai2 lokacin taga an bude wata kofa an turo wani akan keke ido ta ware tare da fadin M sa....... m samir..............
Chapter 7 · 0% Book details