← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 45

Sashe 1

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[30/12/2018, 21:35] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan'malikin kawo*

Page 1

*Da sunan Allah mai rahma Mai jin qai wanda ya kara bani ikon fara rubuta wani labari bayan na kammala *TAMBARIN TALAKA* *yanda na fara lafiya Allah kasa in gama lafiya🙏*

*Wannan labarin ban yishi dancin zarafin wani koh wata ba So idan kaga abunda ke ciki yayi shige da rayuwanka badan kai nayi ba ko dan ke*

*ban yarda wani ko wata su canza Min labari tako wani siga ba duk wanda yayi haka ba tare da izini naba ban yafe ba*

Kasar Spain kasa ce da take da mutane fararan fata wato turawa sannan ita wannan kasar yare daya takeyi wato Spanish sai wasu tsirara suke English a airport mutane ne makil anata ihu tare da gudu Wanda yaja hankalin Wanda basu san dalilin ihun ba, suma suka fara dubawa koh lafiya wani matashi ne kallo daya zaka masa kasan cewa shima bature ne jami'an tsaro ne a zagaye dashi yayin da mutane suke ta faman miki mishi paper da biro wasu kuma nata faman daukanshi hoto tafiya yakeyi yayin da yake daga musu hannu shima wata yarinya karama yaga tana miko mishi takarda da biro tsayawa yayi ya amsa tare dayi mata signing sannan ya shafa kanta ya mika mata takardan har waje mutane suka bishi inda motoci ke jiran su, daya daka cikin motar aka bude mai Ya shiga yana daga ma mutane hannu jan motar akayi Suka bar wajan, wani dangareren Gida suka nufa bayan Sun faka aka bude motar fitowa yayi ya nufi kofar shiga cikin gidan bell ya danna wata baturiya daka gani Mai aiki ce dan Tana sanye da kayan masu aiki itace ta bude kofar ganin wanda yake bakin kofar yasata saurin rungumeshi tare da fadin sannu da zuwa duk cikin yaren Spanish suke magana da Fara'a ya amsa da nagode ina Dad? Tace yana ciki yan..... Kafin ta karasa sai ga wani mutum ya fito dan dattijo da sauri ya nufi saurayin yayi hugging dinshi yana fadin My son barka da zuwa dan sakinshi yayi tare da buga kafadan shi yana fadin ina alfahari dakai murmushi saurayin yayi tare da fadin ngd Dad zama yayi akan kujeran dake falon wanda yasha kayan more rayuwa tare da fadin mai aka ajiye min? Dad yace your favorite mai aikin gidan ce ta Kawo mai coffee amsa yayi tare da fadin thank gina yana dan hadawa da turanci cikin maganan shi, Sha ya farayi sannan ya tashi ya nufi dinning inda ya bude wata hummer ya zuba abinci ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya tashi ya haura dakinshi dake gidan wai waye wannan saurayin ne..... Muhammad samir sunansa dan asalin kasar Spain ne domin a nan mahaifinshi yake dan kwallon kafa ne a laliga wanda yake bugama FC Barcelona yana daya daka cikin manyan yan kwallon da ake alfahari dashi a duniya baki daya Wanda akafi sani da m samir tun yana yaro Dad dinshi yace Mum dinshi ta rasu bai taba ganin koda hotan mum dinshi ba, abun yana damunshi sai yasa bai cika zama kasar shi ba dan yana fushi sosai idan ya tuna bai san waye mum dinshi ba, a hannun gina ya taso duk da ita ba musulma bace amma mahaifinshi na kula Dashi tun yana karami yake son buga kwallon kafa kasancewan son kwallonshi yayi yawa yasa bai wani yi karatu mai zurfi ba daka secondary Skul ya gama ya fara buga kwallon kafa duk da sai mai hanya yake samu shima Dad dinshi yana daya daka masu kudin kasar Spain sai yasa bai wani sha wuya ba wajan hayewa, da yana premier league inda yake buga ma Manchester United daka baya ya koma laliga yake buga ma Barcelona wanda aka bashi number 7 domin irin cin kwallon da yake yi number dinne ya dace Dashi sunan mahaifinshi Muhammad Ali, sai yake amfani da sunan Dad din nashi Kafin nashi, m samir matashin saurayi kwata2 shekaranshi 28 a duniya yana da kudin Dashi kanshi bai san nawa ke gareshi ba domin bayan kwallo yana business amma bashi yake kula dashi ba yana da budurwa mai suna sonia yar kasar England duk da ba musulma bace amma yana sonta kuma ita yake son aura tunda addininshi bai haramta mishi hakan ba wannan shine kadan daka labarin shi......

Koda ya shiga daki wanka yayi yasa boxer da singlet kwanciya yayi tare da daukan wayanshi yana dannawa message ne kala2 gasu nan duk bai bude ba ga wasu na kara shigowa Dan tsaki yayi domin bai san ta yanda zai fara karantawa ba inda yana tare da Sonia ne data karanta mai dialing din number dinta yayi ya kara a kunne bugu biyu ta daga tare da fadin swt hrt I miss you wen r u coming bck dariya yayi mai sauti tare da fadin Sonia yau fah nazo Spain and jiya muna tare tace kasan bana son kayi nisa Dani in baka dawo ba nan da 1 week zan zo Spain yace OK zan dawo b4 d tym kafin nan munyi match din da za'ayi inma ban dawo ba sai kizo dan nima nayi missing dinki sosai nan sukaci gaba da hira na soyayya duk cikin harshen turanci kafin suka kashe wayan.

*NIGERIA*

Garin abuja wata matashiya ce cikin riga da wando tasa karamin gyale ta yane kanta kallo daya zaka mata kasan yar wani babban mutum ce domin cikin falon da take zaune ya isa ya nuna maka suna da dukiya yarinyar fara ce tana da tsawo amma ba sosai ba sannan kuma ba wada bace tsawonta dai normal tana da manyan ido sosai ga gashin ido kaman tasa lashes gata fara kaman kalan larabawa kyanta ya wuce duk yanda mai karatu yake tunani wani saurayi ne ya shigo falon da sauri ta tashi tana fadin Ozil dan Allah karfe nawa barce suke da wasa nasha koh 2 ne gashi nasa duk channels din da ake kwallo amma ba'a fara ba, yace toh m samir ai ba zasu nuna ba a nan nima yanzu gidan ball zani inga irin cin da za'a ma Barcelona tace haba dai muna fa da m samir taya za'a cimu dariya yayi yace haba mu madrid ai muke da yan wasa ba kuba gidan madara tace dan Allah ni mubar wannan musun muje Gidan kallon tare in yaso in mun dawo asa mana irin dish din Gidan kallon, wata mata ce ta amshe da fadin amma kam jawaeer kina da aiki dan rashin mafadi da kamun kai sai kice zaki Gidan kallon ball bayan kin san duk Maza ne a ciki babu mata? Kai kuma kabir harda biye mata koh? Baki ta turo tare da fadin mum dasu M samir za'a buga fa kuma kin san in ban ganshi ba zan shiga cikin damuwa, Mum salati tayi tare da fadin jawaeer anya ba gamo kikayi ba ki dauki son duniya ki daura ma wanda bai san dake ba bai masan da zaman ki ba may be ma bai san kasarki Nigeria ba, tace mum taya zaki ce bai san Nigeria ba bayan anayin World Cup nidai Mum mun tafi kallo sai mun dawo ta kalli kabir tace Ozil muje dan Allah tym na tafiya fita sukai suka bar Mum na jimami tare da tausayin yarta ita kuma kalan jarabawan ta kenan son dan kwallo har take fadin shi zata Aura in bashi ba babu wanda zata Aura gashi ita ba yarinya ba balle ace yarinta ne tunda yanzu tana shekara 20 dai2 a duniya zama Mum tayi tana tuna baya lokcin da jawaheer taga m samir ta rude take fadin shi zata Aura har take gaya ma dad dinta kullum tayi sallah sai tace Allah yasa ya aureta wai wacece jawaheer?........ Ku biyoni dan ji yawan comment shi zai nuna min kuna son ci gaba.....

*Maryam obam*
[31/12/2018, 14:16] Maryam Obam Group Kd: *JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

Page 2
Chapter 1 · 0% Book details