← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 45

Sashe 21

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 31-32

Kallonshi tayi ya sakar mata murmushi tare da daga mata gira, yace jawaheer banso ana damunki sai yasa na canza miki sim nd kuma ban san any abu da zai daga miki hankali kin san abubuwan da suka faru na sanin basu mum bane iyayenki kin san tunda maganan nan ta fito kowa zaiji, nd kuma nasa wasu za suyi ta kiranki dan suji maike faruwa, banso wani koh wata su daga miki hankali har zuwa sanda zamu gano inda iyayenki suke, hannunta biyu ya kamo ya matse tare da fadin sai yasa na karya layin, murmushi tayi tare da fadin banyi fushi ba, kawai na dan damune akan mai yasa ka karya sim din ba tare da kamin bayani ba, amma yanzu da naji komai sai naji hankalina ya kwanta komai kuma ya wuce, yace dat my sister, yaushe zamu tafi abuja? Tace ba kace sai anyi kwana biyu ba,yace yes inaso in saba da kakanninmu gashi kuma bana jin yaranku, tace bari in fara koya maka, yace yauwa amma ba'a nan ba, kizo mu tafi waje, tace ok bari in canza kaya, yace ok ki sameni mota, daki ta shiga tasa wata jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan, ta nufi dakin adda taga tana bacci dan haka ta fita kawai tana shiga mota taga anja bata cemai komai ba har suka isa wani hadaddan restaurant babu kowa sai su kadai daka gani yasa an kama mai wajan ne duka, shiga sukayi suka zauna, kallonshi tayi tace mai za muyi a nan? Yace abinci zanci kin san ba komai na iya ciba, nd ke kuma baki damu damai naci ba, tayi narai narai da ido tace nifa kasan bani da lafiya ba yau na dawo gida bama, murmushi yayi yace hakane, my baby da sauri ta dago ta kalleshi hada ido sukayi ita tana mamakin sunan daya kirata dashi, shiko yana mamakin mai yasa kullum jawaheer take kara kyau, idan yaga ta mishi kyau yanzu anjima kuma sai tafi kyau,hura mata fuska yayi tayi firgit tasa hannunta ta rufe fuska tana dariya, dai dai lokacin masu saida abincin wajan suka zo suna tambaya mai za'a kawo musu, fada musu yayi ita tace tuwon semo miyan kuka, suka tafi, basu dade ba suka kawo abincin, sannan suka roqeshi akan su dauki hoto dashi, bai musa ba haka ya tashi suka dauka, suna ta murna, zama yayi yana kallon abunda jawaheer zata ci, lokaci daya kuma yayi dariya yace jawaheer miye haka? Tace mene? Yace wannan abun da zaki ci miye? Tace tuwo, kasa fadan sunan yayi, tace ka gwada ci akwai dadi sosai, kai ya girgiza alaman a'a, murmushi tayi ta fara ci, mai yakon yaci nashi saiya tsaya kallonta yanda take ci sai yaji abun ya burgeshi, dan haka shima yasa spoon cikin tuwan yaci ido ta kura mishi, taga ya cinye ya kara ci wasa wasa sai gashi ya cinye tuwan duka, saida ya gama yace ashe akwai dadi sosai dariya tayi tace abincin mu yana da dadi, murmushi yayi sannan ya fara cin farfesun kazan da aka hado mata dashi bai wani ci da yawa ba ya ajiye tare da kallonta yace ban taba cin abinci mai yawa irin haka ba, dariya tayi tace dan wannan abincin shine mai yawa? Yace eh mana, yace toh a fara koyamin hausa, tace mai kake so ka koya?? Yace komai amma nafi son in fara koyan gaisuwa, nan ta fara koya mai gaisuwa tana fada mai da turanci saita fassara mai, sannan ta koya mai tambayan abu, da wasu yan abubuwa, murmushi yayi tare da kunna wayanshi taji magananta ashe recording yayi, kokarin kwace wayan ta farayi wai zata goge garin haka ta fada jikinshi sukai qasa, wani irin yanayi dukansu suka shiga musamman ma shi, domin kirjinta ne ke kwance akan jikinshi, ganin irin kallon da yake mata yasa ta tashi da sauru tare da fadin kayi hakuri, baice mata komai ba harya tashi sannan yace baki ji ciwo ba? Kai ta daga mishi alaman eh, cikin sanyin murya tace muje gida dare ya farayi, tashi yayi yace muje, mota suka shiga aka sauketa kaman bazai fita ba komai ya tuna oho ya fito har kofan gidan ya kaita sannan yace mata saida safe, bata bashi amsaba ta shige, a falo ta tarar dasu mum harda dad, mum tana ganinta tace jawaheer daka ina kike maiya sami wayanki? Tace mum muna tare da m samir sannan na canza number ne, ido dad ya bita dashi yace saboda me kika canza number kuma baki bamu ba, tace dad m samir ya siya mana dazu nan ta fada musu number din suka saka, dad yace zai tafi hotel din daya sauka mum ta rakashi jawaheer kuma tayi dakin da take kwana ita da mum.

M samir koda ya isa an kira sallah isha'i dan haka saida yayi sallah sannan yayi wanka ya kwanta, amma kuma sai me?? Tunanin jawaheer ne cike a ranshi, musamman dazu data fado mishi jiki ido ya lumshe tare da fadin maike damuna? Kanwata ce da sauri yace no bazan iya ba kanwata ce kawai sabuwan da mukayi ne yasa nake jin wani abu but zanyi dan nesa da ita, duk yanda yaso ya cire tunanin jawaheer ya kasa daka karshe recording din da yayi ya kunna yana jin muryanta yana dariya har bacci ya daukeshi.

Itama ta gefen jawaheer tunanin nashi tai tayi ga wani irin azabban sonshi dake kara shiganta, Allah ya sani tana hakuri da irin son da take mishi amma ya kasa fahimta wani lokacin har tunani take inda zaice ta bashi jikinta zata iya bashi dan dai kawai yasan tana sonshi, duk da wani lokacin tana kokarin cire shi a ranta amma ina abun ya gagara sai dai kullum tayi sallah tana roqan Allah mafi alkhairi.
Chapter 21 · 0% Book details