Sashe 27
Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Dago dakai tayi ta kalleshi sannan tace plz ka daina fushi dani, dan murmushi yayi tare da fadin komai ya wuce rungumeshi tayi tare da shafa mishi gashin kanshi, dariya yayi yace karki bata min gashin kai, tace sai in gyara maka, kiran driver yayi yaja suka wuce, tafiya suke kowa da abunda yake tunani, ita ta gefenta tana tunanin yaushe zai sota, yaushe zai fahinci irin son da take mishi, shiko ta gefenshi yana tunanin tunda sun bar yola babu ita babu ganin dr dama shine damuwanshi ya rasa mai yasa ya tsani dr din, dan waigowa yayi ya kalleta bacci yaga tanayi dan jiya batai bacci ba tunani ya hanata, ido ya kura mata yanda take bacci hankali kwance, yana cikin kallonta yaji ta fado jikinshi, murmushi yayi tare da kara gyarata ya mikar mata da kafa tare dasa kanta akan kafanshi, tafiya suke mota nata sharara gudu, bai taba long journey ba a mota sai yau, dan haka shima ya gaji sosai, amma yana jin dadin tafiyan, bude ido tayi taga anata gudu, tashi tayi daka jikinshi da sauri tana murmurza ido, murmushi ya sakar mata, tace har yanzu bamu kai ba? Kai ya daga mata alaman eh, tace kai wlh na gaji gaskiya da nisa, murmushi yayi tare da fadin matso nan, matsawa tayi kusa dashi yasa hannunshi akan kafadanta yace kefa kinyi bacci bai kamata kiga nisan wajan ba, tace ni nasha ina tashi zan ganni a gida, dariya yayi yace oh i see sai yasa kikai bacci, kai ta girgiza alaman a'a, yace toh miye? Tace jiya banyi bacci ba sai yasa nayi yanzu, kallonta yayi yace maiya hanaki bacci?tace babu komai kawai dai bana jine, shuru yayi tare da aiya nawa cikin ransa kodai tana tunanin wannan dr din ne? Tsaki yayi mara sauti amma duk da haka taji, dago kai tayi da sauri ta kalleshi ganin ya tamke fuska yasa tasa hannunta tana shafa mishi fuskan tare da fadin miye kuma? Hannunta ya cire daka fuskan nashi tare da fadin babu komai, bata kara cewa komai ba har suka zo wani kauye da ake ta siyar da abubuwa, tace driver dan faka, driver tsayawa yayi a gefen titi, kallonta yayi yace mai za kiyi tace yunwa nake ji abu zan siya, yace nop ki bashi ya amso miki, tace ai ban san mai zan siya ba saina fita na gani, kallon wajan ya farayi yana dubawa, tsaki yayi tare da cema driver yaja motar su wuce, driver ya tada motar suka tafi, tace ya zamu tafi ban siya komai ba, yace saboda abun wajan bai min ba, tace nifa yunwa nake ji, yace sorry in naga wajan da yayi min sai a tsaya kici, kai ta daga alaman toh, tafiya suke tayi babu wanda ya kara magana, har suka shiga cikin wani gari yace driver ya tsaya, bashi kudi yayi yace ya siyo mata kaza da drinks, amsa yayi ya fita jim kadan sai gashi ya kawo kaji har guda biyar, da drinks da yawa, amsa tayi ta fara budewa kudi ya kara ma driver yace kuma kuje kuci abinci tare da sauran security din, yace ok, bude kazan tayi tace kai yayi yawa, fara ci tayi tare da miqa mai kai ya girgiza tare da fadin nop bana ci, bata fuska tayi tace in baka ciba nima zan daina ci, kafada ya daga alaman bai dameni ba, ganin haka yasa ta ajiye naman wai tayi fushi, murmushi yayi tare da daukan naman yasa mata a baki ta kawar dakai yace plz kici ban san taurin kai, daukan naman tayi shima takai mai wajan baki ya kawar dakai ta kara matsawa kusa dashi zata bashi ya janyota jikinshi wanda yasa bakinta ya mannu a nashi, dukansu tsayawa sukai cak, sunyi wajan minti daya kafin ya danja baya, da sauri itama ta matsa tare dajin wani iri, shuru dukansu sukayi na wani lokaci sannan taji muryanshi yana fadin muci, bata musa ba suka fara ci, har driver ya dawo suka tafi baka jin karan komai sai wakan nicki minaj, sai wajan karfe hudu suka karaso garin abuja, tana ganin sun shigo taji wani irin dadi, gida suka nufa da sauri ta fita suka ci karo da khalil wani irin runguma sukai ma juna na murnan ganin juna, khalil yace sis sake ni mana inje inga samir, tace babu ruwana dakai dariya yayi yace sorry sis ai nafi jin dadin ganinki akanshi, dariya tayi tace mai wayau, sakinshi tayi ya nufi m samir dake tsaye yana kallonsu yana dariya hugging dinshi yayi tare da fadin bros u r wlcm, m samir yace thanks, ya umar ne ya fito shima cikin murna yayi hugging m samir sannan suka shiga ciki, jawaheer dakinta ta nufa tana shiga tayi toilet dan tayi wanka, bayan tayi wanka ta fito tasa wani wando 3quater da wata top mai bala'in kyau ta fito falo ta gansu su duka suna ta fira hawaye ne ya zubo mata tunawa da tayi bata hada komai dasu ba, wani irin zafi takeji daka zuciyarta, juyawa tayi zata koma daki dad ya kirata tsayawa tayi cak dan haka ya tashi ya nufi inda take, ya janyota jikinshi tare da fadin ina zaki, tace zani daki ne dad, yace no muje, kaita yayi har wajansu ta zauna kowa idanshi na kanta, tausayinta suke ji sosai, ga hawayen da take son boyewa ya kara zubowa, khalil yace sis miye haka? Bata bashi amsa ba sai kuka data saki tare da fadin mum plz muga kwalin da aka baku ni, kowa ya tausaya mata da turanci take magana kowa dake falon yaji mugun tausayinta, mum cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi dakinta sai gata da kwali, miqa ma jawaheer tayi ta riqe kwalin tana kuka, budewa tayi taga international passport, dauka tayi taga wasu abubuwa akai budewa tayi tana kuka wani dan karamin passport ne ya fito, da sauri ta dauka tana kallon hotan fuskan matan sak mata da sauri ta nuna ma mum tana fadin mum kalla ki gani da sauri mum ta amsa tace wlh itace ta bamu ke jawaheer itace kuma duk yanda akayi mahaifiyarki ce dan ga kaman ku nan, ci gaba tayi da duba kayan ta dauko wasu riga da wando masu kyan gaske tana kallo, mum tace wannan sune kayan data bamu ke sune lokacin a jikin ki, rungume kayan tayi tana kuka mai ban tausayi m samir dake zaune yana kallonta cike da tausayi ya tashi ya nufeta tare da goge mata hawayen yace jawaheer kiyi hakuri ki daina wannan kukan nayi miki alkawarin haduwa da mum dinki bada dadewa ba wannan nauyin yana kaina, kuka ta kuma saki tare dayin hugging dinshi duk wanda ke falon saida tausayin jawaheer ya tsargo mai cikin zuciya, musamman khalil da sukafi sabawa dashi lokacin da yaji ba kanwar shi bace yayi takaici sosai dan yana son jawaheer, m samir amsan kwalin yayi tare da fadin mum a nan zan zauna ina daki na? Mum ta kalli jawaheer tace jawaheer kaishi dakin kusa dana khalil, mum tayi hakan ne dan jawaheer ta daina kukan, tashi tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya, bayan sunje kofar dakin taja jiki ta tsaya tare da nuna mai kofar da hannu alaman ga dakin nan, murmushi yayi tare da fadin tare zamu shiga, batai magana ba ta bude kofar ta shiga shima ya shigo, dakin akwai komai a ciki ga kamshi dake tashi daka ganin mum dazu tasa akasa komai dan tasan da babu komai a dakin, kallonta yayi yace wow dakin yayi kyau bari inyi wanka ki zauna ki jirani, kai ta daga mai alaman toh, yana shiga ta fita waje dakinta ta nufa ta kwanta tana kuka mai cin rai, yanzu basu mum bane suka haifeta ji take abun ya dawo mata sabo, musamman da taga bros umar khalil ga mum ga dad ga samir, amma ita bata hada komai dasu ba, mai yasa haka ya faru da ita mai yasa mum dinta ta bada ita, lallai tana bukatar jin amsa ada bata da burib haduwa da mum dinta amma a yanzu tana so, tashi tayi da sauri ta dauko wasu takardu tasa a jaka tare da daukan key din mota, har zata fita ta tsaya ta koma ta nufi wardrobe dinta ta dauko wata doguwar rigan atamfa tasa tare da yafa gyale akanta karami fita tayi ta nufi dakin m samir tare da fatan Allah yasa bai fito daka wanka ba, shiga tayi tako ci sa'a bai fito ba wajan kwalin ta nufa ta bude tare da kwashe kayan dake ciki tana kokarin fita taji ya kira sunanta da jawaheer tsayawa tayi cak, ba tare data waigo ba, ganin bata waigo ba yasa ya fara matsowa kusa da ita ji tayi ya riqota ta baya tare da juyo da ita, kallonta ya tsaya yi sannan yace wannan kayan fah? Mai zaki dasu? Kallonta ya kumayi daka sama har qasa sannn yace ina kuma kikë shrin zuwa? Wani irin hawaye ne ya gangaro mata sannan tace zan tafi zan tafi gaba daya zanje neman mahaifiyata lokacin da nake yola banji ina son ganinta ba, amma dawowa na nan gidan yau yasa naji ina son haduwa da ita, yau nasan miye iyaye bazan iya zama a nan ba dole in tafi in nemot..... Janyota yayi jikinshi tare da toshe mata baki yace ya isa haka jawaheer ya isa haka, karki kara tunanin barin nan gidan, kina tunanin kinyi adalci kenan yasu mum za suji in suka ga bakya nan?? Kinyi tunanin haka? Tace karka dakatar dani ka barni dan Allah yace jawaheer mai kike tunani kin san halin da kowa zai shiga kuwa? Nima kaina kin taba tunanin wani hali zan shiga idan aka nemeki aka rasa? Da sauri ta dago dakai suka hada ido lokaci daya kuma ta fashe da kuka tare da fadin koda na tafi kuna raina har abad......... Shhhhhhhhh ya dakatar da ita tare da fadin okey na fahimta amma kafin ki tafi inaso ki fadamin wani irin so kike min dahar kike tunanin barina gaba daya saboda wani dalili?? Zaki iya nesa da abunda kike so ba tare da kin sameshi ba?? Kasa magana tayi sai kuka da take tayi, shima shurun yayi tare dayin hugging dinta sosai yana mai jin kukan nata har cikin ranshi, ido ya lumshe ya rasa mai yasa yake jin abubuwa da dama akan jawaheer wanda baya ji akan ko wata mace, ko sonia da sukai zama tare na lokaci mai tsawo baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a halin yanzu sakinta yayi tare da janyota suka zauna akan gadon dakin yace jawaheer kiyi shuru kibar wannan kukan, nayi miki alkawarin neman miki mum dinki jibi zan koma spain muna da wasa bazan dawo kasar nan ba har sai na nemo miki mum dinki, inaso kimin alkawari ba zaki kara tunanin barin gidan nan ba, kai ta daga cikin kuka alaman eh, tare da rungumeshi tana fadin nagode sosai Allah ya baka abunda kake so, a hankali yace ke nake so jawaheer..........