← Book details Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 45

Sashe 26

Jawaheer Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Shiko m samir ya rasa dalilin da yasa ya tsani dr, shidai abu daya ya sani bawai yana son jawaheer bane, kawai yana tausaya nata ne, dan shuru yayi lokaci daya kuma yace ba haka bane, kawai bana sonta da dr dinne dan ban yarda da hankalinsa ba, daukan wayanshi yayi ya doka mata kira, ringing biyu ta dauka, yace mata kin gama shirin mamaki tambayar tashi ya bata tasan dai dazu yana ta nuna mata halin ko in kula, yanzu kuma yana tambaya waiko ta shirya, tace eh na shirya komai duk da basan komawa nake gobe ba, yace saboda wannan dan iskan dr din koh?? Jawaheer ina tunaninki yake wai yaushe ma kika fara sonshi ne?? Shuru tamai tana jin ikon Allah daka cewa bata son komawa ya hakikance yana ta zagin mutum wanda baisan maike faruwa ba, tace kana cin hakkinsa domin shi bai san maike faruw....... Wani irin tsawa ya mata tare da fadin yimin shuru ban san haka kike ba, da tun farko ban daukeki a matsayin friend ba, wani irin takaici taji lokaci daya maganan da bata zata, zata fito ba taji ta fada nima fa budurwanka bace kace ni kawarka ce ina da right in kula duk wanda naga dama, jin ya kashe wayan yasa ta fara tunanin maita fada mishi haka, daura hannu tayi akai tana kuka tare da fadin Allah yasa ba fushi yayi da ita ba, daukan wayan ta tayi ta kirashi amma saiya saka mata busy alaman ya kashe wayan, daka karshe ma data kara kira sai taji switch off, kuka ta saki mai karfi mum dake kwance kusa da ita tana bacci ta farka tare da tanbayan lfya jawaheer? Tace mum wlh ina son m samir ban son in rasa shi, mum ta janyota jikinta tana fadin kiyi hakuri jawaheer idan Allah yasa shi zaki aura dole ya zama mijinki ance matar mutum kabarinshi, tace hakane mum, in ban sami m samir ba zan iya shiga cikin wani hal...... Toshe mata baki mum tayi tana ta rarrashinta, dakyar tayi shuru amma maganan bacci kam babu shi, dan ya gudu yanda taga dare haka taga safiya, tunda tayi sallah asuba, ta nufi dakin adda, adda tace jawaheer lafiya naga kaman idanki a kumbure? Kuka ta fara tare daba adda labarin abunda ya faru, adda tace ai gaskiya kika fada mishi baki Karya ba, aishi ba saurayinki bane, dan haka dole ji tsaya da wasu, jawaheer tace haba adda nifa shi nake so, adda tayi tsaki tare da fadin ai sai kiyi ta son nashi, kina son mutum yana miki wulakanci dan yaga ya hadu, shima yanda ya hadu haka kema kika hadu, babu namijin da zai ganki yaji bai sha'awar ya mallakeki, dan haka wlh kima cireshi a ranki tun kafin ya sa miki ciwon zuciya, gwara ki nemi mai sonki kibar wanda baya sonki, jawaheer cikin kuka tace adda bana son wannan magan ganun naki basu da dadin ji wlh, adda dariya tayi tare da fadin kaji ja'ira gaskiyan ne baki so? Tace adda taya zan cirshi a raina bayan kin san ba abu bane mai yihuwa? Adda tace ina zaune zanji kince kin cireshi a ranki amma fah kar kice na miki baki, kallon adda tayi sororo tace kaman ya adda? Adda tace nan gaba zaki gani badai namiji bane shi, jawaheer tashi tayi ta fita alaman taji haushin maganan adda, dariya adda tayi tace kai Allah ya yaye miki yarinya sai kace a kanfa aka fara soyayya ita ko zuciya ma taki yi, shiba sonta yake ba amma ta like mai, dakinsu jawaheer ta shiga taga mum na hada kaya mum tace yauwa jirgin 8 za mubi kizo ki shirya, jiki a sanyaye tace toh fita tayi ta nufi toilet tayi wanka da ruwan sanyi dan garin ana dan zafi, fitowa tayi ta fara shiri cikin wata doguwar riga na less yayi mata mugun kyau, duk da batai makeup ba, ta daura dankwali irin ture kaga tsiya ta yafa wani karamin gyale, sannan ta fita falo, inda adda tasa musu abinci kunu da alale da farfesun kayan ciki, zama sukai suna ci amma ita kam jawaheer tunani take saida mun ta lura da ita tace jawaheer tayi firgit mum ta girgiza kai tare da fadin kici abinci mana, bata ce komai ba ta fara ci, bata wani ci da yawa ba ta ajiye, adda tace zo muje ki rakani can gidan, tashi tayi suka fita ita kuma mum ta fara shiri itama, bayan sun fita tafiya sukai mai dan nisa jawaheer tace kai adda na gaji, adda tace muje mun kusa, kan wani dutse suka je suka zauna, jawaheer tace ina gidan? Adda tace jawaheer babu inda zamu nace muzo nan ne saboda mu sami daman magana ni dake, inaso kiji kuma ki duba ki gani, jawaheer idan kika duba rayuwa yanzu ya canza a baya kinyi kuskure kin nuna ma samir kina sonshi yaki yarda ya soki kaman yanda kike sonshi, idan kika duba zaki gane tun daka sanda kika furta kina sonshi zaiga bazaki iya rayuwa ba tare dashi ba, sannan namiji yace yana sonki yata kaya balle kece kika furta mishi kalman so, aikin bani, wlh indai kika bi yanda na fada miki zai fito yace miki yana sonki, jawaheer tace me kenan? Tace matso kiji, magana ta mata a kunne, jawaheer tace amma kina ganin hakan zaiyi? Adda tace insha Allah ki gwada, tashi mu koma ma dan nasan yanzu ke ake jira, kallon agogon hannunta tayi taga 8:30 tace adda lokaci ya wuce gashi wayana yana gida, adda tace kai muyi sauri toh, suna karasawa kofar gidan taga motocin m samir a kofar gidan, gabanta taji ya fadi ance jirgin 8 za subi gashi yanzu 9 ya kusa, tana shiga ta ganshi a tsakar gidan yana kaiwa da komowa,waigowa yayi ya ganta a tsaye wani irin kallo ya mata tare da fadin daka ina kike?? Tace mun fita ne da adda, yace karfe nawa yanzu?? Tace 8:49 yace what time zamu tafi? Tace 8 yace gud tawo muje fita sukayi suka hadu da adda, ya kira security dinshi ya mishi magana yace ya fadama adda, yace adda yace in fada miki mum ta wuce saboda jawaheer ta bata lokaci suma yanzu zasu tafi a mota, nan adda taita musu addu'an sauka lfya, jawaheer tace bari in dauko kayana, riqota yayi tare da turata mota suka tafi, tace mishi kayana fah? Yace keep quite karki dameni plz, shuru tayi tana kallon sa, lokaci daya tasa kuka waigowa yayi yana kallonta, yace driver ya faka, bayan driver ya tsaya yace mishi ya dan fita, driver na fita ya janyota jikinshi tare da rungumeta ido ya lumshe yace miye haka jawaheer? Tace haka aboki ya kamata yama kawarshi mai yasa kake fushi dani? Sakinta yayi da sauri kana kallonshi zaka gane ranshi a bace yake, nanata sunan yayi aboki wato yanzu bata sona, aboki ta daukeni...........

*maryam obam*

*JAWAHEER*

*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*DEDICATED TO.....*

*Nafisa mrs dan malikin kawo*

Page 37-38
Chapter 26 · 0% Book details