← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 74

Sashe 8

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takira Dinatu tana tambayarta me yasa baki tsaya an gyara ko in dake ba? Cikin rawar murya"Tace bani da lafiya ina kwance a hostel ranarma ban shigo ajiba". Hakane? Ta tambayi sauran d'aliban suka amsa da eh.sai tadan dafa kafad'rta"Amma yanzu kinji sauk'i?Eh malama naji sauk'i.To jeki zauna ko.Tajuya gaban allo tafara rubutu,tagama rubutawa tajuyo tana fuskantar d'aliban tana musu bayanin sabon darasin da suka shiga.

Sudaida tasake kallan siririn farin agogon fatar dake daure ahannunta na dama,lokacin tama ya kusa k'arewa amma dan wulak'anci ta barta a durk'ushe, gwiwoyinta har sunyi tsami dan rashin tausayi da imani,tabi k'eyarta har zuwan gashin kanta da harara, wannan uban gashin k'aryane ba na ta bane wig ne,ga wani d'inkin rashin mutunci da tayi da atamfar jikinta,koya tayi tasa oho?Taja dogon tsakin dayasa duk yan ajin suka kalleta da mad'aukak'nn mamaki.

Kasham tasake jijjiga kai"ni keki jama tsaki ko?Wallahi yau sai nayi maganin bakin rashin kunya.Tashi kafad'a min abinda yasa kikaki tsayawa ranar juma'a.Taturo baki gaba"to ai Yaya D'ansarai ne yace shi bazai zauna jirana yarasa sallar juma'a ba,ni kuma shine na bishi. Wani lallausan murmushi yasu6uce mata har kyawawan fararan hak'oranta suka bayyana,jin ta ambaci D'ansarai wato dama k'anwarshice wannan? Kawai sai ta rik'o hannunta suka fita.

Ajin yakaure da hayaniya,wasu suna mata ALLAH yak'ara gwamma ayi maganin bakin tsiwan, wasu masu raunin zuciya har idanunsu sun cika da kwalla na tausayin halin da zata tsinci kanta aciki indai tashiga dak'in malamai,musamman kuma da Kasham tayi wannan murmushin sai suke ganin lallai na tanadin wuyane da ALLAH ne kad'ai zai ceci Sudaida.

Sun d'anyi nisa da ajin sannan suka tsaya.Kasham tadafa kafad'arta "Kidaina irin wannan halin bashi dakyau,masoya da mak'iya ba a guzurinsu halinka zai baka su a duk inda kaje"Next time karki sake binshi sai kinyi aikinki kingane ko? Tagyad'a kai.Nima kiyi hak'uri da abinda namiki.Tayi mirmishi "bakome jeki aji ga malamin lissafinku can zai shiga"Always be a good student.

Takoma aji tana wata tafiya irin ta eh yane naci dubu sai ceto.D'aliban suka zaro idanuna suna binta da kallan sama da k'asa alamar"a ah abin mamaki wai Baturiya da suna manga.Dan ba hawaye ba wata alama ta an bata na jaki,amma ba damar tambayarta ya akayi aka haihu a ragaya?Danga Malamin lissafi nan yahad'e girar sama da k'asa,dan shima k'wallan shegene shi yasa ko d'an k'us k'us k'us d'in nan na d'alibai basuyiba sai an tashi tara za a baje kome a fai-fai.Sudaida tamusu fari tana wani lallausan murmushi sannan tazauna awajan zamanta,Suna had'a idanu dashi itama tashiga taitaiyinta.

Suna ciye-ciyensu dasu A'isha a sanda aka buga tara,sauran yan ajin sun zagayesu ana tambayarta an daketa kuwa?ya akayi tabarta tadawo aji da sauri?Sun dauka har a buga tara basu gama horata ba,bulala nawa aka mata?Tawani hura hanci cikin kuri kamar gaske "tama isa ta dakeni ne?Ai wallahi ko kura ta san gidan me babban sanda.Suka kyalkyale da dariya suna ihu;shegiya yar gidan Ibrahim-Mai Lambu, tad'aga musu hannu"a ah kar wasa yayi wasa a tsikari uwar miji fa.Ni yar sunna ce dan haka kar wacce takuma shegan tani ehemmm.

Kasham dasuke zaune a benci ita da wasu malaman suna hirarsu ta k'walamamata kira tayafito ta da hannu.Sudaida tadanja tsaki"nifa wannan malamar tana neman shigarmin hanci da k'udundune. Suka sake kyalkyale da dariya"kila yanzu ne zata hukunta ki a bainan-nasi.Dammm...zuciyarta tabuga tsoro ya baibaye ta, kuma kila hakane,ba mamaki tajuyo maganganun sune tunda dama ba a hankali sakayi taba.Bata kulasuba tamik'e tana Istirja'i.

Ga ni tafad'a cikin ladabi "dole gyad'a tai mai idan tak'i tasha matsa"Kasham tabita da kallo,haka kawai taji tana santa,tunda k'anwar masoyin tane.Lidiya tace"meye haka kuma?Kin kira yarinya kin tasata a gaba da kallo kamar wata magiji.Tasauke gwauran numfashi, tasa hannu a jaka ta zaro kud'in dabata k'irgaba tamik'a mata"ungo kije kisai abinda kike so. Sudaida tabita da kallan tsoro da mamaki kamar yadda sauran malaman sukayi "to da wace hujjar nasara zaiyi hawan k'aho?

"Kar6a mana Sudaida.

Tajuya ba tare data kar6a ba"bar abinki nima ina da nawa.Lidiya tadaka mata tsawa"ke k'aramar mara kunya dawo.Sai kawai tasa gudu.Tayi kwafa zamu had'u dake gobe aji.Kasham tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH Lidiya karki daketa dan bata miki kome ba.How dare you Kasham kice bata min kome ba ni sa'ar wasan tace dazan kirata tak'i zuwa?Saboda ita kanwar wancan me shegen girman kan tsiyan?To niba ruwana abu kazan uban ta zanci.Haushi yakama Kasham sai kawai tace"ai ko abu kazan uban ta yafi k'arfinki har abadan duniya.Cikin tafasar zuciya Lidiya tanuna kanta da yatsanta"Kasham ni kikema wannan rashin mutuncin saboda wasu tsinannun hausawa?Ban miki wani rashin mutunci ba, magana kikayi ni kuma na baki amsa.Banda shiga sharo ba shanu ina ruwanki da ita?Ko ke kika kirata? Kome tamin ni naja,idan naga dama in mata hukunci,idan naga dama in k'yaleta bai shafeki ba"wannan sa kai a uku ne takaban siriki.

Suka farar cacar baki malamai suka shiga tsakani daga nan taran yawatse dan an koma aji. Takoma Staff-Room dan bata da darasi a kowani aji har a tashi sai kuma gobe.Tabishi da kallo cikin harara dan kwana biyu taje yajin aiki akanshi, duk yadda takejin san shi ba ta kulashi sai dai tayita kallanshi.Tamaida kanta jikin kujera ta lumshe idanunta tana wata kisima a zuci "Julaibib kyakkyawane"Melanin beauty"tayi nazarin shi dakyau baya san hayani,wani abun ba wulak'anci yake mataba haka halinshi yake bashi da yawan magana,tana so ta aureshi tahaifi yarinya me irin kwantaccen gashinshi, tana san Julaibib ta rasa ya zatayi da rayuwarta"Ciwon so" data san inda zata nemo maganin shi tasha ta warke daga san D'an Sarai ne?

"Oh my God!, ta dunk'ule hannu ta naushi iska"

Dasauri tamik'e zuwa wajanshi D'ansarai takira sunanshi.Yad'ago yakalleta yacigaba da abinda yake yi,sai ta rasa me zatace...Dan ALLAH bani aran correction pen. Yaciroshi a aljihun gaban rigarshi daya soke yamik'a mata.Tashafi hannunshi sannan ta kar6a "nagode idan nagama zan kawo maka.Yagirgiza kai "Kirik'e kawai.To nagode,tasa ajaka dama neman magana ne itama tanada nata fa.

Duk ranar alhamis suke House Assembly, wani ikon ALLAH sai akasa Kasham da Julaibib a house d'aya,Sudaida ma anan take. Kasham a matsayinta na sabuwar malama ita tafara musu bayanin kanta da yar nasiha,sai malamai biyu duk yan TP sai Julaibib cik'on na hud'unsu.Cikin natsuwa yake musu bayani sannan yad'ora da nasiha a kan su dage da karatu ba kawai sai lokacin jarabawa ko za ai wata kaci-kaci da muhawaraba, kullum Ku zama masu nazari da bincike da tambayar duk abinda baku ganeba, da wanda baku saniba da hakane ake samun ilmi me yawa,ita k'wak'walwa d'an Adam ne yake cikata da aiki,idan kuma baiyi hakan ba to ita zata cika mishi da abubuwa na shirme wanda bazai amfaneshi akaran kanshiba,bare har al'umma ta amfana,ina fata zaku dad'a sa k'wazo duk da nasan kunayi amma Ku k'ara, ina kuma fata zaku zama masu amana kamar yadda sunan gidan na ku yake "Amana House.

D'alibai suka d'auki tafi.A'isha da take bayan Sudaida tace"Amma gaskiya ina san Yayanki Sudaida,yanayinshi me sanyine,sukayi murmushi.Mr Julius shugaban house d'in shima yatafa mishi,yau bani da abin fad'a.Yanuna Julaibib da yatsa"This great teacher of ours has said all".Yad'an bubbuga kafad'arshi sukayi murmushi,sannan yakalli d'aliban yad'an motsa kafad'arshi"shikenan you can go back to your classes" duk suka watse.

Maimun yakawo musu ziyarar bazata ranar juma'a da yamma,sun kuma ji dad'in haka sunata ba juna labarin makarantun da aka turasu har Maimun yasako mishi maganar Kasham...Yayi kamar badashi yakeyi ba.Zuwacan kuma yagirgiza kai"ni fa ba zanyi abinda zai zama min matsala ba,aure ba abin wasa bane, ba kuma yin auran ne yadameni ba,a ah samun matar data dace dani me mutunci da mutunta kai.Kasan ALLAH Julaibib Kasham tana sanka,wannan soyayyar da take maka zaisa tamaka biyayya tabi umarninka.Yagirgiza kai"Kyaleta kawai Maimun. Maimun bai kuma maganarba suka cigaba da hirar data shafesu har Musaddiq yafito suka tafi k'wadago neman halali.

Baranzan yajuya yana kallanta"Ke wai meye damuwarki ne?Wani haushin shi takeji gwamma tabar mishi d'akin dan batayi maraba da zuwan shiba,idan tazauna za ayi d'anyan aikine dan shima bashi da mutunci idan yana 6acin rai.A fusace tajuya zata fita,caraf taji yarik'o dantsen hannunta kamar zai k'aryata.

Tarinse idanu dan azaba. Yasunkuya akan fuskarta"sai kin fad'a min da uban wa kika fara soyayya da har kike guduna? Sake min hannu.Yasake rik'eta tamau.Sai fa kin fad'amin da uban wa kika fara soyayyah? Haushinshi yadad'a ninkuwa a zuciyarta Kawai sai tace da"Ubanka...bata gama rufe baki ba taji saukan mari hagu da dama,idanunshi suka kad'a jawur"za kimin rashin mutuncine?Uba na sa'ankine?Yafad'a da karfi cikin tashin hankali da alama allurar soja ta motsa.Uba na ko? Tagyad'a kai duk da a zabar rik'on data keji.Kikace eh? Yashak'eta,manyan idanunta suka fir-firto numfashinta yazo wuya,yasake kifa mata mari hagu da dama,sai da taga wasu k'ananan taurari sun tarwatse, gefen bakinta ya fashe,ji da ganinta suka d'auke na wucin gadi..

Wannene abin so?... A tari fitsari a wanke zawo?

18 Rabi'a Thani 1441
15 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta'in

...GWAJIN DAFI💔

Almost true story
Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Shafi na biyar.

Dak'yar aka 6an6areta a hannunshi bayan tasha wahalar duniya.Yarafff... tafad'a gado tana wani irin tarin wahala tana fuzgo numfashin ta dayake k'ok'arin kufcewa.Shima ya fuzge daga rik'eshin da akayi ana ta bashi hak'uri,yayi kanta,aka sake rik'eshi

Lidiya tashigo da gudunta dan bata san abinda ke faruwa ba yanzu aka kai mata rahoto"haba Baranzan kazama namiji mana, jarumin namiji me kwanan daji irinka me zai sa katsaya fad'a da mace?Kasham fa kwana biyu bata da lafiya ya kamata kamata uzuri.Anki a mata uzurin wa tafad'a ma bata da lafiya? Yabita da kallo tana kwance sambal,gashin kanta a hargitse kuma ta rame ba haka yasan Beauty d'inshi yar gayu ba.To kitashi muje asibiti. Shiruma amsace.Yad'ibo wasu damin kud'i yaba Lidiya wai tarakata asibiti ta tabbata an dubata ankuma bata magani me kyau.Tagyad'a kai tare da sara mishi "Yes sir tabuga k'afar damanta a k'asa.
Chapter 8 · 0% Book details