← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 74

Sashe 58

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasake bin shi da kallo cikin tsoro da shakka"to ko dai Yayi Julaibib ya fara k'arama sama hazo ne?data isheshi da tambaya sai kawai yamik'e yashige d'akin baccin su har yanasa mukulli,bai fito ba sai da za shi masallaci sallar azahar.Tamik'e ta tare k'ofar.Yad'an yamutsa fuska "ke bani hanya yanzu za tada sallah.Tagyad'a kai"ba in da za ka har sai ka fad'amin abinda yake damunka da har za kace a rabu da Inna..

"Adai-daita sahu a had'a kafad'a...

Suka fara jiyowa daga masallaci yad'an kalleta cikin natsuwa"barin dawo daga sallah sai muyi maganar ko?

Daga masallaci makaranta yawuce bai koma gidan ba,tagaji da jiranshi,itama tatashi tabishi,yana jin an kwankwasa k'ofar ya amsa daga ciki"na'am bismillah shigo,bai zaci itace ba.Takulle k'ofar tazare mukullin"Yaya D'ansarai ni fa ka sani a rud'ani wallahi, wai me yake damunka ne Inna za tayi magana dakai kace wai a rabu da ita sannan ka k'wace waya ta ka kashe,ta kama ka kashe me yafarune?Ni ma kwana biyun nan kwata-kwata bana gane maka.Yamaida kanshi jikin kujerar"to Inna me za tamin?Inna bata da maganin damuwata fa.

Da rawar murya tafara nuna shi da yatsa"Kai Yaya D'ansarai Innarce..ba..ta da maganin... damuwarka?To duk fad'in duniyar nan ma kana da kamar tane?Takalleshi cikin takaici"to wa yake da maganin damuwarka?!

Yajanye kanshi daga jikin kujerar yad'ora duka hannayenshi a saman tebur d'in sannan yakalleta cikin natsuwa"Zaujatiii...ke ce maganin damuwata,ina k'aunar ki, ina jin takaicin ace wai ni Julaibib yanuna kanshi da yatsanshi wai ni zan rabu dake dan kawai ba kya haihuwa, ni ina son ki a kowani irin hali da yanayi na rayuwa,Sudaida ko baki haifa min Ya'ya ba ba na nadamar aurenki.

Ni yanzu abinda yake damuna yahanani rawar gaban hantsi shine na kasa samo mana mafita ta yadda zamu rabu salin-alin ba tare da Inna ko Kawu ran wani daga cikin su ya sosuba, kema kuma na san kin k'osa amma kina min biyayyane kawai saboda na rok'i alfarma kar kice kome...Dammm... Zuciyarya tabuga...tanajin wani irin yanayi mara dad'i yana bin ilahirin gangar jiki da zuciyarta,gaskiya idan tarabu da Yaya Julaibib...kai anya? Sai tabar wannan ayyane-ayyanen na zuci.

Yawani marairaice"ALLAH yamiki albarka Zaujatiii...yarik'ota da wani salo"ko ke zan d'aurama wannan aikin na lalubo mana mafita danni dai har yanzu na ka sa, amma ko bama tare Zaujatiii...ki rik'e wannan a zuciyarki "ke ce mace ta farko dana fara k'auna,k'auna irin wannan ta aure zan kuma cigaba da k'aunarki ko da bama taren.Jikinta yadad'a yin sanyi da jin kalmar nan ta rabuwa...ganin hakan da tayi sai yacigaba da zugata ta hanyar kambama halayenta na kwarai,da kuma mamakin da yakeyi wai ita da kanta take ikirarin saki bayan ta san hadisin Manzon ALLAH da yace duk macen data nemi mijinta yasake ta batare da wata hujja ta shari'aba toh k'amshin aljannah ma bazata shak'aba,kuma shi k'amshin aljannah ana fara shak'arshine tun daga tafiyar shekara d'ari biyar,haba Zaujatiii...da ilminki da wayonki da kome na ki,tayaya wasu dangin miji can za su rabamu,bayan basu suka had'amu ba,ni fa nake auren nan ba wani ne yakemin ba,ai nine zan miki gorin haihuwa kece kin d'anji haushi ko?Karki kuma d'aga hankalinki a kan duk maganar masu magana,sau nawa muna zuwa ganin likita akan rashin haihuwa ana kuma bamu tabbacin dukkanmu lafiyar mu k'alau lokacine kawai baiyi ba,ba da bakinki kikace ke kin daina shan wata k'waya dan neman haihuwa kin barma ALLAH ba?Me Yaya Asma'u za tayi ta6ata miki rai?Yau kika san halinta?Ai tun kafin mu zama ma'aurata kin sani dan ko gidanku taje sai tanuna wannan halin na ta,kin gani ganin idanunki ke ganauce kuma jiyau..

Rashin haihuwa ba k'ask'anci bane wallahi,Idan kika duba gidan Manzon ALLAH a duk matanshi ba wacce ya keso sama da Nana A'isha kuma har ta koma ga ALLAH bata haihu ba,bayan ita a kwai wash matayen na shi da basu haihu ba,to me garage darajarsu?Annabawan ALLAH nawane da basu haihuba?

Ganin damar ALLAH me idan yaga dama yabaka Ya'ya maza zallah,ko yabaka mata zallah,ko yahad'a maka maza da mata,haka kuma ganin damarshice yabarka bakarare(Mara haihuwa) kinga da...

Bai k'arasa furucin shiba ta k'ank'ameshi tana kuka,yayi lallausan murmushi dan hak'anshi ta tadda ruwa,yacigaba da rarrashinta"Zaujatiii...ni D'ansarai ni ne me auren nan kuma na ce mutu ka raba,ko kin haifa min Ya'ya ko baki haifa min Ya'ya ba,kuma na miki alk'awari zan yima tufkar hanci,ba me kuma samun ke a damuwa a dangina,su suje su rungumi mazajensu cikin annashuwa ni kuma su dagulama Zaujatiii...nah lissafi?Toh karki damu kinji ko?Tad'ago takalleshi"Ya'ya D'ansarai nagode maka da wannan tunatarwar ta ka"idan rai ya 6aci to bai kamata hankali ya gushe ba...kai mijin alheri ne;tasauke gwauran numfashi

"Rayuwata idan babu kai a cikinta za a samu tasgaro me tarin yawa,tadad'a k'ank'ameshi tana shak'ar k'amshin deodorant da arabi'an perfume d'inshi,yad'ago fuskarta suka kalli juna yad'an dage kira yana mata wani kallan k'auna yana murmushi "mun zama k'arfe da mayen k'arfe ko? Tajijjaga kai"eh wallahi autan Inna,D'ansaran Baba,Zaujiii... Ustazun Sudaida yar Ibrahim,jikar Ibrahim Me-Lambu.Suka sumbanci juna yace kuma"mayyar rake abin ma yasamu shiga wai d'an wake a hotel har da injin d'in matse ruwan ko da ta zama tsohuwa ba hak'ora ko?

Tad'an daki k'irjinshi,shi kuma yabata marin soyayya suna dariya.Tad'auki wayarta a saman tebur d'in ta kunna"toh kira Inna gaskiya dan ta damu da rashin jinka tunda har takirani.Yagirgiza kai "gwamma mutafi Zonkwa ayi kome idanu na ganin idanu"zan fad'a mata kece kika hanani.Tad'auki jakarshi taraya a kafad'a suka fito daga office d'in, suka jera suna tafiya zuwa inda ake ajiye motoci da mashinan malamai tana fad'a mishi"Inna baza ta ta6a yadda ni na hanaka kiran taba,tunda ni kullum sai mun gaisa ko ta kirani ko in kirata.

Watannin Sudaida bakwai kenan da tafiyarta Gidan-Waya,duk wannan watannin zuwanta Zonkwa sau hud'u,yanzuma tanata mishi magiya yabarta taje tunda sun samu hutu amma ya hana,wai tayi zamanta a in da mijinta yake ai shine zai fi mata kwanciyar hankali,tagyad'a kai"ni ma na sani ai bawani dad'e wa zanyi ba mak'o d'aya dan ALLAH, amma ya hana,haka dole ta hak'ura,dangin Julaibib kuma sun barta tana rawar gaban hantsi bata san me yafaru ba,amma tabbasss...ta dad'a yadda da kalaman shi kamar yadda yace ba me sa mishi mata a cikin damuwa.

Da safe tana kwance tak'i tashi tahad'a mishi shayin shi ko ruwan wanka,shi yamusu kome,yagama shiryawa sannan ya zauna a gefen gado"Sudaida yakira sunanta.Tad'ago tana kallanshi yana sanye da babbar riga yar ciki da wando na farin yadi yana karya hular zita"har yanzu baza ki tashi daga kwanciyar k'asan nan ba?Tasauke idanunta k'asa"ni dai nafi jin dad'in nan.Yagyad'a kai"sauri nake yi damunje asibiti.Tamik'e zaune dakyar"ba sai munje asibiti ba,naji sauk'i Yaya D'ansaarai.Yagirgiza kai"za dai kiji sauk'i,tun yaushe nakai miki ruwan wanka amma har yanzu baki tashi kinje kin yiba?Yamik'a mata hannayen shi"ta so muje in cud'a ki.Tayi yar dariya"bayan ka shirya?Ai zaka 6ata adon ka,yi tafiyarka yanzu zan yi.Yad'an motsa kafad'a"uh to menene a ciki,ba sai in canja wasu kayan ba? Tamik'e tana mishi rakiya,kad'an ta taka mishi ta dawo tayi kwanciyar ta dan dama bata so tayi wankan,idan tafad'a mishi to sai ya tilasta ta yin wankan ko ta so ko tak'i.

Har yadawo tana kwance yayi tsaiii...yana kallanta yana bin d'akin da kallo,ba abinda tayi yakad'a kai cikin damuwa"wannan ba halin Zaujatiii...bane tabbasss bata da lafiya.Dakyar yatashe ta sai wani narkewa takeyi, amma tanayin wanka sai tajita garau...yana kallon tashar larabawa suna nuna yanayin al'adunsu yana cin gasashshiyar kaza me kayan lambu tashigo yabita da kallo tana sanye da material bak'i me yarfin filawoyi ruwan k'asa, d'an kunne,sarka da warawarenta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi saboda kyallinsu,fuskarta shar da kwalliya, bakinta yana kyallin jambaki ja.

Tazauna suna kallan juna "Zaujatiii...kinyi kyau dame kike son tukwuici?Tad'ora ha6arta a kafad'arshi tayi furucin da wani salon shagwa6a "agada(plantain) yajuyo yakalleta"kin cinye wannan agadan dana siyo miki ne?Ta amsa kai tsaye"wallahi tun jiya.Yabud'e baki dan mamaki saboda ada shi yake matsa mata tasoya musu dan ba wani dad'ata da k'asa yayi ba,amma a yan kwanakin nan cin agada takeyi kamar ta samu abincin gado,d'an kullum, ranshi yadad'e me martaba tuwo miyar kuka abincin hausawa.Kai shifa bai yadda ba sai da yaje yaduba in da suke ajiyewa yaga ba kome sannan yadawo yana cemata lallai kinyi k'ok'ari,yad'auki waya yana kiran wani mak'ocin shi da yau yatafi Jos kuma anjima zai dawo dan ALLAH yasiyo mishi agada.

Yasake kallanta bayan yagama wayar amma fa na d'auka bakya jin dad'i danaga tun safe kina ta bacci har shabiyun rana.Ai na fad'a maka lafiyata k'alau kawai ni dai nafiso in kwanta in yi baccine.Ya mata nuni da kazar.Tagirgaza kai dan ko sha'awar ci batayi,tad'auko lemun peach tana sha suna hira jefi-jefi suna kallansu har suka gama shirin,sannan yamik'e zai koma makaranta "adawo lafiya.Takashe kallan tad'auki wayarta ta kunna data zuwa duniyar yanar gizo...

Da daddare kafin yadawo daga sallar Isha'i Sudaida tayi baccinta a inda ta idar da nata sallar. Yatasheta"Zaujatiii...ga agadan an kawo.Dakyar tad'an bud'e idanunta da yanayin bacci takalleshi sai ta mayar ta rufe,tayi wani juyi tana dad'a shemewa a dadduma"barshi sai da safe ni bacci nake ji,tacigaba da baccinta sai kuma tamik'e zuwa d'akin bacci.

Yabita da kallo har tashige.Shi kad'ai yayi zaman D'akin-shak'atawa yaci abinci kad'an, yaje yahad'a shayin shi da baya gajiya dasha.Yagama yan rubuce-rubucen shi har zuwa sanda bacci yafara kawoma idanun shi ziyara,yashiga d'akin ta kashe wuta,yakunna fitilar wayar shi yana hasketa" tana kwance a k'asa kuma yau tsabar jin bacci ko kayan bacci bata tsaya sawaba,yad'anyi murmushi yana cigaba da kallanta numfashi na shiga da fita cikin kwanciyar hankali,sai tamishi wani irin kyau na musamman, ya dad'a gyara mata rufa dan yasan ko ya maida ita gadon to sai ta sauko wai ita k'asa yafi mata dad'i,yakashe fitilar yakwanta yana musu azkar d'in bacci.

Abinda yaketa maimaituwa kenan,kullum bata da kuzuri,bata san yin kome sai kwanciya,yau dai abin ya isheshi,dan haka yana dawowa daga Kaduna jakarshi kawai ajiye,yatasata agaba sai tashirya sun tafi asibiti dan daren jiya kusan kwana sukayi tana mishi wash...wash...mararta tana mata ciwo amma abin mamaki baturiya da suna manga gari na wayewa sai tamik'e wai ta warke,yanzu kuma yadawo ya ganta lamooo bata da wani kuzari sai bacci-dai bacci dai bata gajiya...Yabita d'akin tanata nuk'u-nuk'unta"Zaujatiii...hijab d'in ne baki gane ba kome?Tabud'e wardrobe tad'auko.
Chapter 58 · 0% Book details