← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 74

Sashe 13

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barrack kuma?Ta tambayeshi cikin mamaki"Eh barrack kin gama makaranta to zaman me za kiyi?Mutafi kafin lokacin auran mu yayi nafa gaji da zama ni kad'ai kingane ko?Bai jira amsawarta yajuya yayi tafiyarshi.Tabi bayanshi da harara lallai za ayita dan wallahi tayi rantsuwa ba wanda zata sake bi har takwana dashi indai ba D'ansarai ba,bata ga kuma wanda ya isa sata canja wannan ra'ayi na taba har abadan duniya.Ita ya ma sosa mata inda yake mata k'aik'ayine,cikin gari za taje wajan Julaibib ta kwana biyu bata ganshi azahiran ceba amma kullum dashi take kwana dashi take tashi a cikin zuciyarta.

Tacanja kayan jikinta da dogon buje na velvet bak'i sai rigar shirt checker me d'amewa ta yafa siririn bak'in mayafi a gyararren gashinta data mishi ponytail style,jaka da takalmanta masu tudu bak'ak'e,tasa wasu manyan d'ankunne masu kama da awarwaro suma bakak'e sai siririyar sark'ar rosery a wuyanta.

Kai tsaye tashiga shagon.Abdul yana zaune yana aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta a darasin tattali (Economics) tak'arema shagon kallo ya dad'a cika ba kamar kwanakin baya ba, za taso taga irin canjawar da D'ansarai yayi.Tadawo da kallanta ga Abdul "Kai d'an samari ina Julaibib d'in? Fuska a had'e ya amsa "Baya nan.Haushi take bashi ita ba wani abu za ta siyaba amma sai tazo tana damun mutane yad'anyi k'unk'uninshi.

Taja kujera tazauna tana mishi kallan nazari,wani murmushi ya su6uce mata "wai shima k'arami dashi ya iya had'e girar sama data k'asa,tana so ta mishi wasu tambayoyi game da Julaibib amma ta san ko tayi a banza talaka ya girmi sarki bazai bata amsaba"Kai k'aninshine? Uhh yace batare daya bud'e bakiba. "Ina Sudaida?Ya yamutsa fuska shifa baya san adameshi, dak'yar kamar me ciwon baki yace "Ta tafi makarantar allo.Bata sake tambayar shi kome ba ta dai gane wannan halin nasu na rashin san magana a jinin sune.Itama sai ta bud'e Ovation d'in hannunta tana dubawa amma rabin tunaninta na ga Julaibib da inda yatafi.

Da d'an hanzarin shi yashigo shagon tare da sallama dan ya san lokacin makarantar allo yayi ba ya so Abdul ya makara.Caraf idanunsu yahad'u"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"tabbas da bata ganshi ba komawa zaiyi.Tamik'e tsaye tana mishi kallan k'auna me ciki da shauk'i " Yayi shar dashi cikin fararan kaya kanshi da bakar hula dara takalmanshi sau ciki farare,k'amshin arabi'an perfume d'inshi ya mamaye shagon,D'ansarai d'an gayu ne,me tsabta na gaban kwatance dan ba wanda zai juri sa fararan kaya sai ma'abocin tsabta.Idanunsu yakuma had'uwa...sai sukaji wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da zuciyarsu,da sauri yakauda kai yana Isti'aza.

"My enigma ma You're wellcome.. Julaibib bazan gaji ba ga shi na sake biyo ka,wallahi ba saboda kowa nashigo cikin gari da safen nan ba sai dan kai.Abdul yad'auki allanshi "Kawu na tafi.To Abdul ALLAH yabada sa a. Yara6a ta gefensu yawuce yana amsawa da"amin ya rabbi.

"Julai...yatari numfashinta"Kiyi hak'uri bazan ta6a miki k'arya wai dan kiji dad'i ba,bazan iya auran kiba, kiyi hak'uri dan girman...k''iris ya rage ta rungumeshi yayi taku biyu baya da sauri sai ta biyoshi har yafita a shagon yajuya da sauri yacigaba da tafiya.Tabishi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta.

Damme what an enigma man.Tafurta tana furzar da hucin takaicin,ta rik'e k'ugu tana kallan shagon"Ya tafi yabar mata shagon duk da kayan mak'udan kud'in da suke dank'are a ciki amma ko a jikin shi, wai an yak'ushi bishiya"shi D'an Sarai ta rasa me yasa yakeyi kamar yana jin tsoronta a wasu lokutan? Ba saurayin data ta6a yi da baiyi kwad'ayinta ya nuna maitarshi a fili ba sai shi, To me yasa!!!???

Yanzu duk abinda yamata za ta iya d'auka ko? Sai kuma ta girgiza kai"Aiko ba kayan Julaibib bane baza ta iya d'aukaba tunda ba na ta bane,idan tayi haka ai tazama 6arauniya"which is forbiden".Taja kujera tazauna dan bazata tafi tabar mishi shago a bud'e ba tunda ita tasashi tafiya,da batayi yunk'urin rungume shiba ta san zai tsaya.

Aminu ne yashawo kwanar yana rik'e da bokitin fenti da roller daga wajan neman halali yafito. Tamik'e da sauri tana fad'in"yauwa dan ALLAH Aminu ka taimakeni kajirama D'ansarai shago yaje gidane ni kuma sauri nake yi ban san abinda ya tsaya yiba.Ya ajiye kayan aikinshi aciki yajawo buta ba matsala.Sukayi sallama.Yayi alwala ya gabatar da sallar walha da aiki yanashi yi a dai-dai lokacin daya sabayi da zarar rana ta 6ullo.Shima gajiya yayi da jiran dawowarshi yaduba mukulli ya kulle shagon, a gajiye yake yaci aikine kamar ba gobe,yanzu zai je gida ya huta,gaskiya neman halali da wuya kowa kagani a inuwa to ba shakka ya sha rana.

Tunda yakoma gida yarasa sukuni wani abu a can k'ark'ashi zuciyarshi yana damunshi,shi dai yasan Kasham tana san shi da gaske, to amma ya rasa gane fargabar da take mamaye zuciyarshi game da ita.Ga wasu irin rikitattun mafarkai da yakeyi,ya rasa gane ma'anarsu,sai dai shi har kullum yana mik'a al'amuranshi a wajan ALLAH,yana yawaita sadaka.

Da daddare suna zaune a tsakar gida ita kanta Inna ta lura dashi, abincin ma k'adan yaci dan yasan Inna tana saurin gane yanayin shi da bazai ci ba dan cikinshi a cunkushe yake."Autana yau dai ko baka jin dad'ine?Yabud'e idanun shi daya rufesu kamar me bacci sun d'an canja kala"Inna kai nane naji yana d'an saramin.Tamishi kallan tausayi me cike da soyayya irin ta d'a da mahaifi"wayyo! Sannu...ai na ganka yau ba wata walwala,ya kamata kasha magani,ALLAH yasauwak'e. Yagyad'a kai "Amin Inna, ai nasha magani".

Alhaji Abdullahi ne yashigo da sallama Julaibib yakar6i kayan hannunshi "Sannu da zuwa Baba" Yauwa D'ansarai mun wuni lafiya? Yau ka rigani dawowa. Yazauna yana hutawa.Inna tad'auko mishi abinci tana mishi nata sannu da zuwan.Ya amsa da kulawa.Yafito da kaya d'inkakku kala biyar dukkansu farare yana nuna ma Inna.To har anyi d'inkin ne? Amma sunyi kyau madalla Ubangiji yasa rai aka yiwa.Ya amsa da amin yana kallan Julaibib"Ina alfahari dakai D'an Sarai tunda kana san ganin tsohonka ya fi na kowa,amma ni gaskiya nan gaba kar a sake d'in kamin kaya duka kala d'aya yo wannan idan hira nake zuwa ai sai budurwar tawa tace min d'an anace,wanke kamayar,itafa bazata gane cewa kullum wani sabo nake sawaba.Julaibib Yad'an shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "kai Baba wani irin zuwa hira kuma,yanzu sai kama Inna kishiya?A ah kaji D'ansarai da wata magana fa, ba a aurowa aka auro ta?Inna tana yunk'urawa za ta tashi yafara dariya"Dakata mana ina za ki?Ko sauraran shi bata yiba"kanka akeji...yad'an daga murya"zo mana Maimunatu...tashige d'aki.Alhaji Abdullahi yakad'a kai "Uh uh uh mata duk haka suke da kishi ba babba ba yarinya,ka ganta nan tunda k'uruciya indai zanyi maganar k'arin aure to zata tashi tabarmin wajen.Julaibib ya sunkwui da kai dan maganar ta mishi nauyi.

Yasake kallan Julaibaib sannan yanuna shi da yatsa "Ita mace dad'in mu'amala ne da ita amma sai ka fahimci halinta,ka kuma sauke duk wani nauyi na ta daya ke kanka,to sai kaga ALLAH yahore maka ita kaji dad'in zama da ita,ai ka sani dai-dai da tsinken da zatayi sakacen naman da ka siyo mata idan tagama ci kai zaka kawoshi ko?Yagyada kai "Eh Baba na sani".

Yace to mace yar gatace gaba da bayanta, kar kayi la'akari da kome yayin da zaka mata kome face cewa aure bautar Ubangijine, shid'in ne yace haka za a mata bad'an kome na taba.Kuma babban jigon zaman aure shine HAK'URI za kayi hak'uri da ita a wajan gazawar ta irinta yar Adam,kaima za tayi hak'uri dakai a wajan gazawar ka irin na d'an Adam,dan babu wani mutum a doron duniya da yake cikakken da bashi da nak'asu sai Annabinmu Muhammad sallallahu alaihi wa ahlihi wasallam.Dan haka sai ana kauda kai ana yafiya,dan wasu lokutan idan suka kwafsa maka sai kaji kamar ka karairayasu,kashafe su a doron duniya,to amma hakan bazai yiwuba dan namiji ne yake cika mace,macece take cika namiji,taimakeke niyace atsakanin juna.

Kadinga tuna cewa tunaninka da nata ba d'aya bane,ko a gidan fiyayyan halitta za6abban za6abbuma sun nuna irin halin nasu,kuma hakan shine cikar macen taka,haka ALLAH yaga damar halittarsu. Yagyad'a kai cikin ladabi" To Baba nagode.

Maza dangin gurjiya sai an fasa ake sanin me k'waya.

25 Rabi'a Thani 1441
22 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta'in

...GWAJIN DAFI💔

Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Shafi na takwas.

Baranzan yashigo gidan da d'okin ganinta, yanata k'wala mata kira amma shiru bata amsaba. Yashiga d'akin da niyyar tashinta dan ya san bacci ne kawai zai hanata amsa kiranshi da kuma fitowa ta mishi Oyoyo cikin d'okin ganinshi itama.Yaja yatsaya da mad'aukakin mamaki yana kallanta,tana zaune kwalliya take fuskarta,yanuna ta da yatsa"au dama kina jina amma kika ki amsawa?Wai lafiya kuwa?Yabita da kallan nazari cike da shakka.

"Beauty wai lafiya kuwa?

Tafurzar da hucin takaici sannan tace"da wannan kiran irin na yan farauta zan amsa maka?Tacigaba da zizara ma girarta jagira"ni gaskiya bana san rashin natsuwa.Yayi saroro kawai yana kallanta tagama kwalliyarta tajawo kayanta tana sawa bujen jeans ruwan bula da d'amammiyar riga mara hannu ruwan madara, yau tayi k'ananan kitson kalaba ta tubkeshi da ribbon ruwan madara sai d'an kunnan beads ruwan bula data sa,wallahi tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,ta sunkuya tana sa takalmi ruwan madara sau ciki me tudu,tagama sawa tamik'e tsaye tana saba jakarta a kafad'a kalar takalmanta ruwan madara,tana shirin fita yakirata "Beauty...Taja ta tsaya sannan tajuyo fuska a yamutse take mishi wani kallan uku ahu"wani abune?Kamar yaya wani abune?Tad'aga misho hannu"kaga malam ya za muyi canjan tambaya ba amsa?Ni fa wallahi sauri nake yi idan ba ka da abin cewa...Yayi murmshi dan wannan kwalliyar ta tsumashi.

"Kurum Ishshi Bazinzira(Akwai kud'i sosai, na rantse miki da ALLAH)
Chapter 13 · 0% Book details