← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 74

Sashe 24

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin daya k'arasa cikin gari har an idar da sallar azahar dan haka yayi alwala yayi sallarshi raka'a biyu ta k'asaru yayi azkar d'inshi sannan yakoma mota yana bin shagunan bakin titin da kallo yana kuma tunano kalaman Sumayya "Idan kaje Rahama Store to ka tambayi shagon Julaibib za a kai ka,yana tambaya kuwa aka nuna shi shagon sai dai kash...Musaddiq ne a shagon, daya tambayi Julaibhib yace yana gida sai bayan sallar la'asar zai fito.Yamik'a mishi wata yar madaidaiciyar jaka ruwan k'asa"Idan ya fito abashi "Miqdad yasake mik'a mishi hannu sukayi musafaha yajuya ya fita daga shagon.

Shima ya so ganin wannan D'ansarai d'in da Sumayya take bala'in so,yayi murmushi ganin yadda tayi da yace bazai kar6i sak'on wani Julaibib ba dan shi ba d'an aiken ta bane, wallahi idanunta har sun cika da kwallah ta sunkwui da kai k'asa bata kuma magana ba,sai tabashi tausayi.Sumayya yakira sunan ta,tana d'ago kai sharrr...hawayan masu d'umi suka zubo a kyakkyawar fuskar ta,tasa hannu ta share su sannan ta amsa a raunane"na'am...Yad'an harareta ke fa raguwa ce daga wasa sai hawaye? Tagirgiza kai"ni ma ban so hakan ba, ban kuma san ya akayi suka zubo ba,ni da Julaibib ai ba wata alak'a kuma sai ta yan uwan takan musulunci,sak'on dazan ba ka wallahi tun a Makka nasiyo mishi,da kuma na san zan had'u dashi a taron MSSN d'in nan na Katsina dana tafi dashi na bashi...ni a yanzu ina san D'ansarai ne saboda shi mutumin kirki ne me addini,amma karka manta ina da jan gwarzo na,dubu jiran mutum d'aya tad'an d'age gira tana wani lallausan murmushi sannan tafurta sunan Salim.Yayi yar dariya "Sumayya kenan so gamon jini.yashige mota yazauna ya d'aura belt sannnan yatayar cikin ambatan sunan ALLAH yad'auki hanyar Kaduna garin gwamna.

Musaddiq yana lissafin wasu kud'ad'e bayan sallar la'asar Julaibib yashigo da sallama yazauna yana kallanshi har yagama yayi rubuce-rubucen shi a littafin da suke rubuta kome na kud'ad'en kasuwan cinsu yamayar cikin dirowa sannan ya ajiye mishi jakar a gaban shi "dazu aka kawo maka.Inji wa?Musaddiq ya dauki mukullin motar julaibib d'in zai fita sannan yabashi amsa "Wallahi ban san shiba bak'o ne"ni nafi. Yagyad'a kai " To Allah yatsare.

Yabud'e jakar dabinon ajwa yagani, ruwan zamzam da farin miski sai envelop da sunan shi yake jiki 6aro-6aro da manyan bak'ak'e

"JULAIBIB ABDULLAHI D'ANSARAI...

Yabud'e da tunanin wa ya aiko mishi da wannan sak'on?

Assalamu alaikum warahmatulla. Julaibib ina gaisheka gaisuwa irin ta addinin musulunci.Ya su Mama?Ya karatu?ALLAH yamaka jagora.Julaibib kasance wata yau raye a cikin musulunci ba wayau da dabara ta bace,a ah ganin damar Ubangijinmune"Alhamdulillahi bi ni'imatil Islam.Wallahi a duk inda naje babu rauni da tsoro zan bayyana identity d'ina saboda addini na yafi kowane addini tunda ALLAH mahaliccin muma yafad'i hakan a Alqur'ani cewa"Addinin musulunci shine addini ko awajan shi "Subhanallahi addinin mu kome anyi programming d'inshi an ba mu.

"Julaibib na san kai mutumin kirkine me k'ok'arin bin dokokin ALLAH gwargwadan iko, dafatar baza ka canja daga yadda na sanka ba. Dan ALLAH kar kabari shaid'an ya rud'eka, rayuwar jami'a ta canja ka.
Daga k'arshe nake mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Me maka fatan alheri a rayuwa.Musha ruwa lafiya...

Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)

Dammm...zuciyar shi tabuga da k'arfin gaske.Sumayya...Sumayya yafad'a ya maimaita cikin san tantance wai wace Sumayyar?Yad'auki wasik'ar yakaranta yasake karantawa,kenan ita ce Amira Sumayya da ta musu lecture akan"Media Influence?(Tasirin kafofin sadarwa)Kasham dai daya sani wacce sukayi College of Education ita ce ta musulun ta?ALLAH buwayi gagara misali,ko shekaran jiya sun samu sak'o ta k'ark'ashin k'ungiyar da take jagoran ta akan Islamic Vacation Conference(IVC)yayi zuru cikin tunano wasu kalamanta da suka ta6a had'uwa da ita a wata seminar da akayi a"National Teachers Institute Kaduna akan"Post Primary Institution Programmed"(PPIP)alokacin ta d'aga hannu aka bata damar yin magana"Tace a gajeran tunani na a kirashi da Propaganda zai fi armashi fiye da Program... bata gama rufe baki ba d'akin yad'auki kabbara kowa yayi na'am da hakan,wallahi shi yasha jin wannan sunan Sumayya Kantiok Donatus to sai dai ko sau d'aya bai ta6a tunanin wai Kasham ce ba...Yatuna ranar farko da daddare a wajan seminar abincin alfarma me rai da motsi aka aiko mishi dashi wai inji Amira Sumayya to ganin sauran ma an basu sai bai kawo kome ba"ashe albarkacin kaza k'adangare kan sha ruwan kasko

"Amira... Sumayya Kantiok Donatus...

Yafurta sunan a zuci...sai yaji wani irin yanayi ya ziyarci ilahirin gangar jiki da zuciyar shi game ita na farin ciki.Ashe shine bai gane taba saboda nikabin data sa,har da gilashin data rufe idanunta"Ina mana barka da shigowa sabuwar shekarar musulunci.Musha ruwa lafiya"abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta kenan.Yajijjiga kai "Tabbas yau goma ga watan"Muharram"yau kuma ga duk musulmin daya samu iko yana azumin "Ashura"Itama tana azumin kenan kamar yadda shima yake yi?Yakad'a kai cikin farin ciki.

"Sumayya ina miki fatan alheri a rayuwa,ALLAH yadauwamar dake a musulunci har k'arshen numfashin ki,ALLAH yaba ki mijin da zai rik'eki da amana,mijin da zai ha6aka miki ki cigaba a rayuwa...

Yad'auki jakar ya rataya a kafad'a yana kulle shagon sai ko ya hango wani d'an k'auyan su Kasham daya ke aikin share-share a Fajumali-Hotel yakira shi...yak'ara so da fara'ar shi"idan kaji gangami da labari,wallahi kamar ka san yunwa nake ji.Yakalleshi da natsuwa ai ba abinci na ce zan ba kaba,kuma ai yanzu lokacin cin abincin rana ya wuce k'arfe hud'u da rabi na yammaci fa?Yabuga k'atuwar hamma baki a bud'e kai da kake a k'oshe kenan wallahi rabo na da abinci tun daren jiya sai yan kame-kame dana yi da safe,ka taimaka min da abinda zan sai abinci dan ALLAH.

Yagirgiza kai"K'wandala ta bazan ba kaba tunda na san mashayar D'one za ta tafi...zai fara mishi rantse-rantse yakatse shi da sauri"kaga in dai yunwar da gaske kake ji to jeka katako kace ma Umma tabaka tuwo na yadda zai isheka in jini...Yad'aga hannayen shi sama"Praise the Lord,Thank you God"yajuya da sauri yaje ya kar6o yazauna zai faraci Julaibib yasake kallanshi cikin natsuwa"Kasham tana ina ne yanzu? Kasham...Kasham... yakalli Julaibib wace Kasham d'in?Kasham kanwar su Alhamdu.Yata6e baki "Kasham ai ta dad'e da barin gida wai ta zama me sallah irin ku,ance wai tana Kaduna amma ni"I don't give a damme ko ma a ina take da me take yi fa.Hakane to idan ka gama ka mayar mata da kwanan.Yajuya yayi tafiyar shi...

Sautu a kasuwar wauta jahilci.

14 Jumaada Awwal 1441
9 January 2020

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSICIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta'in

...GWAJIN DAFI💔

Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Shafi na goma sha uku.

Rana ba ta k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,ranar juma'ar d'aya ga watan Rabi'a Thani aka d'aura auran Salim da Sumayya,Miqdad da Zainab a ranar kuma ko wacce ta tare a gidan mijinta,sai dai mahaifin Kasham bai samu zuwa ba saboda zazzabin da yake yi.

Sumayya sune zaune lafiya suna da fahimtar juna,suna ma juna uziri shi yasa suke da kwanciyar hankali,suna kuma fatan hakan yad'ore har k'arshen numfashin su.

Yana karya hular k'uben dazai sa tashigo da sallama,ta kar6i hular tak'arasa karyawa tasa mishi. Yad'anyi gyaran murya"Ya dai Sumayya yau fa na ganki wata iri.Me ka gani? Shiru yayi yana mata kallan nazari "banga kome a fuskar kiba amma yana yinki ya nuna akwai wani abu,yadafa kafad'arta "kar kiji kome Sumayya ni mijin kine,ba ki da wanda za ki fad'ama damuwar ki sama dani.

Yamata wani kallo"Sumayya mecece matsalar?Fad'a min in har akwai wannan amincin dake cikin zaman na mu. Tamayar da turaran data gama fesa mishi sannan tajuyo cikin d'an murmushi"Miji na nawa ni kad'ai ko?Yagirgiza kai"ai na fad'a miki Sumayya a yanzu bani da buk'atar sake aure,kuma in dai zaman na mu yad'ore a haka to ai ko kin isheni rayuwar duniya, yakalleta amma fa ba alk'awari na miki daga ke ba wata har abadan duniya ba.Tajijjiga kai"d'aya daga cikin abubuwan da suke k'aramin k'aunar ka a zuciya ta kenan fad'ar gaskiya kome d'acin ta. Sukayi murmushi.

Tasake kallanshi cikin natsuwa"tun daren jiya nayi mafarkin Mama kuma har yanzu mafarkin ya tsaya min a rai sosai,dan haka nake neman alfarma kabarni in je in ganta,ka san Uncle ya hanani zuwa wai sai nayi aure idan miji na ya barni shikenan ban san dalilin shi na hakan ba.A yanzu na san kima da girman da uwa take dashi,lallai ta cancanci a mata kome dan a samu albarkar ta, rayuwa tayi kyau duk da rashin sallar da ba tayi, ina san ganinta kewar ta ta dameni,zan kuma yi k'ok'ari wajan ganin na shawo kanta mun dai-dai ta,wata kila tsawon shekarun da mukayi bamu sa juna a cikin idanu ba yasa idan taganni ta yafe min,ni dai ina ta addu'a ALLAH yasa sanyi a zuciyar ta,na san ba abinda yafi k'arfin Ubangijin mu.Yajijjiga kai"gaskiya ne Sumayya iyaye suna da girma da daraja a wajan Ya'yansu, a addinin mu na musulunci suna da mafificiyar daraja sama da kowa.To yaushe kike so mutafi? Bani da za6i,sa mana lokaci.Yad'auki agogon shi yana d'aurawa "Shikenan za muyi magana da Alhaji idan naje kasuwa.To nagode.Yayi murmushi kawai

Tafiyar Dinatu Kaduna waja taransu na zumuntar mata a babban majami'ar su dake Sabon Tasha"Evangelical Church Winning All" (ECWA)na tsawon makonni biyu yabashi damar gyare-gyaran dayace zai yi, gidan yafito rasss har da sabon fenti ko'ina yanata kyalli.Ranar data dawo ta cika da mad'aukakin mamaki tana ka me da ha6a take tambayar shi"ni dai tun kafin in tafi Kaduna da ma na lura da wasu canje-canje saboda yawan kashe kud'in da kake yi,kai ko a ina ka samu mak'udan kud'ad'en da kayi wannan gyaran?Anya kuwa Baban Alhamdu ba ka daga cikin masu zuwa cikin gari suna fasa shagunan hausawa?Dama kwanakin nan abinda ake ta musu kenan.

Yagalla mata harara"ai kema kin sani ko lokacin dana ke ganiyar k'uruciya banyi sata ba,bare yanzu da girmana da kome ALLAH yasauwake.To me kake siyarwa da bazan yi tunanin haka ba?Ba kome. Tazuba mishi idanu "gaskiyar magana bazan yadda dakai ba in dai ba fad'a min in da kasa mo kud'in nan kayi ba. Yamik'e"ai nima ba so nake yi ki yadda dani d'in ba. Tabishi da kallo har yafita.
Chapter 24 · 0% Book details