Sashe 2
Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 7 min read
Su kuma Kataf(Katafawa)suma bayan yak'in Zangon-Kataf d'in sai suka zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Atyap,Su kuma ana tunanin asalin maguzawan Kano ne suka fito suka kafa sansaninsu a wajan,Masu yawan fatauci musamman Kanawa kowa ai yasan mutanan Kano ba cima zaunan al'umma bane,harkar kasuwanci a jininsu yake tun tale-tale,idan suka zo a nan suke ya da Zango bi ma'ana suke hutawa daga doguwar tafiyar da sukayi,bayan sun huta sai su shiga k'auyuka da sauran garuruwa dan harkar fataucinsu, to dalilin hakan garin yasamu wannan suna na Zangon-Kataf...Shi kuma asalin ma'anar"Zango Ciwon kurkunune"da yake fito ma mutum a k'afa,ko ad'an yatsa sai yakasa tafiya saboda tafiyar k'asa da akeyi a da bana wasa bane,wani zarene yake fitowa a wajan sai yayi kamar zai tsinke yatsa ko k'afar,to a inda mutum yazauna zaman jinyan da zaiyi har sai ya warke zai iya tafiya,to sauran abokan tafiya ba jiran mutum za suyiba,to idan aka had'u da wasu,ko kuma suka koma gida sai afara tambaya"ina wane? Sai abokan tafiyarshi suce ai ya ya da zango.
Akan kasuwa akayi wannan yak'in na Zangon-Kataf,su Katafawa sunce sai dai a tashi daga inda ake cin kasuwar a koma inda su suke so, tak'amarsu ai sune tushen wajan,kowa yazo a bayan sune,dan haka yadda suke so dole haka kowa zaibi,Su kuma Hausawa da Fulanin wajan sukaja tunga ALLAH yakashesu kasuwa baza ta tashi daganan ba...Kaya-kaya-kaya kowa yaja ya kafe nashi ra'ayin za abi... Atakaice kenan.
Sarkin Zazzau na wancan lokacin adalin sarkine,daya samu labarin bayyanar wad'annan mutannan sai ya turo wakilanshi dan su musuluntar dasu, sai dai kash... Wakilan sarki sunci amanar sarki basuyi abinda yakamata ba,sai suka bi yarima suka sha kid'a,suka sasu a k'angin bauta,su kama mata da ya'yansu wacce duk tamusu sumata fyad'e,su kwashe musu katti majiya k'arfi su tafi dasu masarautar Zazzau a matsayin bayi dan haka akwaisu da yawa a masarautar Zazzau,d'aya daga cikin ire-irensu shine Yakowa wanda har gwamnan kaduna yayi kafin ya mutu,shi yasa suke wata wak'a wai (Ba zamu ramaba ALLAH ne zai rama mana🤔)
Suka tafi suka bar baya da k'ura dan da yawan matan da suka ma fyad'e sun samu ciki kuma basu zubar ba sun haihu sun mayar da ya'yan irinsu kaico! kuma da yawansu an turasu Biafara Inda Ojuku shima ya jazama k'abilarshi ta Igbo haramcin yin shugabancin k'asar Nigeria har abadan duniya"garin neman gira an rasa idanu"Bayan yak'i suma sun kwaso ganimar yak'i,duk macen data musu suma sun taho da ita yankinsu dan suma anjaza musu salalan tsiya tunda basu da kowa duk sun mutu a wajan yak'i.
Suna cikin k'unci da damuwar abinda aka musu kuma ba daman ramawa kasancewar su bayi sai ga bayyanar wakilan kiristanci(Missionaries)Su basuyi abinda wakilan Sarkin Zazzau suka yiba,suka taimakesu da duk irin taimak'on dasu kaga ya dace su basu, suka dinga musu wa'azi akan addinin kiristanci (Christianity) shine addinin gaskiya,su kuma sukayi na'am da hakan suka rik'e addinin da hannu biyu,nan da nan suka waye ga kuma bayyanar ilmin boko an gina musu makarantu,asibotoci da duk abinda ake buk'ata,shine sai suka bar zaman kan dutse suka kafa k'auyuka da garuruwa suka warwatsu tunda dama sunada mugun yawa, kamar irinsu:-
Fadiya.
Fadan Kaje
Madauci.
Madakiya.
Katsit.
Kamurun Kaje.
Ladduga.
Zonkwa.
Da sauran su kuma ance wasu daga cikin sunayen Ya'yan uban Bajju d'inne Baranzan aka sama k'auyuka da garuruwan.
Suma Katafawa suka kafa nasu k'auyuka da garuruwan kamar irinsu:-
Asha a wuce.
Bakin gogi.
Dama kasuwa.
Mashan.
Unguwan wakili.
Gora Bafai.
Samarun Kataf.
Zangon Kataf.
Da sauransu da sauransu.Amma duk da haka Kajawa da Katafawa(Bajju da Atyap) masu yawan gaske sun zama musulmai iyaye da kakanni,suna kuma musuluncin da gasken-gaske,d'aya daga cikinsu Maryam Gid'ad'o Idris, inda tazo garinsu Samarun-Kataf tagina asibiti, masallacin juma'a da makarantar addini me suna
(HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF)
Musulman wannan yanki Hausawa da Fulani sun amfana kwarai da gaske da wannan makaranta wanda ta sanadiyyarta suka fara halartar gasar Musabak'ar Alqur'ani me girma ta Jahar Kaduna,dan manyan malamai masu addini tad'auko daga Bauchi da Adamawa,sai wasu daga garin Samarun-Kataf,da Zangon-Kataf da Zonkwa, sune suke koyarwa.
Shekaru masu yawa sun shud'e, an cigaba da mu'amala cikin kwanciyar hankali kowa yana neman kud'inshi lafiya lau.Wannan kenan atakaicen takaitawane.
Doctor Julaibib Abdullahi D'ansarai asalinshi d'an D'ansarai ne,k'auyene dake k'aramar hukumar Malumfashi a Jahar Katsina,suma a wayansu suke saboda ilminsu,shi k'wararran likitan mata da k'ananan yarane,yayi aiki a jahohi biyar daga nan gwannati ta turoshi wannan gari a matsayin babban likitansu,garin yama Doctor Julaibib dad'in zama shida Iyalanshi,yayanshi guda uku suka cigaba da karatunsu,suma sauran yan'uwa na D'ansarai duk wanda yazo dan ziyara sai garin yamishi dad'in zama dan haka sai yanemi canji aiki yadawo nan da iyalanshi suyi zamansu,da haka danginsu na D'an sarai suka dawo Zonkwa gaba d'ayansu aka cigaba da hayayyafa.
bayan ya gama aikin aikin gwannati (retired) Sai bai koma D'ansarai ba,yan'uwa da zai koma ko dansu to suna zaune anan,yagina k'atan gidanshi yacigaba da rayuwarshi a haka har Ya'yanshi suka girma sukayi aure,da matar d'anshi Bishir ta haihu sai Bishir yama Babashi kara yasa sunan mahaifin Doctor Julaibib wato Abdullahi.Ai ko Dr.Julaibib yaji dad'in wannan kara dan haka yad'auki san duniya yad'orama Abdullahi,kome nashi na Datti ne kamar yadda yake kiranshi,Abdullahi ya taso cikin gatan daya zarce na duk sa'anninshi.
zai shiga aji d'aya a secondary ALLAH yama Doctor Julaibib rasuwa mutuwar data dakesu sosai,sannu ahankali kuma zafi da rad'ad'inta yanata raguwa,kafin matarshi tagama idda itama tace ga garinku nan.
Mahaifansu suka cigaba da kula dasu.koda yagama Secondary sai yafad'ama mahaifinshi yafi sha'awar kasuwanci fiye da cigaba da karatun boko,mahaifinshi yayi na'am da hakan duk shi d'an boko ne ma'aikacin gwamnati, yace kowa da abinda yake sha'awa a rayuwarshi, idan aka hana mutum abinda ya keso to an shiga hakkinshi, sai dai idan abinda ya keso d'in shari'a bata yadda dashi bane.Yakawo kud'i masu tsoka yabashi tare da mishi addu'ar ALLAH ya sanyama kasuwancin na shi albarka.Haka rayuwa tacigaba da tafiya kamar yadda tasaba har suma mahaifan nasu suka kwanta dama.
Alhaji Abdullahi dattijon arzik'ine, matarshi ta aure guda d'aya da albarkan ya'ya uku, Karima,Asma'u da kuma autansu Julaibib da suke kira D'ansarai,musamman mahaifinshi.Alhaji Abdullahi yanaji da Julaibib sosai dan bai manta gata da soyayyar da Dr. Julaibib ya mishi ba.
Julaibib ya taso cikin tarbiyyar musulunci,ALLAH sai yatarfama garinsu nono yarone me jin magana,duk yadda iyayan nashi suka d'orashi a haka yataso.Yana gama secondary yasamu gurbin karatu a Kaduna State College Of Education(KSCOE)Gidan-Waya,shida abokinshi kuma d'an uwanshi Musaddiq.Duk wata d'awainiya ta karatun Alhaji Abdullahi ne yayita ba tare da mahaifin Musaddiq kuma Kawu a wajan Julaibib d'in ya bada ko sisin kwabo ba.
Alhaji Ibrahim shine aminin Alhaji Abdullahi tun zamanin k'uruciya abin kuma bai rusheba har girma,Alhaji Abdullahi shi yaga kanwar abokinshi yace yanaso itama ta amince aka d'aura musu aure.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Ibrahim Me-Lambu shine tushensu Alhaji Ibrahim,dan haka Ya'ya da jikoki da Ya'yan jikokin gidan suna amfani da Me-Lambu a k'arshen sunayen su na makaranta,wasu ma da wane ko wance Me-Lambu suke amfani.Ibrahim Me-Lambu ya samu sunan Me-Lambu ne saboda sana'arshi ta saida kayan lambun kamarsu:-tumatur,tattasai, albasa, alaiyaho,yalo,latas, karas,lafsir da sauransu da sauransu.
Asalinsu yan k'aramar hukumar Tsanyawa ne ta Jahar Kano.Cirani yakawosu garin Zonkwa Iyaye da kakanni,dad'in garin da kuma k'addarar ALLAH inda ya rubuta maka zama to ba makawa anan d'in zaka zauna kome dad'i ko rashin dad'in waje,da suna zuwa ganin gida daga baya suka daina sai kalilan daga cikinsu dan suna da yawan gaske a Zonkwa,wasuma basu da sauran dangi na jini a Tsanyawa,Unguwa gudace dasu k'atuwa ta musamman da ake kira"Lungun Kanawa.Sukayi zamansu a nan suka hayayyafa.
Alhaji Ibrahim matanshi na aure guda biyune,Mama itace uwargida kuma mahaifiyarsu Musaddiq,Khausar,da sauran kanninsu maza da mata.Sai Umma mahaifiyarsu Aminu,Adnan,Sudaida da tarin kaninsu maza da mata.Kan ya'yansu a had'e yake saboda matan sunada fahimtar juna,mijinsu kuma yana musu adalci dai-dai iyawarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿
Julaibib yana zaune atsak'ar gidansu yana nazarin wani littafi duk da wancan makon suka samu hutu.Musaddiq yashigo da sallama,yad'an daki kafad'ar Julaibib "Haba malam an samu hutu kaima ya kamata ka hutafa"Julaibib yayi kamar ba dashi yake maganaba.Musaddiq ya jijjiga kai"gaskiya na gaisheka"yawuce dak'in Inna, tana zaune a inda ta idar da sallar walha,sai yasaki labulan"to barinje na dawo anjima".Daga ciki ta amsa"shigo ai na idar.Yazauna suna gaisawa,sai yafara mata hirar Safiyya budurwarshi da sak'on data bashi yakawo mata.
Aminu shima yashigo da sallama yana fad'in shi wai D'ansarai baya gajiya da karatune Inna?Yakama ha6arshi da hannun dama"Tabbb ina ruwan Alhuda-huda,koda yake bazai gajiba tunda yafi sha'awar zaman gida, gaskiyar magana wannan da macece da sai ince ALLAH ya kashe ya ba mijinta kakarshi ta yanke saka wallahi.Inna takalleshi"kamar yaya?Yawaiwaya inda Julaibib yake zaune"o Inna aishi ya huta da fitinar mata tayawan tambayar unguwa, zani gidan wance,anyi haihuwa zan shiga barka, zanje dubiya dan gidan wance an mishi shayi, muna da biki agabas,gobe suna a arewa,jibi tarewar yar gidan wance a yamma, zani, zani, zanin mata ai bata k'arewa.Inna tayi dariya.
Julaibib yakalleshi ba laifinka bane, ka ci bashi zan kuma rama.Aminu yagyad'a kai"Nima zan so haka,ina nan ina jira,yashige D'akin-girki yad'auko kunun tsamiyarshi yafito"Inna yau naci aikine kamar ba gobe,tun daga sallar asubahi sai yanzu zan koma gida.Inna takalkeshi da tausayi "Wayyo sannu,a lallai ka aikatu neman kud'i makahon aiki, ALLAH dai yak'aro masu albarka.Amin Inna nagode barinje in kwanta.To ALLAH huta gajiya.