← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 74

Sashe 32

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalin Sudaida bai kwanta ba har sai da taganta a Staff-Room agaban tebur d'inshi ta'ajiye littafin ta kuma sa hannu,tafito tana sauke numfaahi"wai ALLAH na! nayadda k'wallan mangwaro na huta da kud'a.Takoma wajan Julaibib yanata kallanta ta gilashin motar yana kissima wani abu a zuci,tad'auki jakarta. Yad'ora hannun damar shi a saman sitiyarin motar"kin ko karya?A ah.Yakalli agogon motar ai da sauran lokaci kafin kuyi assebmbly ko muje Staff-Quater gidan abokina Aminu Idris ki karya a can?Tagoya jakar"barshi kawai Yaya Julaibib,ai Yaya Khausar zata kawomin.Sukayi sallama,yad'an lek'o da kai "kuyi hak'uri yau akwai inda zani dana dawo na d'auke ku"tad'aga hannu tana mishi adabo ba matsala nagode,tabi motar da kallo har yafita daga gate d'in farko sannan tajuya zuwa ajinsu tana murmushi.

Kwanci ta tashi asarar me rai,biki saura wata d'aya,awannan lokacin Julaibib baya samun zama saboda zirga-zirga tsakanin Azare da Zonkwa,Yadad'a gyara bangaranshi dan anan zasu zauna tunda bai gama ginin shiba.Dasafe yaje gaishe da Kawunshi sunata hira musamman abinda yashafi kasuwancinsu,sai da zai tafi yamik'a mishi wasu mukallai na gidan kane,na baka d'aya daga cikin gidaje na na Unguwar-Rama daura da masallacin Yarbawa hakak malak. Julaibib yad'ago kai bayan ya duba takardar shaidar mallakar gidan sunan shinei ajiki"Kawu nagode ALLAH yasa da mafificin sakamakon shi, ALLAH yak'ara girma.Amin.wannan ai ba kome bane.

Yad'auki Musaddiq sukaje suka ga gida,sabone dal sai k'ura dayayi tunda bakowa yasa yara suka wanke lungu da sak'o na gidan.Kafin yakoma Azare sun sa kome da ake buk'ata suka kulle sau ranar daza a kawo amarya.

Yajingina da bishiyar mangwaran k'ofar gidan yana kur6an madarar shanun tatsar lokacin,hirarsu sukeyi cikin nishad'i irin ta masoyan juna.Bilkisu har naji kin fara k'amshin amarci fa.Tad'anyi murmushi.Yayi tsai da idanun shi yana kallanta"Megado baki ce kome ba? Takauda kai"Kazo ka tafi bana so kayi dare a hanya daga nan zuwa Azare tafiyace me tsayin gaske"Megadon bana san tafiya yau "Takalleshi cikin kulawa"saboda me?Yanunata da yatsa.

Tad'anyi luuu da idanunta kamar zata rufesu sai kuma ta sunkwui da kai"Julaibib ai kai nawane,ni d'in nan ta kace Insha-ALLAH,amma bazan so ace nice silar ta6ar6arewar al'amuranka masu mahimmanci ba,bautama k'asa a matsayin ka na d'an bautar k'asar dole ne,kome kuma za kayi to kayishi yadda ake buk'ata,kazama me amana; tafiyarka ai ba itace rabuwar muba,koda munyi nesa da juna to amma ai zukatanmu suna tare,kuma ga waya muna gaisawa,muna chatting, har video call duk munayi,tad'ago cikin natsuwa da kulawa tad'an kalleshi"duk basu wadatar ba D'ansarai?

Yanad'e hannayan shi a k'irji yana murmushi "sun wadatar Megado,ke macen alheri ce da bata taya 6era 6ari.Yamik'a mata kofin madarar yashiga mota yazauna yana d'aura belt "ALLAH yamiki albarka Bilkisu "tarufe mishi murfin"Amin D'ansarai nagode,sukayi sallama. Tabi bayan motar da kallo a hankali yake tuk'in har ya6acema ganinta.Tajuya zuwa cikin gida tana mishi addu'ar sauka lafiya.

Inna tabita da kallo"har ya tafi?Sai lokacin tasan Inna tana tsakar gida,ta zauna a gefan tabarmar tana d'an murmushi,kumatun ta suka lotsa ciki"a kunyace tace ya tafi Inna"sai kuma tamik'e da sauri ta shige d'aki.

Tana shan rake tana 'yan wak'ok'inta cikin nishad'i,Khausar kuma tana karanta wani littafi"The secret of occultics powers"su Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu,A'isha tace ya naganku haka?Khausar takalle su "to da ya kike so ki ganmu? Tazauna a gefan gadon"banga kun shirya ba,za muje ganin d'akin amaryane. Khausar ta ajiye littafin"har kin tunamin ance da mahaukaci baya duka.Tabud'e wadrobe tad'auko hijab sannan takalli Sudaida"to mayyar rake badai za kice jiranki za muyi har sai kin gama shaba?

Tamusu kallan uku ahu"kuyi tafiyarku dan ni bana zuwa gayyar sod'i.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"gayyar sod'i fa kikace? Zuwa gidan Yaya Julaibib d'in?Tayi kamar bataji suba...zuwa can bayan ta shaki iska ta baki ta hanci tafesar tana wani tsuke baki"Eh shi d'in fa wani abu ne?Ni dai wallahi banga abinda zanje gani wanda ban san shiba,ban ta6a ganin shi ba, taja dogon tsaki"gado ne fa da sauran tarkace, tad'ora hannun damar ta a katakon gadan su, wannan ai gadone ko?To gashi na gani akaima nake bacci,sauran tarkacenma muna dasu a D'akin-shak'atawa da D'akin-girki,kuma bama amaryace za tazo da suba,ta kuma jan dogon tsaki cikin tafasar zuciya"kai ALLAH yasauwak'e ma Fulani,wai ace kome mijine zaiyi,ga uban sadaki da suka yanke mai,dubu hamsin sai kace siyar da ita za suyi"ai dai k'arancin sadaki yawan albarkar aure wallahi.

Khausar ta tareta da sauri"ke dakata haka malama ai a addinance dama mijine yakeyin kome na d'aki yakuma biya sadaki,dan hakkin akanshi yake ba akan iyayan taba,mu hausawa mune muka fifita al'ada sama da addini a wannan bangaran,kema ai kin sani sarai ban san abinda yasaki wannan furucin ba.

A'isha ma takalleta"lallai ma yarinyar nan yanzu idan ma siyar da itan za suyi sai su siyar da ita a kud'i me mugun rangwame haka? Dan ALLAH nawa ne 50K? Kai Sudaida me yake damun kine naga alama bakya san

Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o...

Ni kuma wallahi tana burgeni saboda sauk'in halinta,wallahi sam bata d'auki duniya kayan gabas me k'amshin turaran d'an goma ba, haka fa ranan nan da muka had'u da ita a hanyar Islamiyyar su itafa tafara gaishemu amma kikayi banza da ita,bakyau irin wannan halin ko Yaya D'ansarai da baya san kula mutane amma idan kika mishi magana zai kulaki ko sama-sama ne.

Nasmat tana ta nazarin kalaman Sudaida tayi yar dariya tana tafi tasake kallan Sudaida"kina kishi ne?Takusa k'warewa da raken da take sha Dammm... zuciyar ta tabuga tamata wani kallo"kishi kamar yaya,me zai sani yin haka?So...Nasmat ta bata amsa.Duk sai suka zubama Sudaida idanu"biri fa yaso yayi kama da mutum. Numfashinta yad'auke na wucin gadi... tamik'e cikin fushi tana kallan Nasmat "so fa kika ce?Tagyada kai"eh kwarai kuwa so.Sai tafara hayagaga..."eh so ne sai me?Suka kyalkyale da dariya ganin yadda take masifa"eh ina san nashi amma ba irin soyayyar da kike tunani bane, soyayyace irin ta yan uwan taka, karki manta ina da masoyi na da makaranta yake jira in gama sai in koma k'ark'ashin shi ta inuwar aure.

Nasmat ta daki kafad'arta tana dariya "ahaf ba mage ba miyauuu...Takalli su A'isha"kuzo mutafi kunji tunda baza tajeba.Tabisu da kallo har suka gama fita a d'akin.Tad'auki hijab tasa gwamma kawai tabisu,sai wani irin abu mara dad'i ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar ta,kawai sai ta koma ta kwanta,tad'ora tafin hannun damar ta a saman goshin ta dayake barazanar yin ciwo, ta yamutsa fuska tana hura iskar bakinta tana jin wani d'aci kamar tasha mad'aci.

Mama uwargidan Alhaji Ibrahim macen albarka,macen k'warai dattijuwa me yakana da karamci, uwargidan cinta na dalci da amana takeyi,abinda yahaifar da kwanciyar hankali kenan,yasa zuri'ar gidan suka dunk'ule suka zama tsintsiya mad'aurinki d'aya.Duka Ya'yan gidan ta d'aukesu abu d'aya kamar ita ta haifesu.A d'aki tasamu Sudaida a kwance idanun ta a rufe,amma ba bacci takeyi ba.Ta zauna a gefan gadan,Sudaida tabud'e idanun ta da suka d'an canja kala.Mama takalleta da kulawa"wai mantawa kikayi da Sinan a waje?Tadad'a kwantar da kanta a saman matashi "Mama kaina ne yake min ciwo"sanin hali yafi sanin kama"sai tayi murmushi kawai"To ai ya kamata kije kifad'a mishi kar yayi jiran gawon shanu ko?A ciki ta amsa kamar ranta bai mata dad'i ba"to Mama na ji.

Tana fitowa yatareta"Sudaida Sarauniyar Sinan"taturo baki gaba tana d'an harararshi"kai baka san kaina ne ya dameni da ciwo kuma Mama ta matsamin dole nafito"yayi murmushi wani lokaci haka take abu kamar wata 'yar k'aramar yarinya wai an matsamata dole tafito.Sai ya marairaice"Oh ALLAH! Wayyo! Sannu Sarauniyar Sinan taso muje ki kar6o magani? Tagirgiza kai'ai ma navfara jin sauk'i.Yasauke numfashi"kai nagode ma ALLAH,dama ni ne maganin ko?Sukayi dariya.

Tana d'ago kai za tayi magana caraf idanun su yahad'u dana Julaibib,yana sanye da shadda ruwan k'asa yayi shar...shar dashi,magana yakeyi a waya yaja yatsaya nesa dasu.Tad'an ta6e baki"wayar tak'ici tak'i cinyewa,ba mamaki shi da wannna Bafulatanar ce.Yagama wayar sannan yamata wannan rikitaccen kallan da tadad'e bataga ya mataba,dama baya kulasu in dai yatarar suna hira ko magana tamishi sai yayi kamar ba dashi take yi ba"kunnan uwar shegu"tabishi da kallo har yashige cikin gidan.Takalli Sinan ni zan wuce"Shikenan anjima zan bada masoyin Sarauniyar Sinan akawo miki (rake) tayi d'an murmushi "nagode.

Ranar Juma'a suna gidan Yaya Karima sunje mata ziyara sai gashi yashigo da sallama.Yazauna suna gaisawa da Yaya Karima tana tsokanar shi"Kai autan Inna har wani haske naga ka fara ko kaima kana gyaran angwancinne dasu halawa da dilka?Yakai hannu yana sosa k'asumbarshi yana yar dariya"Kai Yaya Karima duk sukayi dariya;banda Sudaida da ta tayi kamar bataji me aka fad'a ba,tacigaba da cin sinasir d'inta,Nasmat tace"wai ina masar Bauchin dana ce ka kawomin tsaraba?Haba ke kuwa Nasmat ai k'aton aiki za ki bani ace tun daga Bauchi har Zonkwa in rik'o masa?Gaskiya bazan iyaba,indai za kici kantu(rid'i)to kije wajan Inna ki kar6a.

Ni masa nake so tunda baka kawo min ba ai shikenan nagode ALLAH kuma yabamu lafiya, amma da Bilkisu ce tace tana san masar ai baza ka d'auki hakan a matsayin k'aton aiki ba ko? To dake da Bilkisu Megadon Zinare...d'aya ne? Sudaida tamik'e"uh wannan Bilkisun dai ko gadon Mahogany ba ta dashi"tajuya za ta bar d'akin. Yarik'o gefen hijab d'inta..kafin yayi magana tajuyo cikin fushi"Yaya D'ansarai sake min hijab ka san dai bana wasa da maza.Su Nasmat suka kyalkyale da dariya kaji wata magana kuma? Yakalketa cikin natsuwa"idan kuma ban sake ba fa?Tayaye hijab d'in gaba d'aya daga jikinta tajefa mishi a fuska "kaje ka kai mata"fuuu...tafita mayafin Yaya Karima tajawo a igiya tayafa.Duk suka bita da kallo.Yaya Karima takama ha6a"to ana wata ga wata aure ya mutu ga gara.Takalli Julaibib ya sunkwui da kai"ranshi a 6ace yake,amma ta san bazai yi magana ba tunda yayi haka,wannan halin shine tun yana yaro indai ya sunkwui da kai.

Yamik'e da hijab d'in a hannun shi "Yaya Karima ni zan wuce idan Baban Abdul yadawo kya mik'a min sak'on gaisuwa.To auta mungode kwarai kagaishe dasu Inna sai na shigo.

Har yakoma Azare Sudaida bata yadda sun kuma had'uwa ba ko gidan Inna bata sake zuwa ba dan kar ma su had'u sai bayan data tabbatar ya tafi sannan taje.Yakirata sau d'aya a waya tak'i daga wa shima bai sake kira ba.
Chapter 32 · 0% Book details