← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 74

Sashe 26

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baban me fara'a ne shi yadinga jan su da hira har dai suka saki jiki.Suna cin abincin da Hafsa ta girka musu yau an hutashshe da Kawunta.Dinatu tahigo gidan cikin kwala kiran sunan Kasham...Kasham... Kasham..

Sumayya ta cire hannunta a abincin tana Istirja'i kafin tashigo Sumayya ta mik'e, a k'ofar d'akin sukayi kaci6is,takalle ta sama da k'asa sai tayi murmushi"Hail Mary...tarungume ta.Sumayya ta rintse idanun ta tana jiran saukar dundu a gadan bayan ta amma bataji hakan ba, har suka saki juna tana dad'a k'are mata kallo, wani kyau da annuri na musamman tayi"Sannu Kasham tad'an dafa kafad'arta"na ji dad'in ganin ki suka shiga d'akin takalli Alhaji Hafiz"Sannu Shedrak shima ya canja mata gaba d'aya to yaushe raban data sa shi a idanun ta shekara da shekaru yayi kyau mijin ta kuma ya tsufa sai yaza kamar shine gaba da Shedrak.Suka shiga gaggaisawa.Ranar dai suna cikin farin ciki musamma Dinatu ganin duk wanda yazo musu sannu da zuwa sai ya yaba irin kyan da Kasham tayi kamar wacce take zaune a wata k'asa,kowa na so yaga na shi cikin wadata.

"Lallai zaman Kaduna ya miki dad'i.Inji Lidiya.Sumayya tayi lallausan murmushi"kawai kishirya kayan ki mutafi.Tagalla mata harara"ai ko da kikayi wannan kyan banga abinda zai rud'eni in bar addinina ba.Itama ta galla mata harara"a ina kike da addinin?Kina da maraba da pagan ne? Kasham kar fa ki zageni.Sumayya tasake yin murmushi"come on Lidiya ni dake ai mun san gaskiya ko dan kawai d'aci gare ta?Ba fa yau na sanki ba,na sanki farin sani kamar yadda kika sanni farin sani,ranar Lahadi kina zuwa majami'a? Sai ta mik'e cikin borin kunya"bana zuwa kuna bazan je ba sai kiyi abinda za kiyi dani.Tafice fuuuu tana surutai rubbish girl...tabita da kallo haba yarinya ba abinda zanyi dake,za kuma ki dawo ne da k'afafunki.

Sumayya tasa mu Maman a d'aki, ta tazauna akusa da ita sannan tafara rok'on ta "Mama dan ALLAH kiyi hak'uri kiya femin laifin dana yi, na san da ciwon haka azuciyar ki.Cikin fushi ta kauda kai"bazan yafe ba ki tashi ki bani waje.Haba Mama kiyi hak'uri kisa min albarka,ai har kwanan gobe ina sanki ina alfahari dake a matsayin mahaifiya,dan kinyi d'awainiya me yawa akaina tun ina cikin cikinki har kika haifeni, wallahi bani da abinda zan biya ki dashi.Tasake tuno girman hakkin Y'aya akan mahaifansu musamman uwa da addinin musulunci yazo dashi kaico! Wanda ba ya cikin musulunci wallahi yana cikin duhu me girma, inama-inama tana da wani iko!? Da ayau d'in nan kowa na ta sai ya zama musulmi.

Takoma hannun ta Maman ta fizge da sauri"ke sakar min hannu mara jin magana kawai"kiyi hak'uri Mama na miki alk'awari bazan sake 6ata miki rai har kiji ciwon hakan ba Insha-ALLAH matuk'ar bai sa6a ma addinin musulunci ba.Tamata kallan uku ahu"Shari'a law" bata amsa ba tafara kuka haba Mama yanzu bazaki yafe min ba?Duk duniya bani da kamarki fa(In the whole wide world)

Takalleta cikin fushi"kin san da haka amma nace kar kiyi sallah sai kika gudu wajan Shedrak har kina min k'arya wai an ma Tina Operation?Tagirgiza kai"gaskiya ban yadda ba kin nuna min Shedrak ya fini.Ba haka bane Mama. Tasake galla mata harara"to yaya ne? Tamarairai ce"Mama tafiya ta Kaduna wajan Uncle da duk abubuwan da suka biyo baya"It's a destiny (K'addara ce) suka kalli juna Sumayya tajijjiga kai "Ki yadda dani Mama wannan k'addara tace daban isa in kauce mata ba no matter how,kuma ai gwamma tawa tafiyar sau dubu tunda gashi na dawo a cikin hayyaci, koshin lafiya da kwanciyar hankali kuma kowa ya yaba,yayi sam barka to ai ko Alhamdulillah.

To amma Mama Judith fa...? ran Maman yak'ara 6aci Sumayya tacigaba"Judith ta tafi amma bata dawo a cikin hayyaci, k'oshin lafiya da kwanciyar hankali ba, kuma kowa tirrr... da ALLAh wadarai yakeyi daganin ta, ba kuma wanda yakuma damuwa da ita sai ku.Ba aure tayi ba fornication shine sana'ar ta" which is forbiden"ba addinin daya yadda da hakan Islam ko Christianity sai dai san zuciya kawai,san zuciya kuwa 6acin ta yau ga Judit a ciki kuma Mama...ta tare ta dasauri ya isa haka Kasham jikinta yayi sanyi duk irin alwashin data d'auka ranar duk da sukayi ido hud'u da Kasham sai ta nemi shi tarasa,gaskiya Kasham tafad'a sai ta rungumeta"naya fe miki kome ALLAH ya albarkaci auran ki, wancan d'in shine Julaibib?Tagirgiza kai tana murmushi"ba shi bane.. taba ta labarin duk abinda yafaru da ita bayan barin ta gida.

Tazuba mata idanu"to ni me zance miki Kasham? Sallah ne dai kin riga kin fara kuma ko na ce miki ki daina na san bazaki daina ba, kuma ma ban miki adalci ba,tunda duk a cikin Ya'yana dana haifa daga ke sai Rahab da Bitrus kune kawai masu jin magana, kune kuka maida hankali a karatu gashi nan kuma kune rayuwar ku tayi kyau,yanzu Bitrus shine personal manager a Bajju Community Bank(BCB) Rahab ta gama karatunta har ta fara aikin ta a asibiti, anjima kad'an za ta dawo gida tunda aikin rana wannan makon takeyi,ke kuma gashi kinyi aure hankalin ki akwance kuma kina cigaba da karatu.Rahab d'inma ta kusa yin aure.Sumayya tana ta godema Ubangiji daya sauk'ak'a kome fiye da zatan ta, tasaki jiki sunata hirar yaushe gamo suna kyalkyala dariya "Da da mahaifa sai ALLAH.

A babban D'akin-shak'atawar gidan suka yi jam'in sallar su saboda k'auyan gaba d'aya ba masallaci tunda babu me sallah.Suna jam'in sallar Isha'i Rahab ta shigo da d'okin ganin Kasham dan tun a hanya tasamu labarin zuwan su, d'agowar su daga ruku'u Rahab ta tafi zata rungume ta Maman ta dakatar da ita"Ke Rahab karki ta6a ta baki ga sallah suke yiba?.Taja da baya da sauri"Oh Basakut"ta tuna idan suna sallah ko magana basa yi.Tajingina da bango tana kallansu"yadda suke tsayuwa,suyi ruku'u su d'ago, su tafi sujjada,su d'ago,su sake komawa sujjada suyi zaman tahiya har zuwa sallama kowa yafara karanta azkar d'in bayan kowace sallar farilla.

Cikin murmushi tajuya wajan Rahab. Rahab takama ha6a cikin mad'aukakin mamaki tayi tsalle ta rungumeta tana ihun murna Jesust Christ Halelujah"Kasham kece kika zama wata big madam?What a suprise, ta daki kafad'arta"tell me the secret.Sumayya tashafa wajan"gaskiya fa akwai zafi"suka kyalkyale da dariya.Rahab ai kema kin canja kinyi kud'i fa"mint note"suna shiga asusun ajiyar ki duk k'arshen wata suka saki juna. Rahab tasake binta da kallo daga sama har k'asa gaskiya canjawar da nayi ba irin wacce kika yi bace"wonderful"tashafa kyakkyawar fuskar ta data ke ta hasken musulunci da Imani"wannan irin kumatu da kika fara ajiyewa ga fari, ni dai ko shafa man sa fari kika fara ne?(bleaching)Ba Sumayya ba hatta sauran sai da sukayi dariya dajin yadda Rahab taketa kod'a ta.Tazauna suka gaisa d'aya bayan d'aya take tamabayar Sumayya sunayan su.Salim yabisu da kallo ga dukkan alamu suna san junan su suna da kirki dama Sumayya tafad'a mishi Maman suce kawai sai a hankali to itama bata nuna kome ba banda farin ciki da ganinsu.

Sumayya,Hafsa,Zainab da Rahab su suka gyarama Judith jiki da d'akin dayake ta k'arni kudaje sai budiri sukeyi,tana kwance cikin hawaye"wallahi da ace zan warke babu abinda zai hanani binku Kaduna in zama musulma.Hafsa ta amsa da sauri "ai ba dole sai a Kaduna ba, ko yanzu za ki iya k'ar6an musulunci.Wani dad'i yakama Sumayya.Ki yadda ki amince kina da rabo ne. Judith ko baki warke ba ALLAH zai kar6eki a haka Tagirgiza kai "uh uh ku kyaleni kawai dan bazan iya sallah ba tunda k'arfina ya riga ya k'are.Sumayya takalleta cikin natsuwa"ai addinin musulunci sauk'i gare shi Judit, ba dole sai a tsaye ko kina da k'arfi a gangar jiki za kiyi sallah ba matukar akwai lalura ko a yadda kike akwancen nan akwai yadda za kiyi sallah.

Rahab tagalla musu harara sannnan taja dogon tsaki"addinin ta'addancin kike sha'awa Judith?Tamik'e a zuciye zata bar d'akin Sumayya tarik'o hannunta.Rai a 6ace tace "malama sakarmin hannu kishiga hankalin ki fa.Tagyad'a kai sannan tasake kallan ta ckin natsuwa"to kiyi hak'uri kizauna magana za muyi Takoma ta zauna fuska a yamutse.Shiru ya ratsa d'akin na wucewar wasu dak'ik'u. Tad'ago kai a zuciye"bana san wawanci fa, ke nake sauraro kin kuma yi shiru.To ai naga ranki a6ace yake shi yasa nayi shiru har sai kin d'an huce karr in k'ara miki zafi.Tamik'a mata lemon biyar a raye(five alive)d'an jik'a mak'oshin ki mana.Kasham I'm I your toy to play with?Tayi yar dariya "absolutely no kiyi hak'uri, amma ina so ki sani addinin musulunci ba addinin ta'addanci bane,addinin sauk'i da salama nw ga mabiyanshi.Tawatsa hannaye "ahab...ba cinya ba k'afar baya"ko d'azuma abinda wani musulmin ku Adam yagama fad'a min kenan awajan aiki.Nidai banga dalilin da zai sa inyi sallah ba,ina da yanci bazan koma inda bani da wani yanciba.

Zainab ta tareta da sauri"ai ko addinin musulunci shine yabaki cikakken yanc me lasisi ma, musamman a matsayinki na 'ya mace,kina da yanci kamar yadda namiji yake da yanci,sai dai mu addinin mu, duk da yancin daya k'wato mana ya nuna mana namiji shine a sama da mace,idan banda addinin musulunci wa yake girmama 'ya mace ne?

Rumawa da suke kiran mace"Devil" shaid'aniya? Wai mace shaid'aniyace ana neman tsari da ita kamar yadda ake neman tsari da shaid'an.

Persia su kuma sun d'auki mace wulak'antacciya k'asa da duk wata halitta wulak'antacciya.

Yahudawa su kuma sun d'auki mace kamar baiwa,da zatai tama namiji hidima, ita kuma ba ta da wani hakki akan namiji

Zamanin jahiliyyar larabawa kuma idan aka haifi macen sai ma adinga zuwa maka jaje kai kuma kana 6uya,amata rik'on wulakanci,ko kuma tanaji tana gani da ranta da lafiyar ta a tona k'asa abinneta.

Wanne daga cikin wad'annan suka ba mace yan cinta?
To a duniyar musulunci da gidan musulunci ne kawai mace take yar ga ta,yar lele, sarauniya kome yi mata ake yi,kome kud'in ta k'wandala na ta na k'ashin kan ta sai ta ga dama za ta kashe.Duk masu yeekuwar yan cin mata indai ba wannan da addinin yabasu bane to wallahi k'arya ce,haushi suke ji, suna so ne ku fito ku sha wahala.
Chapter 26 · 0% Book details