← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 74

Sashe 10

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tadafa kafad'arta ki tayani addu'a duk ranar da ALLAH yabani sa'a yashiga nan ta nuna tsakiyar tafin hannunta,yad'and'ani zak'i da gardin zuma ta,to wallahi na mishi katttt...kisan mummuk'e.Lidiya ta kyalkyale da dariya"gaskiya iska tana wahalar da me kayan kara,malama dame kama ake yin k'ota.Wancan me shegen girman kanne kike tunanin za ki yaudare shi?To yaushe ma yatsayi kulaki bare har hilarki tayi aiki akanshi? Wallahi kinga dai bana san shi amma na jinjina mishi 👍zan kuma iya bada shaidarshi harkar mata baya yinta, dan da yanayi wallahi ko sau d'aya ne tun zuwanshi Gidan-Waya da mun sani,kema ai kin san mune idon gari a makarantar nan,wannan harkar sai sojanki Namamajo,ke dai kawai ALLAH yaganar dake,amma banda 6atan basira mutum yace baya sona to nima banga abinda zai sa ya kuma d'ad'ani da k'asaba tunda shi d'in ai ba mahad'in numfashi na bane,ko yaranmu d'aya dashi zan hak'ura in kyaleshi,bare wani hausawa me girman kan tsiya,shiba kowan kowaba dillalin kashi,kin sani ni nak'i jinin hausawa, ke ba hausawa kad'ai ba duk wani me sallah bana sanshi da inda k'arfin iko na rantse miki da ALLAH ba wasu tsinannun masu sallah dazasu zauna mana a gari.Taja tsaki fuskar nan tarine da 6acin rai ruwan kafircine zallah babu gauraye da haske da tausayi da Imani ko na sisin kwabo, jikar kajawace (Bajju) gaba da baya"bana san ma su sallah.Kuma ba yadda za kiyi dasu "sun zama kuturwar uwa dole a zauna dake.Kasham tabata amsa,sannan tasauko akan mashin d'in tawuce bayan aju-juwa da aka k'awata wajan da shuke-shuken filawowi masu ban sha'awa,tadinga bi tana tsinkosu kaloli mabambanta masu k'amshi tacika hannunta sannan tasa zaran ulu,ruwan hoda tadaure tawuce d'akin malamai zaman jiranshi.Dak'ik'a biyar da buga k'ararrawar canjin darasi sai ga shi yashigo,saida tabari ya zauna a kujerarshi yana hutawa ba ajin dazai kuma shiga sai gobe.Yakwantar da kanshi a jikin kujerar, idanunshi a rufe wani bacci me dad'i yafara shirin saceshi sai kawai yaji an shafa mishi wani abu a daidai hancinshi me wani irin k'amshin dad'i, yabud'e idanunshi da yanayin bacci har sun d'anyi ja.

Tamishi lallausan murmushinta "perceive the natural fragrance of this bounch of flowers.Tafurta hakan da wani salo irin na ta nayanga sannan tacire daga hancinshi ta d'ora mishi a saman tebur.Yakauda kai daga kallan da take mishi kamar kura taga nama.Wallahi yama rasa abinda zai ce mata.

Tayi k'asa da murya ganin wasu malaman sun fara sa musu na mujiya"ai nasan ban kyauta maka ba ko?Kai dai ba a maka gwaninta,d'an motsa kafada tayi "karka damu dani,kar kayi la'akari dacewa nice nakawo maka,tagirgiza kai kayi la'akari kawai da tarin amfanin da k'amshin furen filawa yake dashi ga d'an Adam.How I wish Jualiabib ka bani dama na nuna maka irin kaunar danake maka, tagirgiza kai cikin damuwa "How I wish ka tallafi zuciyata ka magance min damuwar cikinta...sai dai kash!Ban samu hakan ba,saboda baka san illar kaso a k'ikaba,tabbas daka san haka da baza kabari zuciyata tayi gobara ba.Tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya "Don't let the love that I have for you to go in vain please...!

Yad'ago yakalle ta,sai yaji wani abu ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar shi,har ya bud'e baki zayi magana sai kuma yagirgiza kai"a ah Julaibib daure kawai, maganin kar ayi to tun farko kar a fara"kawai sai yamik'e yabar d'akin.

Shunkut ya sunkuyo a fuskarta yana murmushi"Ke ki hak'ura dashi mana ai ba a soyayyah dole, yanuna kanshi da yatsarshi"ni d'in nan namiji ne duk abinda yake dashi namazan taka nima ina dashi,kiyadda kawai muyi soyayyah.A fusace ta tureshi"you fool! dawa za kayi soyayyah Shunkut?Tayi d'as da yan yatsunta over my dead body.Tagalla mishi harara sannan taja mummunan tsaki"ruwa ai ba sa'an kwando bane"sai yajuya yana tafiya "Amma kuwa za kiyi 6atan 6akatantan...

A gajiye lik'is yashigo,gidan shiru dan Inna tana gidan Hajiya,yazauna yana hutawa, ya6alle botiren gaban farar rigarshi,yamaida kanshi jikin kujera tare da lumshe idanunshi sassanyar iskar bayan la'asar tana ratsashi. Mafarkan da kwana biyu nan yakeyi sun tsaya mishi a rai"Kasham yake gani cikin kyakkyawan kirar kalangunta,sanye da kayan fulani,gashinta yasha gyara ta tufkeshi a baya,amma kuma idan tayi magana muryar Sudaida yakeji"ya rasa kan wannan mafarki.

Hayaniyar shigowarsu Kamila yasashi bud'e idanunshi,aiko suka shigo sunata zuba surutunsu, sunata mishi tambaye- tambaye.Shigowar Musaddiq yasa suka koma tsakar gida suna wasannin su,yadaki kafad'ar shi"kai malam tashi da ALLAH magana nazo muyi. Uhun ina jinka.Musaddiq yabishi da kallo"Julaibib ka nemi A'isha kawarsu Sudaida mana tunda dama ta nuna tana sanka kaine baka bada goyon baya,tana da hankali kuma ko su Baba idan sukaji ita kake so za suji da...yatari numfashinshi a hasale "bata min a matsayin matar aure ba,dan haka akai kasuwa".Yakalle shi da mad'aukakin mamaki"To me yayi zafi da har idanu za suci wuta haka? Tagyada kai "To yayi,indai har A'isha bata maka a matsayin matar aure ba to ashe gulmace da kai,kana kuma kallan mata za kuma ka iya za6a,amma da zarar magana ta tashi sai kace ba sa gabanka,to kuma harsu Baba sai sunji zancen nan.

Yanunashi da yatsa"Idan kai zaka min zaman auran ai sai in aureta.Yamaida idanun shi ya rufe, shi wai ma wacece wata A'isha?Wasu lokutan dai Sudaida tana fad'a mishi"A'isha tace tana gaisuwa"ko kuma A'isha tace kaza da kaza game kai,sai dai bazai iya tuno me take fad'a d'inba, dan ba itace a gaban shiba,shi dai bai san tana sanshi ba,dan ko Sudaida bata ta6a fad'a mishi wai A'isha tana san shiba, kila Musaddiq d'inne kawai yake san had'awa.

Sallar a zahar Julaibib yayi yagama azkar d'inshi sannan yafito daga masallacin makarantar,yau ba ayi wani karatun kirkiba saboda Inter-House ya kusa,ga dalibai nan sunyi rukuni rukuni na irin abinda suke so, suke dad'a yin gwaji (practice)yajingina da bishiyar giginya tare da rungume hannayanshi a kirji yana kallan Sudaida yadda take d'aga mulmulallan bak'in k'arfen discus da yadda take jefashi cikin k'warewa da nishad'i a bokan wasanta suna mata tafi wasu suna mata ihu dan tanayi yadda yakamata.Yayi murmushi yatuna lokacin da yake makaranta yayi wasannin kala kala,wasan kwallo ne bai ta6,a burgeshi ba wannan sai Musaddiq,saboda kwazanshi a fannin wasannin shine yarik'e shugaban wasanni na lokacinsu (Game Prefect) yakalli Khausar sune yan Javelin, Nasmat kuma ana bangaran Long jump. Yabar jikin bishiyar yana tafiyarshi cikin natsuwa har yaje Staff-Quater zai kar6i wasu littafai a wajan Mr Julius.

K'arfe uku tanayi yasake komawa filin wasannin da Nasmat yafara cin karo yace"Ke idan ba zaku tafi gida bane ni kunga tafiyata.Dan ALLAH kajiramu barin kirasu tayi cikin filin da dan gudunta.

A mota suka sameshi ya musu wannann rikitaccen kallan nashi Sudaida tabud'e baki za tayi magana yanu nata da yatsa"kul naji bakinki.Tad'an harareshi ta zauna tana turo baki gaba.Yaja tsaki"kunje kun shagala da wasanni ko sallar azahar ma baku yiba ga la'asar ta kusa,kufa kuna da ka'ida da bambanci tsakanin ku da wad'anda dama basu san kome ba sai duniyar, wallahi idan lokacin sallah yayi banga mutum a masallaci ba gobe...yayi kwafa, Nasmat tace"shi fa wannan Game Master muguntar shi har tafi ta Discipline Master.Ke tafi can shi ai ba makaho bane yana ganin k'atan masallaci ai a makarantar,na kuma tabbata da kun fad'a mishi sallah za kuyi bazai hana kuba,ai kowa ya san duk inda musulmi yake ba a rabashi da sallah,sai dai in sallarce bata dame shiba...Yaya D'ansarai... yatari numfashin ta"ke ba nace kar inji bakin kiba?Tasunkwui da kai"wannan mutumin wallahi yanada matsala,tafad'a a zuci,tad'anja tsaki. Nasmat takalleta"ke Sudaida tun d'azu kiketa k'unk'uni abin harda jan tsaki ke da wa? Shiru ma amsace.

A k'ofar gidansu yatsaida motar bai k'arasa dasu gidansu kamar yadda yasaba ba,yakashe motar yafito yashige gida.Sudaida itama tabud'e bangarenta tafito tana masifa"aikin banza sammakon gaida makiyi,aiko ba a motarka zamu dawo gida.

Aminu yana hangota yafara dariya"ke fa Sudaida naga alama raguwa za a yi.Ta turo baki gaba "Yaya Aminu me nayi to? Kinga fuskarki kuwa?Gaskiya yunwar makaranta ba ta dad'i har na tuna lokacin da mukayi makaranta a Bauchi.Yad'an kalleta kinsan yau me su Mama sukayi a gidan? Tagirgiza kai "Tuwon shinkafa miyar shuwaka"Sai kawai tad'ora hannayenta aka"Wayyo ALLAH! ni gaskiya yau ana ta 6ata min rai.Suwaye suketa 6ata miki rai?Takaryar da kai gefen dama ta marairaice "Yaya D'ansarai da su Mama,wallahi gidan Hajiya zan tafi ina canja kaya,dan bazan mutu da yunwaba.Yamik'a mata wasu nannad'ad'd'un carbon paper,Top-bond,babban pensir HB dawasu k'ananan tarkacen zane-zanenshi(Artistry Euipment) to tafi min dasu gida,yanzu haka Bakin Gogi zan tafi wani aikin signboard zanyi.Tasa hannu biyu takar6a "Yaya Aminu ALLAH yatsare.Amin Sudaida suka daga hannayensu suna ma juna adabo,sukayi murmushi sannan kowa yajuya yacigaba da tafiyarshi.

...Dare da rana suna aiki tuk'uru a kanmu,to muma kamata yayi mu zage dantse muyi aiki tuk'uru a cikinsu.Ubangijinmu kabamu rabo me amfani fid-dunya wal aakhirah.

21 Rabi'a Thani 1441
18 December 2019

We Ibrahim' Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta'in

...GWAJIN DAFI💔

Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Shafi na shida.

Da yammacin juma'a jikokin Hajiya sun cika gidan,tun daga zaure za ka fara jiyo hayaniyarsu sun tasata a gaba da shak'iyanci. Sudaida da Nasmat suma suka shigo,suna k'are mata kallo tasha had'ad'd'an leshin auduga ja da k'ananan fararan duwatsu,wuya,hannayenta, da d'an kunnanta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi. Suka kalli juna suka k'yalk'yale da dariya"Hajiya manya wannan irin cakarewar k'uda a gefen gyambo?inji Nasmat. Sudaida tagyad'a kai "Gaskiya kin had'u saura had'uwarki da ALLAH, wannnan k'ure adaka haka?To dawalakin goro a miya,bazawarin tane zai iso da yammacin nan. Gaba d'ayansu suka kuma k'yalk'yalewa da dariya, abinda yahanasu jin abinda Hajiyar take fad'a.

Aminu yashigo sai suka sa ihu da tafi "Yehhh... gashinan, gashinan shine bazawarin data k'urema adaka.Yakama ha6a🤔 wai wai wai, ai kowa ya san Hajiya ba dani take yiba,dan ta san ni bazan juri al'alarta na bani bani kamar mak'ogwaro kullum a bashi ba,bani da wannan hak'urin,kusa idanu anjima kad'an za ku ganshi. Khausar tace Alkasim ne.Aminu yace gajan hak'urine dake koma wanene za ku ganshi. Yamatsa wajan Hajiyar suna maganarsu.
Chapter 10 · 0% Book details