← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 74

Sashe 5

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sha d'aya da rabi a sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar asabar aka taso su daga makarantar allo, tana sanye da bak'ar abaya da farin hijab,da wasu littafan addini a jakar data rataya a kafad'a,allanta kuma ta rik'e a hannu.Suna zaune a dogon dakalin tazo tawuce kamar bata ganshi ba. Yamik'e da sauri yabita"haba ranki yadad'e Sudaida Sarauniyar Sinan,me yayi zafi haka idanu suke cin wuta?Takalleshi da 6acin rai"wai dan ALLAH kai baka da wajan zamane sai a cikin yan maro (Wiwi)? Zama da mad'aukin kanwa fa yana kawo farin kai. Yagirgiza kai cikin damuwa "Sudaida ba yadda zanyi da sune,ina zaune zaman jiranki suma sukazo suka zauna,wajene na kowa to ya zan musu?Khausar tazo tawucesu da takaicin Sudaida,ta rasa abinda yaja hankalinta wajan soyayyar Sinan.

Bakice kome ba.Sinan yakatse shirun. Tad'an harareshi"ALLAH yaso ka na na huce.Yayi dariya tare da shafa k'irjinshi bangaren da zuciya take.Yauwa ko kefa,kinga yanzu hankalin masoyi ya kwanta.Sukayi hirarsu sannan yataka mata kad'an sukayi sallama,yaso yarakata har k'ofar gida amma tace nan ya isa, dan tasan su Yaya Musaddiq suna wajan da autan Inna,kuma ba tasan wannan rikitaccen kallannashi me ban haushi dan ba magana zai yiba..Taja tsaki"ALLAH yasauwak'e mishi wannan halin...

Nagari ake so ba d'an gariba.

13 Rabi'a Thani 1441
10 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD... 2geda with Ra'ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta'in.

...GWAJIN DAFI💔

Almost true story
Daga alk'alamin 🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Shafi na uku.

Kasham tabaro k'auyansu Madauci da yammacin ranar talata,bayan taji sauk'i daga jinyar da tayi na tsawon awanni ashirin da hud'u.Tashiga cikin makaranta da d'okin ganin Julaibib ta kuma hango shi a inda suke zama.Tak'arasa da saurinta "Barkanku da yammaci"Maimun abokin karatunshi ya amsa"Yauwa barka dai.Tatsare Julaibib da manyan idanunta masu maik'o cikin kallan k'auna me cike da shauk'i "kai bazaka amsaba kenan?Iskar data d'ibo tama bata isheshi kalloba.Tayi jimmm...na wucewar wasu dak'ik'u tana kissima wani abu a zuciyar ta,sai tad'an motsa kafad'a any way...sai anjima. Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi.

Julaibib my enigma man...Salonka yana k'ayatar dani wallahi"...

Maimun yakalleshi"Kai nifa bangane ma wannan bita da kulli"dukan kabarin kishiyan ba"Meye had'inka da itane duk inda taganka sai tazo wajan?... Julaibib yafad'a mishi kome.Maimun Yagyad'a kai "to ka yadda mana tunda har ta amince za tayi sallah ba kuma wanine ya tilasta mataba,ai inaga ba wata matsala,kuma kayi jihadi ne,gata kuma Masha-ALLAH kyakkyawace.Yamik'e yana mishi wannan rikitaccen kallan nashi"bazan iyaba.Maimun zai sake magana yad'aga mishi hannu"dakata haka malam, taso mu tafi.Maimun yagirgiza kai "ba d'akin da zan tafi yanzu gwamma in d'anyi shawagina.Yajuya yayi tafiyarshi to shikenan.

Yana shiga d'aki ya ajiye Hand-out, yasa hannu yana 6alle botiren gaban rigarshi tare da lumshe idanunshi a kasalance,yacireta rigar yajefa a saman kujera,ya gaji lik'is ga rashin bacci,dan baiyi wani baccin kirki a daren jiya ba saboda karatu da binciken wasu littafai da yake yi na tafsirin Alqur'ani me girma,idanunshi har wani yaji-yaji sukeyi,a a hankali yafurta"yau da wuri zan kwanta...

"Zanzo tayaka kwana...

Bazato yaji an mishi wata irin runguma ta baya,zuciyarshi tabuga dammm...dan wallahi yaji tsoro...

"Zanzo tayaka kwana tunda Musaddiq baya nan.Tafad'a cikin rad'a

Kasham...zuciyarshi taraya mishi, tabbasss ita d'ince danga k'amshin turaranta nan... Yayi k'ok'arin raba ta da jikinshi amma ya kasa,dan ruk'on kura taga nama ta mishi...

Kanshi yayi wani irin sarawa.

Tafara mishi wani salo da hannayen ta a cikin gargasarshi dake kwance lufff bak'ink'irin da sheki...kar...kar...kar...Jikinshi yad'auki rawa"baah...ba... bahh..banasooo!...dak'yar yafuzgo furucin.Tayi lallausan murmushi tad'ago kanta tana kallan kwantaccen bak'in gashin kanshi...

Meye baka so din...???

Yayi shiru.Tagyad'a kai"tayaka kwannanne baka so ko wannan din?tacigaba da mishi wani salo da hannayenta a dai-dai saitin zuciya... Jikinshi ya mutu murusss...

My enigma say something hun"

Tasake fad'a cikin rad'a da wani irin salo na ta nayanga.Yadaddage ya hankad'eta...tafad'i tabaya akan katifarsu.Hanyar fita yayi sai dai abin mamaki "talaka da mata hud'u har da k'wark'wara me gari gwauro"ta kulle k'ofar dan dama baiji shigowarta ba.

Daga kwancen take kallanshi, yasunkwui da kai,gaba d'aya ya jike sharkaf da zufa kamar wanda yad'auki awanni yana matso jiki.Wata jijiya tafito asaman goshin shi rad'am kamar shatin bulala ranshi in yayi dubu ya 6aci...Amma jikinshi ba k'arfi kona sisin kwabo kamar wanda aka zarema laka.

Sai kuma jikinta yayi sanyi, tasan itace tasashi a damuwa tamik'e tsaye"Kayi hak'uri Julaibib "tahad'a tafukan hannayenta"Dan ALLAH kayi hak'uri ba naso ace ta dalilina kashiga damuwa,danni me k'aunar kace,farincikin ka shi nake so ba damuwa ba.k'walla yacika idanunta... muryarta tafara rawa

Bazaka hak'ura bane D'ansarai?

Yadda tayi furucin a hankali da wani irin salo,yasa yad'ago zai kalleta,itama shi take kallo caraf idanunsu yahad'u,yakauda kai dasauri yanajin wani irin abu yana zagaye ilahirin jiki da zuciyarshi,shi yasa baya san kallan wannan manyan idanun na ta masu maik'o.Kawai sai ta fashe da kuka,tsoro da mamaki suka baibayeshi to me aka mata wai???

"Kasham...

Yafurta sunan dak'yar.Tad'ago da sauri tana kallanshi.Sai kuma yayi shiru kamar me koyan had'a kalmomi da yadda ake furtasu.Idanunshi sun kad'a jawur.

Julaibib kayi hak'uri dan ALLAH".

"Bakomai...Tayi murmushi yau wace rana ya mata wata magana ta daban ba amsar daya saba fad'aba na "Bazan iyaba"saita kalleshi "to za ka aureni?Yayi shiru kanshi ak'asa.Tad'an motsa kafad'a. Tana zuwa kusa da k'ofar ya matsa da sauri kamar zai hantsila.Tayi yar dariya"Matsoraci kawai "ni ba abinda zan maka yanzu amma duk ranar daka shigo nan tanuna tsakiyar tafin hannunta na maka kattt...kisan mummuk'e,sai tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta wani murmushi ya su6uce mata. Tamishi wani kallan k'auna me cike da shauk'i...Tabud'e k'ofar tayi tafiyarta.Yasauke gwauran numfashi "wallahi da basu da lecture gobe da sassafe da yau yayi tafiyar shi gida kamar yadda Musaddiq yatafi.Yamaida k'ofar yarufe da sak'ata yasa mukulli sannan ya kwanta cikin wani irin yanayi.

Tana zuwa d'aki tafasa ihu tafad'a gado.Lidiya da suke yan'uwa kuma d'akinsu d'aya sai dai kowa da abinda yake karanta kamar dai Julaibib da Musaddiq tabita da kallo sai juyi take cikin wani irin yanayi,tabar yanka ganyen Ogu da take yi na abincin darensu,tazauna agefen gadan.

"Inzayadami Kasham?(Meyafaru Kasham)

Kasham tacigaba da juye-juyenta cikin wani irin yanayi,zuwa can kuma tamik'e zaune, tajingina kanta ajikin gadan cikin sanyin murya tace " Julaibib ne"

"Jesus Christ! Holy ghost fire!!!

Lidiya tafad'a tare da dafe kirji da duka hannayenta,tabita da kallan takaici taja dogon tsaki, wallahi kinji kunya,wai dan ALLAH me kika ganine ajikinshi daya tafi da hankalinki haka? Dogone k'akk'arfa,kar kuma kimanta Baranzan wanda kukayi alkawarin aure dashi,shima haka yake,ke ya mafi Julaibib tunda shi Sojane training d'in da yakeyi shi ko rabin-rabinshi ba ya yi, sunansu kuma d'aya"Maza"ko akwai wani abu bayan haka?Tayi lallausan murmushi"taja dogon numfashi a hankali take fitar da iskar tabaki ta hanci.Sannan tace"Hummm...Lidiya kenan ai maza kama suka tara amma halinsu ya bambanta. Tagalla mata harara"kin gama asara,ni dai banga abin so a wajen me shegen girman kai ba,shi ba kowan kowa ba dillalin kashi.Sannu wannan dazai amsa miki da yauwa sai yaga dama amma ke kina neman haukacewa saboda shi...kai tirrr...wallahi tayi d'as da yan yantsunta takoma kan girkinta tana mita Rubbish girl...

Kasham tazame takwanta"duk abinda zaki fad'a indai akan san D'ansarai ne bazai ta6a tasiri a zuciyata ba har abadan duniya, ina san shi koda shi aka tarama munanan halayen jama'ar duniya,ni na san ko waye Julaibib,ba shi da wani girman kai"so hana ganin laifi...

Suna zaune a shago jadawalin bikin Musaddiq d'in suke dad'a dubawa,dan saura kwanaki goma sha biyu.Tayi sallama daga waje tana sanye da riga da zani da dankwali na atamfa ruwan goro da ratsin k'ananan filawoyi ruwan madara da Bak'i,tayafa bak'in mayafi takalmanta bak'ak'e abinci takawo musu.

Wa alaikumussalam shigo.Tana shiga idanunsu yahad'u,yad'an saki fuska"yau Baba yayi tafiya sai zuwa yammaci zai dawo, ni kuma ban san irin garar da yake had'a muku ba idan kun kawo abinci"rake zan sha"sai Maths text book da Graph-book da za a sai mana ni da Yaya Khausar.

Banza yar k'auye,tafi kibamu waje, ba dama a tambayeta me take so sai tace"rake"to ba za a sai rakenba.Julaibib yad'aga mishi hannu "a ah malam shan koko fa kwanciyar rai,to me yamaka zafi?Yamaida kallanshi wajanta"koda yakema idan fitsari abin banzane kaza ma tayi mana.Ta sunkwui da kai"kowa yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yakeyi,shine ko nama a wasu lokutan baya iyaci duk san shi da nama kamar kura sai gani sai hange idan ciwon hak'orinshi ya motsa.

Me kace? Musaddiq yatambaye shi fuska a yamutse.Abinda kaji na fad'a"ke Sudaida jeki ki...sai kuma yamik'e ina zuwa.Dakanshi yasiyo musu Maths da graph d'in yakuma kar6o musu gasassun kaji guda biyar,d'aya ki kaima Inna,biyu nasu Mama,ku kuma dukkanku kuyi hak'uri ku raba biyun.Tasa hannu biyu takar6i ledojin"mungode Yaya Julaibib".Yakauda kai daga kallan da take mishi.Jeki kinji karki daka ta wannan da hidimar aure tasa kanshi yake shirin yin gobara... mutum bai kar zomo ba sai kiga yana shirin ba shi rataya.Tawaiwaya inda Musaddiq d'in yake,shima su yake kallo.Sai ta toshe bakinta da sauri kar dariyar da take 6oyewa ta su6uce mata tashiga uku,idan yakoma gida da daddare zai iya bata na jaki...tajuya dasauri tabar shagon.Julaibib yabita da kallo fuskarshi da murmushi.

Yauma Musaddiq ya rigashi komawa gida tun ranar laraba yatafi,Maimun ma an aiko mahaifiyarshi bata da lafiya shima yatafi.Yana fitowa daga masallaci yanufi d'akinsu dan yanajin yunwa shi kuma yafi gane yadafa abinda zaici fiye da yaje capteria,yana da miya dan haka yadora farar shinkafa yazauna yana yayyanka kabeji, tumatir albasa da gurji.Tana jingine da bishiyar barankaci tana hangoshi dan abaranda ya zauna saboda cikin akwai zafi kuma ba wuta,tana mishi kallan k'auna me cike da shauk'i,shi ko baima san tanayi ba kunu a mak'ota.Tasauke numfashi tana kiran sunan shi a saman la66anta wani murmushi yasu6uce mata ranar da duk ALLAH yabani sa a akanka?....Hummm tagyad'a kai"d'aurin gwarmai za kasha amma na k'auna... tajuya tafiyarta.

Hajiya tashigo da sallama.Ya amsa cikin murmushi"Sannu da zuwa Hajiyarmu, yashimfid'a mata tabarma.Tace a ah mutanan Gidan-Waya saukar yaushe?Ai tun safe ina garin nan,wajejen k'arfe sha d'aya naje gida ba kyanan.Tagyada kai"Tabbas anyi haka,naje asibiti gaishe da Liman na masallacin juma'a ne.Yace "ALLAHU-AKBAR"ashe har yanzu ba a sallameshi ba?Ubangiji yabashi lafiya,zaman jinyar kuma yasa kaffarace. Ta amsa da amin,amin.Anjima ya kamata kuje kugaishe shi Yagyada kai "Insha-ALLAH.
Chapter 5 · 0% Book details