← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 74

Sashe 15

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasham ai ban san baki da hankali ba sai yau, a duk zuri'ar mu ba me salla sai ke ce za kice za kiyi? Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"to baki isaba,ina tagirgiza kai wannan ba za ta sa6uba bindiga a cikin ruwa, dama abinda ki ka dinga yi kenan a makaranta bin mazan hausawa?Tama Maman na ta wani kallo me kama da harara"ni ina ruwa na da rashin sallar zuri'arku?Kuma aike ma kin san mazan hausawa ba k'ashin yarwa,sau dubu nawa ina kawo miki kayayyaki kinaci,kin kuma sani sarai su d'inne suke bani,baki ta6a k'in kar6a ko ki min fad'a akan in rabu dasu ba, sai yanzu dan nace ina san zama irinsu?Ashe kowa yana san wawa haihuwar shice ba a so? Tsamaninki banza kika dinga ci? Takai mata wani mari amma tagoce dasauri yabi iska, tamata dak'uwa kinci uwaki,dan abu kazan ubanki ba za kiyi sallah ba,abinda ba mayi dake sa'in'sa amma gashi daga fara cewa kina san wani tsinannen bahaushe har kina min rashin kunya kina fad'amin maganar dakika ga dama...Tabuga cinye na rantse da ALLAH baki isaba sai dai idan bana numfashi za kiyi sallah.Kasham tagyad'a kai"To maji ma gani ai...an binne tsohuwa da rai.

Lidiya tashigo suka had'u suna ta zagin ta amma ko a jikinta wai anyak'ushi bishiya.Tad'an motsa kafad'a tare da ta6e baki "Kanku ake ji...ta d'auki jakarta"bazan iya wannan bud'ar kan karyan ba, kuci kanku kusha bak'in ruwa.

"Kasham ani yake?(Kasham ina za ki?)

Tajuyo muryar Maman a tsawace.Tayi taku biyu sannan taja ta tsaya"Ani yake?Tasake tambayar ta,ko a jikinta tace.

"Ana kari Julaibib(wajan Julaibib zani)

Dawo ki zauna karki kuskura ki bar gidannan.Tad'anja tsaki sannan tak'arasa ficewa da saurin ta"idan na dawo kar ki barni inshigo"kuma ko ku mutu ko ku rayu wallahi sai na yi sallah kuma ALLAH zai taimakeni in auri D'an Sarai...ALLAH dai yakai damo ga harawa...

Tajuya kan mijinta cikin tafasar zuciya ni dai ka sani gaba d'aya zuri'armu babu wanda yake sallah,sai dai in wancan ne yake yaudare min yarinya,yake so tabi layin shi,to kaji na rantse da girman ALLAH bazan yadda ba, zanje har cikin gidanshi inci mutuncin shi, ba ki yamana ga shi nan yana shirin kama Kasham, dama ya dad'e yana fad'in idan munki sallah to Insha-ALLAH Ya'yanmu sai sunyi.Yagirgiza kai cikin damuwa yasan matarshi bata da mutunci, to shima dai dan uwan na shi Yayanshi uwa d'aya uba d'aya Shedrak,wanda a yanzu yake amsa sunan Alhaji Hafiz ba barin ta kwana yake yiba shima mafad'aci ne wallahi.

Kiyi hak'uri Dinatu mu zauna musan abinyi,nima ba na goyon bayan abinda tazo dashi,kuma da kike fad'in Shedrak ne yake yaudare ta to yaushe rabonshi da zuwa garin Zonkwa bare har yashigo k'auyan Madauci?Tayi shiru.Yawatsa hannaye kingani ko?Ai shekarun da yawa ko Kasham baki haiifa ba a lokacin. Muje wajan Pastor ayi addu'a ko Baptismal idan yaka ma sai a sake mata.Tamik'e cikin gyad'a kai"eh to ka kawo shawara to tasu mutafi ai bamuga ta zama ba da zafi-zafi akan daki k'arfe.

Kasham bata kwana a gidan ba,sai washe gari da hantsi.Lokacin kuma Mamanta ta dad'e da tafiya kasuwa,dama ita take fita ta nemo musu abinda za suci dama sauran buk'atunn rayuwa,yar kasuwa ce sosai da take cin kasuwancin ta gari da k'auyuka na nesa dana kusa,shi kuma mijin kullum yana gida yana aikacen-aikacen yau da kullum da akeyi a gida har girki ma a wasu lokutan idan ba kowa shi yake yi.Yad'ago yana kallanta "Kasham zo mana ganin tana shirin shigewa d'akin ta,tayi kamar ba ta ganshi ba kuma har had'a idanu sukayi lokacin da za ta shigo.

Tazauna a d'aya farar kujerar robar,ko sannu bai samu arzk'in tace mishi ba bare in kwana (Oh mu Ya'yan Ibrahim🤔inda ranka ka sha kallo...sunan wani shiri a Freedom Radio)A ina ki ka kwana Kasham?Tazuba mishi manyan idanunta masu maik'o"wannan wace irin tambaya ce haka Baba? Yagirgiza kai "ai na ga ke a gida kikafi kwana shi yasa na tambayeki kuma Baranzan yazo nemanki na san ba a wajan shi kika kwana ba.Baba ba ruwanka da inda na kwana. Tad'ora k'afa d'aya akan d'aya tana karkad'a kafar dama,tana wata yatsina da hura hanci alamar bala'i takeji da gasken-gaske.Ta sauke gwauran numfashi Ka na ji ko Baba? Eh ina jinki.ALLAH sai na auri Julaibib,ka san yadda nake jin k'aunar shi a zuciya ta kuwa?Takad'a kai"no matter how zan kwatan ta maka ba za ka gane me nake jiba...sai tafashe da kuka duniyar ta cukurkud'e mata wallahi,rana zafi inuwa k'una,to a ina ake so tasamu sassauci ne?Julaibib,Iyayanta,Baranzan, Lidiya, da yan uwan ta kowa yana jin haushinta? To ita tace ma zuciyar ta ta k'aunaci D'ansarai ne???

Tausayi irin na d'a da mahaifi ya mamaye zucyarshi,saboda shi yana da san Ya'ya sai dai abinda tazo dashi me girma ne, amma ga dukkan alamu tana san wannan D'an...menene ma sunan na shi oho ya manta, tunda har ta yadda tabar Baranzan da suka shafe shekaru hud'u suna soyayyar su hankali kwance ba abinda ya ta6a shiga tsakanin su na tashin hankali amma akan shi wannan bahaushen sun fara fad'a,dama duk cikin Ya'yansu ai daga Kasham sai Rahab ne basa canja samari kamar yadda ake canjin kayan sawa,kuma su biyun ne suka maida hankali ka'in da na'in akan karatu, sauran maza da matan suna can suna cin karansu ba babbaka. Matanma sai su shafe watan ni takwas basu lek'o gida ba, suna can wasu garuruwa da jahohi suna zaman kansu suna kuma sheke ayarsu yadda yaka ma ta,galibi ma zuwan su gida sai da dalili me k'arfi kamar lokacin Christmast,New-Year, da Esther,su kanzo a Valentine amma ba kowane Valentine ba.

Kiyi hak'uri Kasham dak'yar ya rarrashe ta tayi shiru,manyan idanunta masu maik'o sun kad'a jawur "Kiyi hak'uri Kasham ni kin san matsala ta ba babba bace,zan iya barin ki kiyi sallah tunda kina sanshi, za kuma cigaba da kasancewa 'ya ta,bazan tauye miki yanciba" you have human right"kuma shekarunki sun kai na duk wani d'an Adam me hankali,babbar matsalar "inda gizo ke sak'ar Dinatu baza ta ta6a amince miki ba,idan kinki ji to na san za ta yafe ki a cikin Ya'yanta, za ta barma hausawa ke forever kinga kuma baki mata a dalci ba, ta so ki ta kula dake ta miki kome na rayuwa...kema ba za kiji dad'i ba.Yakalleta yad'an motsa kafad'a ya cigaba da gyaran waken da yake yi na girkin rana.Itama tamik'e tana k'unk'uni.Yad'anyi murmushi k'uruci dangin hauka,Kasham baki san rayuwa ba.You know nothing but wannan soyayyar data rufe miki idanu." So makaho...

Lidiya tabita da kallo "to wai ke da kike ta wannan hank'oran,kike k'ok'arin 6atawa da kowa akan wannan tsinannan kun dai-dai tane ya yadda zai aureki zai zama miki uwa da uba dasauran danginki da za ki rasa? Dan abu kazan ubanki ina ruwanki?Babbar manufuka kawai,bitch ai na san ke ki ka k'yank'yasa ma Baranzan!

Lidiya ta k'yalk'yale da dariya dan abun bai ba ta haushi ba,ta kuma k'yalk'yakewa da dariya tana tafa hannaye Jesus Christ of Nazareth gaskiya kin fara cin kai (Hauka)

Kasham ta fad'a gado ta rufe idanunta zuciyar ta tana wata irin bugawa,da bata d'auki alk'warin dai na shan taba ba to da yau ALLAH ne kad'ai yasan ko kwali nawa za ta sha,ba ma kara ba,ta dunk'ule hannu ta dinga naushin matashi idanunta na tsiyayar da hawaye masu d'umi " So babbar cuta...

Lidiya ta dafa kafad'arta sai tamik'e da sauri kamar wacce kuna ta harba"get the hell out this house...ta fad'a a haukace.Lidiya tamik'e sai dai in bar miki d'aki amma ba gida ba,dan kema ba na ki bane. Wawuya kawai da har yanzu ta kasa gane san maso wani take yi... Sai kinyi 6atan 6akatatan za ki gane ashe shayi ma ruwa ne madara da bournvita ne ya canja mishi kala.

Mamanta tana dawowa daga kasuwa ko hutawa batayi suka tasata a gaba sai gidan Pastor.Dama yasan da zuwansu dan haka suka zauna zaman jiran fitowarshi Yashigo D'akin-shak'atawar cikin bak'in suit, rigar ciki shirt, takalmanshi da mashak'in wuya (neck-tie)ruwan k'asa,wuyarshi da sark'a rosery.

Yana rik'e da King James Bible.Da fara'arshi yake musu sannu da zuwa shi ma yazauna suka gaisa sannan ya nuna Kasham da kanta ke hayaki ta d'ora kafa d'aya akan d'aya"ke kina so ki bamu matsala me yahad'a ki da bahaushe ne?Tagalla mishi harara tana mishi wani kallan uku ahu "ah kaji k'arfin hali 6arawo da sallama,yanzu kurace za ta cema kare maye? Shi har yana da bakin da zai ma wani fad'a yaushe-yaushe aka gama rigima d'an shi na cikinshi yama wata yarinya yar Kurmin-Bi ciki,yanzu haka yarinyar tana cikin gidanshi sunyi auran leda (auren da ba Pastor ne ya d'aura shi a majami'a ba Church)wai sai ta haihu za a yi auran gaskiya dasa albarkan Iyaye.Yasake kallanta ba magana nake miki ba?To me ko zai had'ani dashi banda soyayyay.Ina son Julaibib zan kuma aureshi ko kamin addu'a bazai kama niba,ai wallahi gwamma ni ba ciki a kamin ba.Maman za ta mareta yahana kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake yi, ki barni da ita kawai Dinatu.

Pastor wannan abun yana cimin tuwo a k'warya,Ya'yanmu da zarar sun girma sun yi soyayyya da hausawa sai kaji suma suna san zama masu sallah, sai su gudu su aure su ko muna so ko bama so,to a kan me za su dinga yaudare mana Ya'ya suna mana d'auki dai-dai suna converting d'insu zuwa musulunci?Sannan su Ya'yan hausawa mata basa ta6a yadda suyi soyayya dana mu Ya'ya mazan,abun yana k'ok'rin shige makad'i da rawa fa,na rantse maka da girnan ALLAH Ya'yanmu mata da suke sallah a cikin gari sunyi yawan da ko mun fara k'irgasu lissafin zai k'wace mana,to gaskiyar magana sai kun k'arae zage dantse da k'wazo wajan preaching ta yadda za Ku dak'ile wannan al'amari suma suji suna k'yamar mazan hausawa kai ba su kad'ai ba da duk wani me sallah kawai(😊Up up up Diniyal-Islam👏).
Chapter 15 · 0% Book details