← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 74

Sashe 61

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sudaida tarufe musu motar itama tana godiya,Julaibib yasunkuyo"toh kagaishe mana da Hajiyarmu kace mata munanan zuwa mata yawon sallah ta ajiyemin dambun nama,tasa amin kilishi me tsomen aya,yanzu ma zan kirata in fad'a mata. Yad'aura belt yana dariya"toh kura duk kai kad'ai? Yaran sunata tsalle daga cikin motar suna d'aga hannu sunama su Julaibib adabo,a hankali yaja motar suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa tasha kwana ta6acema ganinsu.

K'arfe hud'u na yammacin asabar motar Julaibib ta tsaya a k'ofar gidan Hajiya.A D'akin-shak'atawa suka sameta tana waya,tagama tasauke wayar a kunnanta tana murmushi"lale marhabun,yau ina da manyan baki. Takalli Sudaida cikin tausayi dan ta kasa zama a kujera, zama tayi ak'asa tana matsa k'afafunta da suka fara kumbura alamar ciki ya tsufa wash...tafad'a tana yamutsa fuska"sannu Sudaida ALLAH yaraba lafiya.

Kai Julaibibi Sudaida tadawo kenan sai ta haihu ko?A ah jibi zamu koma ni bazan tafi in bartaba. Hajiya tagyad'a kai"madallah,to idan haihuwar tazo sai kuyi yaya?Hala ka ta6a kar6an haihuwa ne? Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"wannan karan dai zanyi,Hajiya bar wannan maganar kinji,ai haihuwar ma da saura,yad'an kalleta kuma ni gaskiyar magana"I can't do without Zaujatiii... besides me.

Bashakka Julaibibi zama da mad'aukin kanwa...ni dai na sanka me kawaici amma wannan matar taka me suffar takand'a ta fara koya maka rashin ta'ido ko?To kaji dakyau baza tabikaba,to me zata maka da wannan tsohon cikin?Sudaida tayi murmushi tana zancen zuci"lallaima Hajiya ni ce na koya ma Julaibib d'in rashin ta'ido?Yaya D'ansarai wallahi gwani na gwanaye ne bar ganinshi haka Ustazu-Ustazu baya san magana hummm... takyalkyale da dariya tuno abinda yagama fad'a mata daren jiya data keta wani sha mishi k'amshi dan ta karance tsabbb...da abinda yake so.

Tad'an turo baki gaba"Hajiya ai gwamma in zauna a suffar takand'a da dai in zama tashi da nishi...bakiji kirarin muba?Bena bakya tsufa sai dai kiyi girgiza ki sake sabon gashi,kuma waya jazamin wannnan k'aramin jikin idan ba ke ba?Takalli Julaibib"Yaya D'ansarai...Kasha kuruminka k'afata k'afarka ai tare ta gammu.

Yauwa Zaujatiii...tabashi hannu suka tafa, tad'an yafito shi zo kaji,yamatsa kusa da ita tasaita bakinta a kunnanshi tana rad'a mishi wata magana, suka kalli juna,yad'age gira yana nunata da yatsa cikin yar dariya"da gaske Zaujatiii...? Ta amsa kai tsaye"na rantse maka da girman ALLAH.Hajiya takama ha6a ba shakka"wato ana nuna miki ma'aiki kina rintse idanu,da wannan tsohon cikin kike wannan iya shegen k'auri da kare? Tawatsa hannu"to ai shikenan jiki magayi baki kuma mafad'i.Yamik'e barinje shago wajen su Baba"ke sai na dawo zamu tafi gidan Kawu ko? Toh adawo lafiya.

Yana fita Sudaida tamatsa kusa da Hajiya takalleta cikin natsuwa"Hajiya na rantse miki da girman ALLAH nima na fiso in zauna a nan sai bayan na haihu,toh kin san halin Yaya D'ansarai da banyi haka ba ni zai rufe da fad'a,kilama yace nina kira a waya na fad'a miki,saboda ni ma ina ta damunshi ya dawo dani gida,shi kuma yana cemin a ah acan zan haihu,dana fara nak'uda wai asibiti za mutafi, mutumin da a wasu lokutanma har na fara bacci bai shigoba.

Kin san halin miskilancinshi idan suka motsa, maganar duniyar nan za ki mishi,sai dai yamiki kunnan uwar shegu,yasunkwui da kai bazai yi magana ba ko da me za kiyi,yamaida mutum kamar wanda yaci kai(hauka)to Hajiya me zuwa fada ga banza bare kuma Sarki na kira?Hajiya tajijjiga kai"eh lallai kinyi hikima da siyasar rayuwa a nan, dama idan kasan mutum to sai kaci maganin zama dashi, barni dashi zai zo zamu sake tattaunawa.

Suna cin abincin dare kiranshi yashigo tad'aga da sallama,ya amsa muryarshi a dake"har yanzu kina gidan Hajiya ne?Eh Zaujiii... dama yanzu zan kiraka dan na jika shiru...yatari numfashinta"kin jini shiru,ke makauniya ce dabaza ki iya tafiyaba dole sai da d'an jagora ko?Tad'anyi murmushi wannan fad'an dawalakin goro a miya,ba mamaki taran dangi aka mishi akan dole yabarta anan,sai ta fad'a a tausashe duk shi d'in yace ta zauna idan yadawo za suje gidansu"Esbeer Yaya D'ansarai nahhh...ganinan zuwa.Hajiya takalleta"karki nuna mishi kin fahimci abinda yasa shi a damuwa,tarataya jakarta"toh Hajiyarmu mukwana lafiya. ALLAH yasa Sudaida.

Da sallama tashiga D'akin-shak'atawar, yakalleta a d'age yakauda kai.Bismillah,wash...ALLAH! tafad'a sanda ta zauna a k'asa dirshan tana maida numfashi kamar wacce gudun famfalak'i"Yaya D'ansarai na dawo. Yayi kamar ba dashi take magana ba,ganin haka tasama ma kanta lafiya ta hanyar kunna data tana turama A'isha sak'o,wucewar dak'ik'u kusan arba'in sannan yamik'e zaune daga kwanciyar da yayi yakira sunan ta.

Takashe data tana amsawa da na'am.Kishirya gobe da sassafe zamu koma. Gobe kuma?To saboda me?Hummm...ki bari kawai wai har da Baba a fad'a min ya kamata a barki,ni kuma bazan iya ba, Sudaida ko baza kimin kome ba to ni dai ina san zamanki kusa dani,yabud'e idanun shi daya fara rufewa gaba d'aya a kanta"Zaujatiii... ina k'aunarki ba tare da wani dalili ba,zan cigaba da k'aunarki a kowani hali da yanayi na rayuwa kingane ko?Tajijjiha kai"na'am na gane Zaujiii...ALLAH yabarmu tare,mutu karaba takalmin kaza.

Ta sauke numfashi to amma Yaya Dansarai... wani hanzari ba gudu ba,Baba da duk wanda yace kabarni anan umarni suka ba ka ko shawara?Yad'ago yakalleta"shawarace ba umarni ba.Tawani marairaice"to in ko hakane bai kamata kawatsa musu k'asa a cikin idanu ba "Yaya D'ansarai tsakani da ALLAH ba wanda zai so ya haifi d'a a cikinshi bayan fad'i tashin da yayi a rayuwar d'an nan har yazama abinda yazama a doron duniya,sannan wani abun yata so,su bashi shawara a matsayinsu na masoyin shi da suka fi kowa k'aunar shi bayan ALLAH da manzon ALLAH amma yawatsa musu k'asa a cikin idanu ta hanyar kin kar6an shawarar da suka ba shi ace ransu bazai sosu ba?Duk fad'in duniya duk wani me da'awar yana k'aunar mu toh daga bayane sadaka da karuwa,dan da Iyayen na mu basu maidamu mutane a sanda bamu da kome baza mu iya amfana ma kanmu kome ba to da bamu girman da duk wani me son mu ya so muba.

Tasake tausasa murya"Zaujiii...gyara kayan ka baya ta6a zama sauke mu raba,nima yanzu d'an mune a cikin cikina,to ai baza muji dad'i mu bashi shawara bayan mun maida shi mutum yak'i kar6a,bayan kuma shawarar bawai ta sa6ama shari'a bane"Yaya D'ansarai kayi hak'uri kabarni anan d'in,na tabbatar dan haihuwar farice,amma da baza su d'aga idanu su kalli rayuwarmu da abinda yake gaban muba, in dai bamu muka fad'a musu dan neman shawara ko kuma addu'a ba.Zaujiii...Aljannarka a k'ark'ashin Iyayanka take sai ka bisu ka kyautata musu zaka sameta fa.Tayi murmushi kasha kuruminka mijin Sudaida ni zan dinga zuwa maka hutun k'arshen mako(weekend)a 6oye,wallahi ba wanda zai sani sai Yaya Aminu dan na san ba zai k'i kawo ni ba.

Kalaman Sudaida gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata,zuciyarshi tayi wasai,d'aya daga cikin jin dad'in doron duniya samun mace tagari "Zaujatiii...Ke macen alheri ce,ALLAH yamiki albarka. Kiyi zamanki ba sai kin dinga zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Gidan-Waya ba ni duk lokacin dana samu sarari zan zo ko a k'arshen mako ko a ranakun mako(weekdays)ALLAH yamiki albarka yabaki nak'uda kafiifan.

Yana had'a kaya a jakar da zaiyi tafiya da ita yana dad'a jaddada mata"Zaujatiii...kullum fa kisha ruwan zamzam d'in nan,kici dabino,ki yawaita addu'a ba dare ba rana,gobe Insha-ALLAH zan ai ko miki da hulba ki fara tafasashi kina shiga,da kinji alamun nak'uda ki d'ibeshi ki had'a da zuma ki cakud'a kidaure kishanyeshi kinji ko?Jikinta yayi sanyi sai take ji kamar kar yatafi,ko kuma su tafi tare tana lumshe idanunta mak'alallun kwallan da suka cika su,suka samu damar zubowa sharrr...yayi kamar bai gani ba,yagama shirya kome a jakar ya rufe yatafi yayi wanka yashirya cikin shigarshi ta dogaye fararan kaya kanshi da hular dara bak'a.

Yagama d'aure bak'in agogo a hannun damarshi,sannan yagewayeta yana magana cikin tausayi da k'auna"haba Zautajiii...kuka kuma! yafara share mata hawayen ai ke macen albarkace Sudaida,ban ta6a nadamar zama dake ba ko na sisin kwabo...haba Sudaidan D'ansarai...Ki k'arfafamin gwiwa kamar yadda ki kayi jiya mana,wannan hawayen na ki sai su sa autan Inna a uku fa...yacikata da kalaman k'auna da kambamawa... Itama ta gewaye shi tare da d'ora ha6arta a kafad'arshi

"Zaujiii... na yi shiru...ALLAH yamaka albarka. Yayi murmushi"amin.ALLAH yatsare min kai, yakiyaye ka da kiyayewarshi,tasa hannu tad'an shafa k'asumbarshi...wucewar wasu dak'ik'u sunata kallan juna, a hankali suka saki juna yad'auki jakar shi sannan yad'aga hannu yana mata adabo...Yajuya yatafi sai ta d'aga labulan taga tana cigaba da kallan shi yashiga mota yad'aura belt yayi azkar yasa mukulli yatashi motar...har yabar haraban gidan tana cigaba da kallan danjojin motar yayi nisa ya6ace ma ganinta sai taji wasu zafafan hawaye suna zubo mata sharrr...shar...tasaki labulan takoma ta kwanta cikin kewar masoyiii...

Shekaru goma sha uku kenan cifff...da auren Julaibib Abdullahi D'ansarai da Sudaida Ibrahim Me-Lambu. A wad'annan shekarun ALLAH ya zurta su da Ya'ya sanyin idanu da Bilkisu...kyakkyawar yarinya data d'auko kyan Iyayenta,bak'in gashi me yawa da tsantsi irin na mahaifinta, sannan ALLAH yabata farar fatar da bana Iyayenta bane ganin damar Ubangiji ne kawai.Bilkisu yarinyace data yi farin jini a zuri'arsu kaafatan,gata da natsuwa bata da yawan magana kamar mahaifinta,idan kaji dariyarta toh dashi suke magana, ga ta da k'wak'walwa duk abinda aka koya mata sau d'aya toh ya zauna kenan ba ta buk'atar maimaici,tana da kaifin basira.

Bilkisu Julaibib D'andarai...

Shekarunta biyar a yanzu haka tana primary one a makarantar boko,bangaren Islamiya kuma tana da haddar Izifi goma sha biyar daga Yasin zuwa nasi duk in da kaja mata Insha-ALLAH zata cigaba.

Sai Maimunatu Julaibib D'ansarai... kanwarta takwarar Inna suna kiranta Walida me shekaru uku.Sai kuma wani cikin da take dashi.

Julaibib ya d'auki son duniya ya d'orama Y'ayan nan musamman Bilkisu son ta yake kamar me, saboda dalilai masu yawa,na farko ya sameta a sanda baiyi zato da tsammani ba,na biyu tayi kama da Innarshi,na uku sunan marigayi daya so auren ta kamar me amma ALLAH bai k'addari za suyi aure ba,na hud'u Sudaidan da yake so yake k'auna ita ta haifa mishi,na biyar yarinyar akwai ta da k'wak'walwa da sauransu da sauran...

A gajiye lik'is yashigo gidan da sallama,suka gewaye juna tana mishi tausa a hankali yalumshe idanunshi wata natsuwa ta mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi "Zaujatiii...ta iya biyar dashi da lak'antar abinda yafi kwantar mishi da hankali,yad'an shafa kanta"nagode Zaujatiii...Takawo mishi ruwa yasha,sannan yaje yayi wanka yasa kaya k'ananan wandon chinos ruwan k'asa da shirt mara nauyi fara, yazauna yana hutawa,Sudaida tabishi da kallo.
Chapter 61 · 0% Book details