← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 74

Sashe 57

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani k'amshin turaren d'aki da sassanyar iskar da take shigowa ta tagogin da suke bud'e yamamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta,sai taji ta samu natsuwa ta lumshe idanunta tana jan numfashi"Yaya D'ansarai wallahi me tsabtane,ji yadda yazauna yagyara gidan kamar mace. Tashige d'akin bacci,tazauna a gefen gadon tad'auki wani d'an k'aramin hotonta da ya ajiye a dirowar gefen gadon,ta d'auki hotonne a wani excursion da sukaje a Wadom akan harkar gona tun tana aji biyu a k'aramar secondary,tak'arema hoton kallo tana tuno irin kyan da Julaibib d'in yace wai tayi...Wanda ita dan haushin irin munin da tayi ta turo baki gaba zata yaga sai gashi ya shigo gidan shine yakar6a,tamaida hoton ta ajiye tana murmushi ita tama manta ta ta6ayin hoton.

Taje tayi wanka tabud'e wardrobe tad'auko riga da zani na shadda ruwan makuba dan dama akwai kayanta a gidan,wasu lokutan idan tazo makaranta ba ta komawa Zonkwa sai tayi zamanta koda ba Julaibib a garin tunda baya samun zama yau yana Zari'a gobe yana Katsina, jibi yana Kaduna,haka dai haka dai ake ta gwagwarmaya da zirga-zirga a cikin rayuwar.

Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar Aminu yashigo ya ajiye mata injin d'in matse ruwan rake tagama azkar d'in sannan takalleshi cikin murna da shakka tanuna injin d'in tana kallanshi"Yaya Aminu da gaske?Yajijjaga kai "Sudaida ko da nake da raha ai na san irin rahan da nake yi da kowa,bazanji dad'i ni akaran kaina amin irin wannan kyautar bayan na sa hannu na k'ar6a,sai kuma a kar6e wai wasa akeyi,dan haka bazan ma wani ba, bare ke kanwata da nake ji da ita a cikin k'annina,yad'an kalleta a kwai rake a gidan nan? Tamik'e ai ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar ba ta tsurar fulanin asali bane,a na'urar sanyaya abubuwa(fridge)tad'ibo ferarrun rake guda biyar takawo mishi,yauwa d'auko wuka kigani.

Yakar6i wuk'ar yak'ara yankasu k'anana sannan yasa a ciki,yan dak'ik'u kad'an yad'auki Kofi yajuye mata tataccen tsurar ruwan rake, yamik'a mata tasa hannu biyu takar6a takai tsakanin la66anta da bismilla takur6a,sai kawai tacigaba da sha har sai da tashanye duka.Suka kalli juna,yad'an dage gira"toh ya?Takyalkyale da dariya tana jijjiga kai "Alqur'an yayi ba k'arya,nagode Yaya Aminu ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi.Amin Sudaida"ke ma muk'amuk'inki sa huta da tauna,to kai baka shaba?Yagirgiza kai"sanda za a nuna min sahihancin injin d'in an matsa min na sha. Yamik'e yana gyara zaman hular shi"to barin kama hanya,taje ta d'auko mishi kud'in da zai kaima Inna sukayi sallama.

Tana wanke d'anyen na'ana'a yashigo D'akin-girkin a d'okance"Zaujatiii...saboda ALLAH dama kinzo garin amma baki fad'a min ba?Yazuba mata idanu"to yanzu dana wuce Zonkwa ne fa? Tad'an motsa kafad'a"duk d'aya 6arin manshanu a miya.Yarik'ota cikin kewa sai kuma yasake ta barinje in sallami d'aliban da suke jira a waje yawuce D'akin-shak'atawa yad'ibo wasu takaddu yafita.

Sai da yayi sallar Isha'i sannan yashigo yazauna a kusa da ita yana ganin rubutun da takeyi a na'ura me kwakwalwa"barka da shigowa Yaya D'ansarai.Yagyad'a kai"barkanmu kema kinzo lafiya?Tayi shiru kamar bataji shiba,wucewar wasu dak'ik'u kuma tad'an kalleshi"yayi murmushi kina k'ok'ari fa ALLAH yak'ara basira.A tak'aice ta amsa da "amin.Sai kuma tarufe Laptop d'in tamayar ma'ajiyarta.

Ta dawo tazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna,zama nesa dashi da tayi yabashi tabbacin akwai maganar da zata fad'a mishi me mahimmaci dan haka take yi,dan haka shima yadad'a gyara zama dan yaji yau kuma dame tazo?

"Yaya D'ansarai kana k'aunata kuwa? Baiyi tunanin abinda za ta fad'a kenan ba,amma sai ya 6oye mamakinshi ya amsa mata kai tsaye"eh Sudaida ina k'aunarki.To na rok'eka da girman ALLAH karabani da damuwa,kome yanada iyaka to tsakani da ALLAH abinda zuciyata za ta iya d'auka kenan,idan ba haka ba to ba abinda zai hanata kumbura ta fashe k'arshen rayuwata a doron duniya ya zo kenan,tanuna kanta da yatsa,ni na san ba autar mata bace dan haka zan tayaka addu'a ALLAH yabaka wacce tafini, wacce zata haifa maka sanyin idanu tunda ni na kasa, nima ALLAH yabani dai-dai ni.

Yakalleta cikin natsuwa"me aka miki da kike zancen rabuwa?Da mamaki takalleshi"au yanzu baka gani ba?Saboda bakai ake ma ba?Tayi wani huci cikin kad'a kai"toh madalla,amma Yaya Julaibib gaskiya ni dai bazan iya wannan zaman ba,duk lokacin daka shirya nima a shirye nake zan ba ka sarari.Tamik'e.Jinan Sudaida koma ki zauna. Bata zauna ba sai kawai ta durk'usa a gabanshi tafara kuka

"Yaya D'ansarai kaji tausayina mana bazan iya jure wani wulak'anci da bak'ak'en maganganu ba dan kawai ban haihuba,bana so zumunci ya6aci ne amma na rantse maka da girman ALLAH da da kaina zan d'auki mataki.Tasake fashewa da matsanancin kuka,kukan abu biyu take yi,gana rashin haihuwar akaran kanshi,gana wulak'anci da tozarcin da ake mata akan dai rashin haihuwar me makon ma abarta taji da abinda yake damunta.Haka ta dinga fad'ar duk maganar data fito daga bakinta ba tare data tauna ba.

Yad'ago ta fuskarta sharkaf da hawaye da majina yazuba mata idanu na wucewar wasu dak'ik'u saboda ya rasa abinda zai fad'a mata,sunyi waya da Hajiya kuma tafed'e mishi bire har bindi "tabbasss an dad'e ana mata wannan cin k'ashin, amma shi da ita bata ta6a fad'a mishi ba,ko ya ganta cikin damuwa idan ya tambaya za ta girgiza kai"tace ba kome ko tace wani abu kazane ba gorin rashin haihuwaba,yayi tsaiii...har yasamo bakin zaren,sai yayi murmushi"kinga Sudaida share hawayenki tabbasss ni D'ansarai ina k'aunarki dan haka zan rabaki da bak'in ciki da damuwa.Takalleshi kallan k'arin bayani"Yajijjiga kai"kiyi hak'uri kibani lokaci zanyi tunanin yadda al'amuran za su kasance ba tare da an 6ata zumunci kamar yadda kika hango haka ko?

"Zaujatiii...ina so kimin alk'awari zaki bani lokacin ba tare da kin sake tambaya taba har sai na zo miki da zancen,lokacin na samu mafita...za tayi magana yatari numfashinta"dan ALLAH kar kice kome,ai kin san ba zanyi abinda zai cutar dake ba. Tayi shiru kawai tana share hawaye tamik'e zuwa d'akin bacci takwanta tare da d'ora kanta a saman matashi.

Kad'an yaci abincin daren sannan yaje yayi wanka yasa kaya marasa nauyi na shan iska,yazauna a doguwar kujera ya barbaza wasu takaddu yana aikin cikesu d'aya bayan d'aya sai dai ya kasa jure rashin Sudaida,kewarta ta dame shi dan haka yamik'e zuwa d'akin.Suka kalli juna tana kwance da wani littafin lissafi tana nazarin shi,tamaida kanta cikin littafin amma ta gagara cigaba da nazarin,yazauna a gefen gadan sannan yasa hannu yakar6i littafin.

Tawani 6ata fuska"Yaya D'ansarai gobe fa muna da jarabawa shi yasa nake nazarin nan.Yamata wannan kallan da yake ba ta haushi yagyad'a kai"uh na sani...ni ma gobe zan tafi Katsina yaya kenan? Tad'an turo baki gaba tana dad'a gyara bargon data rufa"toh kowa sai yakwanta yayi ishashshen baccin da ake so mutum yayi duk dare,gobe kowa sai ya tashi a watstsake katafi Katsina,ni kuma in shiga makaranta ba shikenan ba?

Takauda kai daga kallan dayake mata, tafara jero azkar d'in kwanciya.Ai ko ba shikenan ba,ki sallameni.Tagyad'a kai"toh jeka na sallame ka, ALLAH ya lullu6eka da rahamarshi da albarkarshi, asubah tagari.Yayi murmushi sannan yasa hannu yana mata wani salo...salon data kasa daurewa tamik'e zauna tana dariya"Yaya D'ansar...sauran kalaman suka mak'ale sakamakon wani sak'o d'aya bata me girman ban mamaki me sa a fita a hayyaci.

Da safe yagama shirin shi tsab natafiya cikin shigar farar shadda yana zaune a D'akin-shak'atawa, yayi shiru cikin nazarin kalaman Sudaida dan ko da asubahi sai da tadad'a tabbatar mishi tana nan akan bakanta,ta kuma bashi sarari tana zaman jiran shi.Yadda yake juya zuman da yasa a shayi haka yake juya kalaman;tafito daga d'akin baccin su cikin shigar mutunci da mutunta kai kamar ko yaushe za ta shiga makaranta.Tazauna a hannun kujerar "Yaya D'ansarai wai har yanzu shayin ne baka shaba?Tun kafin in shiga wanka fa nakawo maka.Yasunkwui da kai.Sai kawai tamik'e tad'an kalleshi nawucewar wasu dak'ik'u

"Yaya D'ansarai ALLAH yakiyaye hanya...

Tad'an sunkuya tabashi sumba sannan tayi furucin da wani salon shagwa6a"sai munyi waya ko?...tajuya tayi tafiyarta dan tasan ba magana zaiyi ba in dai yayi wannan sunkuyar da kan"sanin hali ai yafi sanin kama.

Yabita da kallo yana lallausan murmushi yayi d'as da yan yatsunshi"hak'ata zata tadda ruwa Insha-ALLAH ai ni dake mutu karaba yarinya.Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci yaja a gurguje yagama karyawa,yad'auki jakar shi ta matafiya ya rataya a kafad'a da mukullin mota yakulle gidan yana addu'ar fita daga gida"bismillah tawakkaltu alallahi walahaula walaquuwata illah billah.Yashiga mota ya zauna yana d'aura belt yana kuma amsa wayar wani abokinshi na koyarwa da za suyi tafiyar tare.Tun daga ranar Julaibib yacanja taku tunda abin iya ruwa ne...

A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar litini (Monday)ranar aiki ko nasara na tsoron ki tana kwance cikin bargo tana baccinta na tofan gira dan yau sai yammaci zata shiga makaranta kiran wayar Inna yashigo tad'aga da fara'a"Innarmu Sudaida takirata tana yar dariya"na'am yar gidan Inna,suka gaisa Inna tace"na ji autana shiru ni da Alhaji har mun gaji min kira layinshi sau shurin masak'i,da tana shiga baya d'agawa amma daga baya kuma ta daina shiga kwata-kwata.

Dasauri cikin d'an bud'e idanu dan mamaki tace"shi Yaya D'ansarai d'in Inna?Eh shi d'in,ko baya jin dad'i ne kuke 6oyewa?Fargaba takamata dan kwana biyun nan itama fa bata gane mishi wallahi"a ah Inna lafiyar shi k'alau,yanzu ma yana cikin makaranta bari ya shigo inji abinda yafaru.Toh ALLAH yadawo dashi lafiya,ALLAH ya jishshemu alheri sukayi sallama Sudaida tana amsa addu'ar Inna da amin,amin Inna.

Tafito D'akin-shak'atawa kawai taganshi kwance a doguwar kujera.Yaya Julaibib takira sunan shi. A hankali yabud'e idanun shi yana kallanta"har ka dawo ne amma baka nemi ni ba? Ni banji shigowar kaba.Yauwa sai tajuya ta d'auko wayarta"munyi waya da Inna d'azu barin kirata,yafizge wayar ta bishi da kallo yakasheta gaba d'aya sannan yatura a aljihun gefen rigarshi ta dama"rabu da ita Sudaida.Tazauna a k'asa gefen k'afafunshi tana bud'e idanu da mad'aukakin mamakin furucinshi"Innarce za a rabu da ita? Bai bata amsa ba yamaida idanun shi yarufe.
Chapter 57 · 0% Book details