← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 74

Sashe 29

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tazuba mishi jajayan idanun ta da suka rine da 6acin rai tadad'a rungume Ummi"bazan yafe ba. Yagyad'a kai"to naji amma dan ALLAH kiyi hak'uri da kukan nan muje ga abincin ku can kije ki k'arya.Bana ci, tasa gefen zaninta tana share hawaye da majina an kashe min Kasham an bar min grandchild cikin maraici... for God sake Shedrak Ummi guda nawa take da zata iya d'aukar wannan tashin hankalin?

Yakalli Ummin"tabbass Ummi ba ta san kome ba,bata ma san me ake kira da mutuwa ba bare har yatashi hankalin ta,guda nawa take?Ko shekara uku batayi ba to amma ya za suyi da hukuncin ALLAH?Yadda duk yaso haka yake zartar da hukuncin shi"idan yaso yafitar da rayayye daga jikin matacce,idan yaso yafitar da matacce daga cikin rayayye"Qaadiran alaa manyasha'u.Dak'yar yasamu ta yi shiru da wannan sambatun da take tayi cikin kuka da d'aga murya.

Makon su d'aya sukayi shirin komawa k'auyansu Madauci,Maman ta so k'warai abata Ummi ta tafi da ita amma Salim da Alhaji Hafiz suka bata hak'uri akan hakan bazai yiwuba kasancewar addini ba d'aya ba.Salim ma yasake ba ta hak'uri tare da alk'awarin kawo musu Ummi lokaci zuwa lokaci suna ganin juna.

"Mutuwa ba ta zama masifa ga mumini,mutuwa hutuce ga wanda yadace da kyakkyawar makoma...ALLAH ba yana nufin 6atama bawa bane dan ya d'auki wani bangare najin dad'in shi Iyaye, mata, miji,Ya'ya da yan'uwa.. Alhaji Hafiz yadafa kafad'arshi "Salim...na san kai namiji jarumi ne,to na rok'eka da girman ALLAH kayi hak'uri kaga yadda kazama kuwa a yan kwana kin nan? Sumayya ta riga ta tafi rayuwarta ta doron duniya ta riga ta k'are,ba abinda take buk'ata awajan mu yanzu sama da addu'a...Addu'a itace abincin mumini...to mu yawaita aika mata dashi.Kaima ka natsuwa kacigaba da zuwa kasuwa ALLAH yabaka macen albarka.Yahad'iye wani abu me d'aci dak'yar yayi furucin" nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma...

Ummi tana gidan Alhaji Hafiz dan shi yanemi wannan alfarmar,amma Salim ya dai basu ita dan kawai sun cika mishi idanu ne,saboda yadda yake sintiri ba dare ba rana.Suna hira a D'akin-shak'atawa zuwan shi gidan a aranar karo na uku kenan.Alhaji Hafiz yakalleshi cikin natsuwa "Salim kayi aure mana.Yad'an yi murmushi kawai. Kayi shiru bakace kome ba?Alhaji ba auran ne bana so ba, tunani nakeyi anya zan samu mace kamar Sumayya?Wani irin zama mukayi me cike da amana, me cike da girmama juna,zan samu macen daza ta rik'e min Ummi da amana? Yagyad'a kai"me zai hana Salim?Kai da can abaya ka san za kuyi irin wannan zaman da Sumayya?To karka cire tsammani daga al'amarin Ubangiji mana.jikinshi yayi sanyi wannan gaskiya"nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma.

Ummi ta shigo da gudunta dan taji muryarshi"Abba na baka tafi ba?Uh ban tafi ba.Tayi dariya"to muje ka kaini Galaxy...in kira Yaya Zuhair mutafi tare?Yakalleta da kulawa "Ummi baza muje Galaxy ba, lokacin makaranta ya kusa,baza mu sake zuwaba sai an bada hutu kinji ko?Ta6ata fuska sai kawai tajuya tayi tafiyar ta, kwallah sun cika idanun ta.Suka bita da kallo har tafice.

Me yasa kayi haka Salim?Dama taku da Ummi zata 6aci?Lallai yau na ganku a rana.Yad'an yi murmushi"ai ba duk abinda take so nake biye mata ba,wani lokacin ko akwai abin ina hanata saboda ta taso cikin sanin ba ko me da mutum yake so a rayuwa yake samu ba, ko da kuwa yana ganin abin baifi karfin shiba, kauna da soyayyar dana ke ma Ummi ba makauniya bace...

Lokaci k'ank'ani Salim suka dai-daita da 'yar limamin unguwarsu aka daura musu aure,shima sai ya samu sauk'in zirga-zirga tsakanin gidanshi dana Alhaji Hafiz saboda Ummi.Mariya tana kula mishi da Ummi gwargwadan ikon ta, shima ya yaba da hakan sai suka samu kwanciyar hankali dan kowa yana yaba k'ok'arin dan'uwanshi,sai tak'ara bada himma tana mata rik'on tsakani da ALLAH kamar yadda zata rik'e Ya'yan cikinta"yaba kyauta tukwuici.

Yana sanye da wandon chinos ruwan zinare sai riga me dogon hannu da ratsin ruwan zinari da bak'i,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata k'yallin hair fruits,k'amshin Arabian perfume d'inshi ya cika d'akin. Alk'asim da suke abokan wasa tawajan uba yashigo yana kallanshi "Lallai mutumin nan kana jin dad'in ka, kaga yadda kazama wani d'an matashin bak'in bature kuwa? Yabashi hannu suka yi musafaha.To ya karatun? Alhamdulillahi ai ya zo k'arshe tunda na gama rubuta Project d'ina.Ah lallai sai shirin tafiya bautar k'asa to Ubangiji yasa aje a sa a.Amin nagode. Yad'auki remote yana canja tasha baya san labaran CNN d'in nan,yan kanzagin Amurka (America)kanwa uwar gami ce,da yad'a propagandar k'arya akan addinin musulunci da musulmai.Yacire wayar shi da yasa a caji ta cika,suka fita zuwa gidan Hajiya sai dai gidan na ta da kwado sai sukayi zamansu a dakalin k'ofar gidan suna hira.

Aminu yak'araso yana kallan Julaibib cikin raha yace"hey dude what's up?Yagalla mishi harara "Amincin ALAH zaka rok'amana ba wannan ba..yatare shi cikin dariya"kar ka wani harareni kai kayi shiga irin ta su ai dole in maka irin al'adarsu,shima yazauna sannan yamik'a musu hannu sukayi musafaha.

Suna ta hira amma ya dai na jin abinda suka fad'a tunda ya hangota"indai yana gari to ranakun k'arshen mako irin haka yana ganinta.A natse take tafiya irin ta 'ya macen data san abinda take yi wato gefen hanya, yanata kallanta har tasha kwana.Wani murmushi yasu6uce mishi"Yarinyar can ya yaba da hankali da natsuwar ta.Aminu yayi yar dariya"Dan Sarai kenan biri yayi kama da mutum fa...na rantse maka ALLAH da zafi-zafi ake dukan k'arfe idan katsaya kallan ruwa...irin na Aisha to ko ba abinda zai hana kwad'o yamaka k'afa. Yajijjiga kai "tabbass zancen ka dutse...

Washe gari lahadi yakafa ya tsare sha d'aya da rabi yabar Musaddiq a shago yaje dakalin wajan yazauna yana fatan ganinta,dai-dai lokacin aka ta shi daga Islamiyar su,wucewar wasu yan dak'ik'u sai ko gata ta zo zata wuce,yabita da kallo tana sanye da dogon hijab me hannu ruwan sararin samaniya kafad'arta rataye da bak'ar jaka.

"Assalamu alaikum...

Karo na biyu kenan yamata sallamar.Dafarko tayi tsammanin ba da ita yake yiba shi yasa tayi shiru, sai da yasake maimaitawa,a hankali tad'an juyo ta kalleshi sannan ta amsa.Da sauri yamik'e daga dakalin ganin ta juya taciga da tafiyarta... "am... Dan ALLAH...Jimana.Tatsaya ba tare data juyo ba tana jiran abinda zai fad'a.Yayi k'asa da murya "kinga yanzu sauran d'aliban za su firfito kuma kamar zamu takura musu idan muka tsaya anan, ko zamu d'an matsa daga can bakin Library? Batace kome ba suka k'arasa wajan yad'an jingina da k'arfen allan bayani(signboard)d'in yana kallanta ta sunkwui da kai.

Ya Ilahi...sai yarasa abinda zai fad'a ta mishi arwa.Wucewar wasu dakk'ik'u tad'ago kai ta kalleshi cikin natsuwa dan shirun yayi yawa "Malam lafiya?Yad'an sosa kunne"Kiyi hak'uri da na san gidan da kike bazan tsaida ke a hanya ba,can d'in zan biyo ki dan kambamawar data dace dake kenan"Dan ALLAH ina ne gidan ku?Tagirgiza kai"ni ba yar garin nan bace karatu nake yi a Nursing School a cikin makaranta nake zama.

Ayyah...to ya muka ji da shan geron Sunday?(garin kwaki/rogo)yadda yayi furucin cikin jimami yasa tad'anyi murmushi"har da kai? Yagyad'a kai"eh ai duk kanwar ja ce,nima d'alibi ne gobe war haka ai na tsufa a makaranta.Atakaice yamata bayanin kanshi itama haka da garin data fito.

Adai-dai lokacin suka shawo kwana dawowar su daga makarantar allo kenan.Juyowar dazaiyi dan sunyi sallama da Bilkisu caraf idanun su yahad'u dana Sudaida"wani irin yanayi mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta, tagalla mishi harara sannna takauda kai,cikin fushi tayi gaba su Khausar suka tsaya gaisawa suna d'an tsokanar shi"a k'ofar gidansu Nasmat tatsaya dan allanta yana hannun Nasmat d'inne kuma rubutu za tayi da wallahi bata tsaya ba"Khausar takalleta "to ke wai saurin meye haka kike yi?Sauri kuma ba wajan zuwa ba tunda gashi dole ta tsaya jiranmu.Tamusu wani malalacin kallo"shiru ma amsace.Nasmat tacigaba"anya waccan ba budurwar D'ansarai bace?Cikin tafasar zuciya ta fizge allanta"kya tambayi kaza hanyar rafi...?Fuuu tayi gaba tana k'unk'uni.Suka bita da kallan mamaki cikin tunanin abinda ya caza mata k'wak'walwa haka.Nasmat tad'an motsa kafad'a "wallahi can da yawarki yarinya.

Tun daga ranar D'ansarai bai kuma yadda sun had'u da Bilkisu a kwanakin k'arshen mako ba. Ranar wata Juma'a yayi shigarshi ta fararan kaya yad'auki motarshi sai Matsirga anan yayi sallar Juma'a.Yana fitowa daga masallaci yadinga bin kwatancen Bilkisu kasancewar shi ba bak'o bane a garin sai ko gashi a k'ofar gidan.Wani dogon dattijo kyakkyawan farin Bafulani yahango, shi da wani da bai k'arasa shi a tsufa ba suna magana, sun dad'e suna maganganunsu sannan sukayi sallama.

Julaibib yatare shi cikin sallama...

Malam Lamid'o ya amsa sallamar yana mik'a ma Julaibib hannu dan suyi musafaha amma ya nok'e a haka ya gaishe shi cikin girmamawa.Malam Lamid'o sai ya yaba da natsuwarshi yayi murmushi"samari daga ina? Cikin ladabi ya amsa"Baba ni bak'on kune. Yagyad'a kai yana kara nazarinshi"af to,to madallah sannu da zuwa to bismillah shigo ciki,yabud'e mishi d'akin zauran suka shiga yanuna mishi wajan zama"zauna ina zuwa"yajuya zuwa cikin gidan sai gashi ya dawo da damammiyar fura da nono tasha zuma da ruwan sha "bismillah samari"to Baba nagode"yajuya yasake fita dan yabashi waje. wucewar dak'ik'u talatin yasake shigowa lokacin Julaibib yad'an sha fura dan baya wani jin yunwa.

"Samari daga ina kake?

Julaibib Abdullahi D'ansarai...

Shine cikakken sunana daga Zonkwa nake.

Yabashi labarin kome game da had'uwarsu da Bilkisu...Ita kanta ba ta san zanzo nan ba.Ni nazo wajan kane Baba indai bakama Bilkisu miji ba to idan ka amince zan turo maka manyana.Yamishi kallan nazari" yanzu misali idan na amince ita kuma Bilkisu bata amince dakai amatsayin miji ba fa?Yad'anyi jimmm...sannan yad'ago cikin natsuwa yakalleshi "bazanji dad'i ba amma bazan ji haushi ba ,dan na san kome na rayuwar bawa yana rubuce ne,yana kuma tafiya daki-dakine kamar yadda numfashi yake shiga da fita ajikin d'an Adam,zan mana addu'a ni da ita Ubangiji yahad'amu da abokan zama na arzik'i.
Chapter 29 · 0% Book details